Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Hukumar Lafiya ta Duniya WHO tare da haɗin gwiwa da UNICEF, Solina, gidauniyar chigari da gidauniyar Sultan da kuma hukumar bayar da lafiya matakin farko za su yi wa yara sama da miliyan 1.8, allurar rigakafin Shan Inna, Polio a faɗin Jihar Zamfara.
Dr. Murtala Ibrahim Salahuddeen, manajan lamarin, cibiyar gaggawa ta ayyukan Polio, a jihar Zamfara, ya bayyana haka a wani taron manema labarai don bikin tunawa da ranar Polio ta duniya a jihar a yau Asabar.
A cewarsa, taken ranar Polio ta duniya ta wannan shekarar shine, kawo ƙarshen Polio yanzu, kowane yaro ya cancanci makoma mai ‘yanci daga Polio”.
Dr. Salahuddeen ya jaddada cewa ana iya yaƙi da cutar Shan Inna, Polio ta hanyar allurar riga-kafi, ilimi da kuma ayyukan al’umma.
“Tare da jajircewar ƙungiyoyin tallafi da haɗin gwiwar gwamnatin jihar Zamfara wajen yaƙi da yaɗuwar ƙwayar cutar Polio, kowane yaro zai iya girma cikin ƙoshin lafiya da ƙarfi.” Ya ce
Yace, ƙungiyoyin bada tallafi za su ci gaba da jajircewa wajen yin aiki kafaɗa da kafaɗa da sarakunan, gargajiya, malaman addinai da al’umma don tabbatar da nasarar gangamin yaƙi da cutar Shan Inna a jihar.
Ya bayyana cewa alluran rigakafin suna da aminci, inganci kuma suna kare yara daga gurguntakar jiki da kuma mutuwa.
“Kamar yadda nake magana a yanzu, hukumar lafiya ta duniya WHO, tare da haɗin gwiwar UNICEF, gidauniyar Sultan, Solina, gidauniyar Chigari da hukumar kula da lafiya ta jihar Zamfara suna mai da hankali kan tabbatar da anyi wa yara sama da miliyan 1.8 rigakafin Polio a faɗin jihar”. Dr. Salahuddeen ya ƙara da cewa
Ya buƙaci dukkan masu ruwa da tsaki a jihar Zamfara da su goyi bayan yaƙi da cutar ta Shan Inna na shekarar 2025 don samun nasarar da aka sanya a gaban a jihar.
Da yake jawabi, babban sakataren hukumar kula da lafiya matakin farko ta jihar Zamfara, Dakta Hussaini Yakubu Anka ya bayyana cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da jajircewa wajen yin aiki tare da dukkan abokan hulɗar bada tallafi domin ganin an kawar da cutar shan inna a Zamfara.
