An yi jana’izar Kakakin Majalisar Dokokin Kebbi a Zuru

Spread the love

An yi jana’izar gawar marigayi Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi, Hon. Muhammad Usman Zuru, a garin Zuru bayan gudanar da sallar jana’iza a Babban Masallacin Zuru a wannan Alhamis.

Marigayin ya rasu ne a ranar Litinin, 6 ga watan Afrilu, 2026, a wani asibiti da ke birnin Alkahira na ƙasar Masar inda yake karɓar magani sakamakon jinya mai tsawo.

An haifi marigayin a ranar 5 ga watan Afrilu, 1970, kuma ya bar mata guda da ’ya’ya biyar.

A cikin saƙon ta’aziyyarsa, gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bayyana alhininsa kan rasuwar, inda ya ce jihar ta yi rashin babban jigo, ɗan majalisa mai kishin aiki da kuma shugaba nagari.

Gwamnan ya ƙara da cewa rasuwar marigayin ta haifar da babban gibi a harkokin shugabanci a jihar, yana mai jaddada cewa halayensa na natsuwa, kwarewa wajen tafiyar da al’amuran gwamnati, da jajircewarsa wajen haɗin kan al’umma da ci gaban jihar Kebbi za su ci gaba da kasancewa abin tunawa.

Haka kuma, gwamnan ya roƙi Allah Madaukakin Sarki da Ya gafarta wa marigayin, Ya ba shi Aljannatul Firdausi, tare da bai wa iyalansa da al’ummar jihar Kebbi ƙarfin jure wannan rashi.

Manyan mutane da suka haɗa da tsoffin gwamnoni, sanatoci, ’yan majalisun tarayya da na jiha, da kuma sarakunan gargajiya sun halarci jana’izar da aka gudanar a garin Zuru.

By Babaji