Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya kori dukkanin kwamishinoni da sauran jami’an gwamnati da ke aiki ƙarƙashin gwamnatinsa.
Wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Nelson Chukwudi, ya fitar a birnin Fatakwal a daren Laraba ya bayyana cewa wannan mataki ya fara aiki nan take.
An yi sallamar ne saboda hukuncin Kotun ƙoli da ya shafi dukkanin kwamishinonin da sauran jam’an da ya kora.
Gwamna Siminalayi Fubara ya sallami jami’an gwamnatinsa ne a lokacin Bikin Ranar ’Yancin Nijeriya.
Sanarwar da Nelson Chukwudi ya fitar ta ce, “Gwamna ya sallami dukkanin kwamishinoni da sauran jami’an gwamnati da wannan hukuncin Kotun ƙoli ya shafa daga mukamansu nan take.”
A cikin jawabinsa a faretin ranar ‘yancin ƙasa, Fubara ya yaba da muhimmancin bikin ’yancin Nijeriya, inda ya yi kira ga jama’a da su yi aiki da shugaba Bola Tinubu don gina kasa.
Gwamnan ya ƙara jaddada aniyarsa ta ci gaba da hidimta wa jihar tare da gode wa jama’a bisa goyon bayansu, sannan ya yi fatan alheri da murnar zagayowar ranar samun ’yancin kasa.
Sanarwar ta aara da cewa, “Mai girma Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya gode wa ‘yan majalisar zartarwarsa bisa hidima da gudunmawar da suka bayar wajen ci gaban jihar a tsawon shekaru biyu da suka gabata.
A baya, Kantoman riƙo, Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya), ya dakatar da dukkan kwamishinoni, mashawarta na musamman da mataimaka na musamman da Fubara ya naɗa.
Ibas ya kuma rusa dukkannin kwamitoci da hukumomi tare da dakatar da shugabanninsu. Sai dai bayan ya sauka daga riƙon muƙamin a ranar 18 ga Satumba aka fara nazarin makomarsu.
Wannan ya faru ne bayan Shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya dakatar da Fubara tare da ayyana dokar ta-ɓaci a jihar.
