A tanadi hukunci kan sakacin likitoci

Spread the love

Mutuwar Aisha Umar, uwa ga ’ya’ya biyar, ba abin baƙin ciki kaɗai ba ne; hujja ce mai nauyi da ke tona asirin gazawar tsarin kiwon lafiyar Nijeriya. Rahotanni sun nuna cewa ta rasu ne bayan da asibiti ya bar almakashin tiyata a cikinta bayan an yi mata aiki, kuskure mai muni, mai sauƙin kaucewa, wanda uzurinsa ma yana da wuya a karɓa. Amma abin da ya biyo bayan mutuwarta ya fi tada hankali fiye da sakacin da kansa: an ce mijinta, Aubakar Binji, an shaida masa cewa mutuwarta “ƙaddarar Allah” ce.

Wannan furuci ya yi daidai da al’adar kauce wa ɗaukar alhaki da ta zama ruwan dare ga mutane, musamman a fannin kiwon lafiya a Nijeriya.

A cewar mijinta, Aisha mace ce mai kulawa, mai tallafi, wadda ta sadaukar da rayuwarta wajen tarbiyyar ‘ya’yansu. Sun shafe shekaru 20 da aure, ta bar ’ya’ya biyar, ƙaramin cikinsu bai wuce shekara huɗu ba. Mutuwarta ta gutsura zuciyar iyalin ta, ta bar rayuwar yara ƙanana cikin wani yanayi. Ba wani bayani ko uzuri da zai dawo da abin da aka rasa, amma shiru da musun laifi na ƙara zurfafa rauni.

Sakacin likita ba “hukuncin Allah” ba ne; gazawar ɗan Adam ce. Lamarin Aisha ba shi kaɗai ba ne. Ya zo ne a daidai lokacin da ake ƙara jin ƙorafe-ƙorafe kan zargin sakacin likitoci a asibitocin Nijeriya, ciki har da mutuwar ɗan shahararriyar marubuciya Chimamanda Ngozi Adichie a wani asibitin Legas, wanda ya haifar da tambayoyi masu nauyi kan ƙa’idojin kulawa da marasa lafiya. Ko a asibitocin gwamnati ko masu zaman kansu, ana ganin alamar maimaituwar matsalar: mutuwa da za a iya kaucewa, iyalai cikin jimami, sannan cibiyoyi su rufe kansu maimakon su fuskanci gaskiya.

Tsarin kiwon lafiyar Nijeriya na fama da ƙarancin kuɗi, ƙarancin ma’aikata, tsofaffin kayan aiki, da raunin sa ido na hukumomi. Amma waɗannan matsaloli ba su zama uzuri ga sakaci mai tsanani ba. Barin kayan aiki a jikin mara lafiya bayan tiyata ba matsalar kayan aiki ba ce; gazawar ƙwarewa da bin ƙa’ida ce. A ƙasashen duniya, irin wannan kuskure ana ɗaukarsa a matsayin laifi da bai kamata ya faruwa ba ko da sau ɗaya.

Sai dai a Nijeriya, yana faruwa, kuma galibi masu laifi su kan tsira ba tare da fuskantar hukunci ba. Ba kasafai ake gurfanar da ma’aikatan lafiya kan sakaci da ya yi sanadin mutuwa ba. Hukumomin sa ido su kan yi jinkiri, su yi shiru, ko kuma su gudanar da bincike a ɓoye ba tare da fitar da sakamako ga jama’a ba. Iyalai kuma su kan ji tsoro, gajiya ko talauci ya hana su neman adalci. Sakamakon haka shi ne al’adar rashin hukunci.

Kamar yadda Aubakar Binji ya bayyana, “ɓangaren lafiya ba ya kula da marasa lafiya yadda ya kamata, gwamnati kuma dole ta ƙara himma. Hukumomin sa ido su yi aikinsu yadda ya dace.” Wannan ba magana ce ta fushi kawai ba, magana ce ta gaskiyar da ake rayuwa da ita.

Dole ne a samar da sakamako. Sakacin likita da ya kai ga mutuwa ya kamata ya jawo alhakin laifi a gaban doka. Likitoci, ma’aikatan jinya ko shugabannin asibiti da aka samu da laifi su fuskanci shari’a, har da hukuncin ɗauri idan ya dace. Ba ramuwar gayya ake nema ba, ana neman hana maimaituwar laifi ne. Idan matuƙan jirgi ko injiniyoyi sun jawo bala’i ta sakaci, ana hukunta su. Dole a daidaita mizani a fannin lafiya ma.

Horarwa ma dole ta sauya. Ma’aikatan lafiya su san ba ilimin jinya kadai ake buƙata ba, har da ilimin dokokin kiwon lafiya da ɗabi’ar aiki. Sanin alhakin doka na ƙarfafa ladabi da kulawa, yana tuna musu cewa marasa lafiya ba lambobi ba ne, mutane ne masu haƙƙi.

Gwamnati ma na da nata rawar. Asibitoci ba za su yi aiki lafiya ba tare da isassun kayan aiki, ma’aikata da horo na ci gaba ba. Jerin binciken tiyata, na’urar duba jiki bayan aiki, da kayan sa ido na ceton rayuka ne, amma sai idan suna samuwa kuma ana amfani da su yadda ya kamata. Kasafin kuɗin lafiya dole ya wuce magana ya koma a aikace.

Biyan diyya ma ginshiƙi ne na adalci. Iyalai da suka rasa ‘yan uwansu sakamakon sakaci da aka tabbatar su cancanci diyya. Kuɗi ba zai mayar da uwa ko ɗa ba, amma zai taimaka wajen ba da kwanciyar hankali, ilimantar da marayu, da nuna amincewar laifi. Tsarin da ba ya bayar da uzuri ko diyya, tsarin ne da ya rasa ɗabi’a.

ƙungiyoyin farar hula ma dole su taka rawa. Yawancin iyalai ba su da ƙarfin shari’a. Tallafin lauya, wayar da kai, taimakon jinya na zuciya da matsin lamba daga jama’a na da muhimmanci domin kada irin wadannan lamurra su shuɗe cikin shiru.

Mutuwar Aisha Umar bai kamata ta zama wata ƙididdiga kawai ba. Ya kamata ta zama alamar sauyi. Idan Nijeriya ta ci gaba da ɗaukar sakacin likita a matsayin ƙaddara ko nufin Allah, za a ci gaba da rusa iyalai, kuma amincewar jama’a da asibitoci za ta ƙara rushewa.

By ukarofi