
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Jihar Kano ta musanta cewa ta yi yunƙurin hana Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso shiga jihar, inda ta bayyana zargin a matsayin ƙarya da aka ƙirƙira da nufin ruɗar da jama’a.
Idan za a tuna, a wata hira da wata jaridar yanar gizo, na hannun daman Kwankwaso kuma jigo a Jam’iyyar NNPP wato Buba Galadima ya zargi gwamnatin Abba Kabir Yusuf na Kano da rubut wasiƙa zuwa ga Gwamnatin Tarayya ta neman ta daktar da Kwankwaso daga zuwa Kano.
To saidai wannan zargi bai samu zama ba domin kuwa, Kwamishinan Labarai da Harkokin Cikin Gida, Ibrahim Waiya, ya yi watsi da shi a wata takarda da ya aike wa manema labarai a ranar Alhamis, inda ya ce zancen ba shi tushe ko makama.
A cewarsa, an ƙirƙiri zancen ne da nufin ruɗar da jama’a da ƙoƙarin tayar da fitina a jihar, yana mai cewa gwamnatin jihar ba ta taɓa yunƙurin hana Kwankwaso ko wani ɗan ƙasa shiga jihar ba.
Ya ƙara da cewa, jihar Kano za ta cigaba da kasancewa cikin aminci da ƙoƙarin kiyaye hukunce-hukuncen doka akan kowane ɗan ƙasa ciki har da ‘yancin zirga-zirga da da zama ɗan wata ƙungiya.
A ƙarshe, ta yi kira ga Buba Galadima da ya samar da hujjoji gamsassu da za su tabbatar da sahihancin furucin nasa ko kuma ya janye su domin kare zaman lafiya da ingancin siyasar jihar.
