Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Kasuwar man fetur a Nijeriya na fuskantar sabon yanayi mai zafi, yayin da wasu gidajen mai suka fara sayar da man fetur a ƙasa da Naira 739 kan kowace lita – farashin da matatar Dangote ta ayyana a matsayin ‘ma-fari’.
Wannan ya nuna cewa gasa tsakanin ’yan kasuwa tana ƙara ƙarfi, abin da ke kawo sauƙi ga masu saye, amma yana jefa ’yan kasuwa cikin matsin lamba.
Binciken da majiyar Blueprint Manhaja ta gudanar ya nuna cewa matakin da matatar Dangote ta ɗauka a watan Disamba na rage farashin fetur daga kusan N900 zuwa N739 kan lita ya girgiza kasuwa, ya tilasta wa masu shigo da fetur da masu ajiya a rumbu su sauya dabarunsu domin tsira. Wannan sauyi ya buɗe ƙofar gasa mai tsauri tsakanin gidajen mai.
A yanzu haka, wasu gidajen mai na sayar da fetur ƙasa da na kamfanin MRS, wanda Dangote ya ba wa amanar jagorantar tsarin farashin Naira 739 a faɗin ƙasa.
A ranar Lahadi, an gano cewa gidajen NIPCO na sayar da fetur a N738, SAO na sayarwa a N735, yayin da Akiavic ke sayarwa a N737 kan kowace lita. A Mowe da ke jihar Ogun, wani gidan mai na kamfanin AP da ke kusa da MRS ya rage farashinsa zuwa N736, lamarin da ya jawo cunkoson masu saye a wurin.
Majiyoyi daga masana’antar sun bayyana cewa yanzu gidajen mai na sa ido kan farashin juna lokaci zuwa lokaci, suna sauya nasu farashi nan take domin kada su rasa kwastomomi. Masu motoci kuma na yin tururuwa zuwa inda aka fi sauƙin farashi, abin da ke barin gidajen da ke da tsadar farashi cikin ƙunci.
Bayanan ƙungiyar Major Energies Marketers Association of Nigeria (MEMAN) sun nuna cewa matsakaicin kuɗin saukar fetur daga waje ya kai N762.38 kan lita, yayin da farashin da Dangote ke sayarwa daga matata ya tsaya a N699. Duk da ƙarancin riba da yuwuwar asara, ’yan kasuwa na ci gaba da rage farashi domin ci gaba da riƙe kasuwa a wannan sabon yanayi.
Wasu daga cikin masu sana’ar sun bayyana cewa rage farashin ba wai saboda fetur daga waje ya fi araha ba ne, sai dai wata dabara ta kasuwanci domin kada su fice daga gasa. Sun jaddada cewa ba sa fafatawa da wani kamfani kai tsaye, illa kawai kare matsayinsu a kasuwa.
Wannan rikici ya samo asali ne tun ranar 12 ga Disamba, lokacin da matatar Dangote ta rage farashin fetur daga N828 zuwa N699 kan lita. Bayan haka, shugaban rukunin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya gargaɗi ’yan kasuwa da ke shirin ci gaba da sayar da fetur da tsada duk da rage farashin. Ya yi alƙawarin amfani da duk wata hanya domin tabbatar da cewa ba a sayar da fetur sama da N740 a watan Disamba da Janairu ba.
Sakamakon wannan mataki, gidajen MRS a Legas, Ogun da wasu jihohi suka fara sayar da fetur a N739, lamarin da ya haifar da dogayen layukan masu saye. Sai dai yanzu yanayin kasuwa na sauyawa, yayin da wasu gidajen mai ke ƙara rage farashi fiye da na Dangote, abin da ke ƙara zafafa gasa.
Mai magana da yawun ƙungiyar IPMAN, Chinedu Ukadike, ya bayyana cewa kasuwa ta shiga cikakkiyar gasa, inda farashi kaɗai ke ƙayyade inda kwastomomi za su nufa. Ya ce babu wanda ke tilasta wa ’yan kasuwa farashi, kasuwa ce da kanta ke daidaitawa. Ya kuma yi gargaɗin cewa duk gidan mai da ya ƙi rage farashi na iya rasa kwastomomi tare da fuskantar matsin kuɗin riba daga bankuna.
A gefe guda, matatar Dangote ta bayyana cewa tun watan Oktoba 2025 ta fara ba ’yan kasuwa fetur har lita miliyan 600, aka ƙara zuwa miliyan 900 a Nuwamba, sannan aka faɗaɗa zuwa biliyan 1.5 a Disamba. Ta ce yanzu an buɗe sayar da fetur ga duk ’yan kasuwa da suka cancanta, kuma tana lodin tsakanin lita miliyan 31 zuwa 48 a kullum gwargwadon buƙata.
Masana harkar kasuwa na ganin wannan sauyi a matsayin zaya daga cikin manyan sauye-sauyen da kasuwar fetur ta taɓa fuskanta a Nijeriya cikin shekaru da dama. A halin yanzu, masu amfani da fetur su ne ke cin ribar wannan gasa mai tsauri, yayin da farashi ke ci gaba da raguwa.
