Daga USMAN KAROFI
Rahotanni daga yankin Gabas ta Tsakiya sun nuna cewa rikicin da ke gudana a Tekun Gulf na ƙara tsananta, inda Iran ta fara faɗaɗa nau’in wuraren da take kai wa hari. A farkon makonnin rikicin, hare-haren sun fi karkata ne kan cibiyoyin soji na Amurka, ciki har da na’urorin kariyar makamai masu linzami da jiragen yaƙi da ke sansanonin soja. Sai dai a yanzu, bayan shigowar mako na uku, dakarun IRGC sun bayyana cewa dukkan kadarorin kasuwancin Amurka a yankin sun zama halattattun wuraren hari.
Hukumomin Iran sun kuma yi gargaɗi cewa duk bankunan Amurka da ke aiki a yankin za su iya zama makasudin hari idan har Amurka ta sake kai farmaki kan wani bankin Iran. Bugu da ƙari, IRGC ta buƙaci kamfanonin Amurka da ke Gabas ta Tsakiya da su kwashe ma’aikatansu tare da rufe wuraren aikinsu domin kauce wa haɗari. Haka kuma, sun gargaɗi mazauna yankunan da ke kusa da wuraren masana’antu da ke da alaƙa da Amurka da su ƙaurace domin kare rayukansu.
Wani jerin sunaye da aka wallafa ya nuna kamfanoni da dama na Amurka da ke aiki a ƙasashen Jordan da Hadaddiyar Daular Larabawa, ciki har da manyan kamfanonin fasaha, makamashi da kuɗi. Sai dai ana shakku kan sahihancin wannan jerin, domin wasu rahotanni sun nuna cewa wani tashar Telegram ce ta kirkiri jerin, ba lallai ba ne daga hukumomin IRGC kai tsaye. Haka kuma, wasu kamfanonin da aka lissafa ba na Amurka ba ne, abin da ya ƙara jefa shakku kan ingancinsa.
A wani ɓangare kuma, akwai rahotannin da ke yawo cewa cibiyoyin adana bayanai (datacentres) mallakin kamfanonin Amurka sun shiga cikin jerin wuraren da ake iya kai wa hari. Duk da cewa babu tabbacin an kai wani hari kai tsaye, wasu manyan kamfanonin fasaha sun fara rage yawan ma’aikata ko kuma shirin dakatar da ayyuka na gaggawa a wasu wurare. Masana sun ce idan aka kai hari kan waɗannan cibiyoyi, hakan na iya jefa harkokin gwamnati da kasuwanci cikin matsala, domin yankin ya zama muhimmiyar cibiyar fasahar zamani da tattalin arzikin dijital a duniya.
