‘Yan matan Kebbi: Mu na iya hasashen inda ɗaliban suke, inji Sanata Maidoki

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Sanatan da ke wakiltar Jihar Kebbi ta Kudu a Majalisar Dattawan Nijeriya, Garba Maidoki, ya bayyana fatansa na dawowar ƴan matan da ƴan bindiga suka yi awon-gaba da su a jihar cikin ƙaramin lokaci.

Maidoki ya faɗi haka ne a wata hira da gidan talabijin na Channels ranar Laraba, wato kwanaki biyu da ƴan bindigar suka kai farmaki makarantar Government Girls’ Comprehensive Secondary School, Maga, inda suka yi garkuwa da ɗalibai guda 25.

“Mu na iya tunanin inda ƴan matan suke, kuma mu na da tabbacin ba su fita wajen Kebbi ta Kudu ba. Akwai fata mai ƙarfi na cewa ƴan matan za su dawo gidajensu cikin kwana ɗaya ko biyu”, inji shi.

A ranar Litinin ne iftila’in ya faru wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mataimakin shugaban makarantar a lokacin da ya yi yunƙurin hana ƴan bindigar garkuwa da ɗaliban.

Tun daga lokacin ne gwamnatin tarayya ta umarci hukumomin tsaro da su gaggauta ceto ƴan matan.

A wani labarin kuwa, Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya je Birnin Kebbi inda ya ziyarci kauyen da al’amarin ya faru bisa umarnin Shugaba Bola Tinubu.

A jawabinsa, Shettima ya jaddada burin Shugaba Tinubu na dawowar ƴan matan, inda ya kirayi hukumomin tsaro da su ruɓanya ƙoƙarinsu wajen ganin an yi nasara a atisayen ceton cikin ƙanƙanin lokaci.

Kazalika, ya bayyana al’amarin a matsayin abin takaici, yana mai cewa gwamnatin tarayya za ta yi duk abinda ya dace wajen ganin yaran sun dawo cikin aminci.

By Babaji