Mai Binciken Kuɗi na Nijeriya ya bankaɗo almundahana biliyan N2.69 a Rundunar ’Yan Sanda

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Rahoton shekara-shekara na Babban Mai Binciken Kuɗi na Nijeriya kan rashin bin ƙa’idojin kuɗi a hukumomin gwamnati na shekarar 2022 ya zargi Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya da aikata manyan almundahana a harkokin kuɗi, bayar da kwangiloli ba bisa ƙa’ida ba, da kuma watsi da ayyuka da darajarsu ta kai kimanin Naira Biliyan 2.69.

Wani rahoto da jaridar News Point ta wallafa, ya ce, rahoton Oditan ya bayyana cewa hedikwatar ‘yan sanda ta saɓa ƙa’idoji da suka haɗa da biyan kuɗaze ga ayyukan da ba a aiwatar ba, bayar da kwangiloli ba tare da sahalewar majalisa ba, da rashin bin dokokin saye-da-sayar na gwamnati. 

Daga cikin abubuwan da suka fi ɗaukar hankali akwai ayyuka 14 da darajarsu ta kai sama da Naira biliyan 1.93, waɗanda aka saka su a kasafin kuɗin 2022 a matsayin ayyuka masu gudana, amma bincike ya gano cewa an bar su kuma an watsar ba tare da kammala su ba.

Rahoton ya nuna cewa maimakon kammala ayyukan da aka amince da su a kasafi, hukumar ‘yan sanda ta ci gaba da bayar da sabbin kwangiloli da ba su bayyana a kasafin 2022 ba, kuma ba a samu wata hujja ta sahalewar Majalisar ƙasa ba. Wannan, cewar rahoton, ya saɓa wa ƙa’idojin kuɗi da dokokin saye-da-sayar na gwamnati.

A martanin da ta mayar, hukumar ‘yan sanda ta kare kanta da cewa waɗannan ayyukan ana ta jujjuya su tun daga shekarar 2017 ne ba tare da samun cikakken kuɗin aiwatarwa ba, sakamakon tsarin “zero-based budgeting” da gwamnati ke amfani da shi.

Ta ce, ayyukan sun kai matakai daban-daban na kammalawa amma rashin kuɗi ya sa aka bar su. Duk da haka, Odita-Janar ya ƙi amincewa da wannan bayani, tare da ba da shawarar a tilasta wa Sufeto-Janar na ‘yan sanda dawo da duk kuɗazen da aka kashe ba bisa ƙa’ida ba tare da maida su cikin baitul malin gwamnati.

Rahoton ya kuma bai wa jama’a mamaki game da wani aikin gina sansanonin wucin-gadi guda 12 masu ɗaki daya-zaya da kuma gyaran wani ginin ofis a Cibiyar Koyar da Sana’o’in Ritaya ta ‘yan sanda da ke Kudan a Jihar Kaduna.

An ce an biya kusan kashi 79 na kuɗin kwangilar, wato fiye da Naira miliyan 111, amma lokacin da masu bincike suka kai ziyara a watan Maris na 2024, ba su tarar da alamun an gina ko ɗaya daga cikin sansanonin ba.

Haka kuma, rahoton ya tona asirin wasu kuɗaɗe da aka biya ba bisa ƙa’ida ba, ciki har da kuɗin da aka kashe don ƙarin ayyuka a ɗakin taron Sufeto-Janar na ‘yan sanda, biyan Naira miliyan 499 don gina Polisen Kwaleji a Bashar, Jihar Filato ba tare da aiwatar da aikin ba, da kuma biyan bashin shekarar 2020 daga kasafin 2022, wanda hakan ya saɓa wa dokokin kuɗi.

Rahoton ya kuma lissafa wasu kura-kuran kamar biyan Naira miliyan 6 ga wani mai taimaka wa Sufeto-Janar kan haraji ba tare da bin ƙa’ida ba, sayen kayan aikin cibiyar sarrafa bayanan NPF kai tsaye ba tare da bin dokokin saye-da-sayar ba, da kuma asarar dabbobin aiki irin su dawakai ba tare da cikakken bayanin inda suka ɓace ba.

Haka zalika, an tattara tsofaffin bindigogi daga sassa daban-daban na ‘yan sanda ba tare da rubutacciyar hujjar yadda aka sarrafa su ba.

Odita-Janar ya kammala da cewa, hukumar ‘yan sanda ta ƙasa ba ta bin ƙa’idojin kuɗi, dokokin bayar da kwangila, da kuma wa’idojin adana bayanai. Rahoton ya jaddada cewa duk waɗannan laifuka za su ci gaba da ɗaure wuyan hukumar har sai an aiwatar da duk shawarwarin gyara tare da dawo da kuɗaɗen da aka yi almundahana da su.

Wannan bincike ya ɗora ‘yan sanda a jerin manyan hukumomin da ake yawan zargi da almundahana a Nijeriya. A baya, ma rahotannin Odita-Janar sun bankaɗo makamantan irin waɗannan matsaloli a hukumomi kamar Ma’aikatar Harkokin Gidaje da Ma’aikatar Ayyuka, inda aka biya biliyoyin naira ga ayyukan da ba a kammala su ba ko kuma ba a fara su kwata-kwata ba. Hakan na ƙara tabbatar da matsalar rashin ingantaccen kulawa a harkokin kuɗin gwamnati, wadda ke jawo asarar kuɗaɗen jama’a da kuma jinkirin ci gaban ƙasa.

By ukarofi