Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Fadar Shugaban ƙasa ta nanata cewa batun tsaro na da kan gaba cikin muhimman abubuwan da shugaba Tinubu ke bai wa muhimmanci a yayin da fadar shugaban ƙasa ke ƙara tattaunawa da hukumomin tsaro da abokan hulɗa domin kawo ƙarshen matsalar tsaro a Nijeriya.
Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan bayan zama da shugaban ƙasa a ranar Lahadi a ranar Lahadi. Ya kuma ce shugaban ƙasa na bai wa duk wani yunƙuri na “ƙwaf ɗaya” domin warware tsaro muhimmanci.
A cewar Idris, shugaban ƙasa ya dawo ne daga garin Jos domin duba al’amuran tsaro kuma yana ci gaba da tattawanawa da hukumomin tsaro wajen fitar da wata dabara da za ta dawo da zaman lafiya mai ɗorewa.
Blueprint Manhaja ta rawaito yadda ake samun ɓullar sabbin hare-hare a wasu sassan jihar Filato biyo bayan kashe-kashe mazauna Anguwan Rukuba da ke ƙaramar hukumar Jos ta Arewa a ranar Lahadin da ta gabata.
Tun bayan ayyana dokar taƙaita zirga-zirga. Sai dai akwai rahotanni na samun hare-hare a sauran jihohi kamar Katsina da Borno.
“Shi (Shugaba Tinubu) ya dawo ne daga Jos, saboda matsalar tsaro da ke gabansa,” in ji Idris. “Yana ta magana da hukumomin tsaro domin samar da mafita mai ɗorewa da haɗin kai da sauran abokan hulɗa da sauran abokanmu na ƙasashen waje domin tabbatar da an samar da zaman lafiya mai ɗorewa.”
Ministan ya jaddada cewa gwamnatin na kallon matsalar tsaro ta fuskoki da yawa musamman a faɗin yankin Sahel, tana jaddada cewa Nijeriya ba za ta iya magance matsalar tsaro ita kaɗai ba. Ya buga misali da ziyarar ƙasar shugaban Chadi, Mahamat Déby, zuwa Abuja a matsayin wani babban mataki na haɗa kai wajen magance tsaro a nahiyar Afirka.
“Wannan abu ne mai muhimmanci yaƙi da ta’addanci. Ta’addanci ba shi da iyaka…Kuma abu ne mai wahala Nijeriya ta iya magance tsaro ita kaɗai,” ya faɗa, yana mai cewa haɗin guiwa da maƙwabtan ƙasashe muhimmin abu ne wajen magance barazanar matsalar tsaro a yankin Arewa maso gabas da faɗin yakin Sahel.
Idris ya ƙara da cewa shugaban ƙasa yana aiki da sauran abokan hulɗa na ƙasashen waje da suka haɗa da Amurka da ƙungiyar tarayyar Turai da Ingila domin inganta al’amuran tsaro a Nijeriya. Ya kuma ce ziyarar shugaba Tinubu zuwa Ingila ta bai wa matsalar tsaro muhimmanci.
Baya ga tsaro, ministan ya ce shugaban ƙasa yana sane da irin damuwa da ‘yan Nijeriya inda ya buƙace su da su ci gaba da nuna kishin ƙasa da haɗin kai.
Haka kuma shugaban kamfanin BUA, Abdul Samad Rabiu, ya kai ziyarci shugaban ƙasa wanda ke bikin Easter a jihar Legas. BUA ya ce ya kai ziyarar ce domin yi masa barka da Sallah da murnar ƙarin shekara da jaddada goyon bayansa ga gwamnatinsa.
Fadar Shugaban ƙasa ta jaddada cewa duk da hutun Easter da ake yi, ana ci gaba da tafi da harkokin gwamnati a yayin da shugaba Tinubu ke ci gaba da ganawa da masu ruwa da tsaki da sake duba dabaru da nufin ganin ya cika alƙawuran da ya ɗauka musamman dawo da tsaro a faɗin Nijeriya.
