Daga UMAR GARBA a Katsina
Wata mummunar gobara ta yi sanadiyar ƙonewar mutane biyar ‘yan gida ɗaya, gobarar ta rutsa da wani magidanci Malam Muhammad Habibu da matarsa, Malama Fatima Muhammad, a unguwar Ƙofar Sauri da ke cikin birnin Katsina.
Gobarar ta kuma yi ajalin ’ya’yansu uku: Khadija, Aliyu da Abubakar waɗanda duka suka rasu sanadiyyar gobarar.
Rahotanni sun bayyana cewa wutar lantarki ce ta haddasa tashin gobarar da misalin ƙarfe 1 na dare ranar Lahadi, bayan an kawo wutar lantarki da ƙarfi, wadda ta yi sanadiyyar ƙonewar mutanen ƙurmus da suka fito daga ahali ɗaya.
Jami’an hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Katsina, SEMA, sun je wurin da safiyar ranar Litinin domin tantance asara da kuma bada tallafin gaggawa ga iyalan waɗanda abin ya shafa.
Tuni aka gudanar da jana’izar mamatan kamar yadda addinin Islama ya tanada, a unguwar ta Ƙofar Sauri da ke birnin Katsina.
