Abba Bichi ne wanda ya fi kowa cancantar zama Mataimakin Gwamnan Jihar Kano

Spread the love

Daga UNCLE LARABI

Ko kai ɗan wane jam’iyya ne, duk a dawarka, idan dai a Kano ka ke, ka san Abba Bichi ya fi kowanne ɗan majalisar tarayya dake Jihar Kano yin aiki a ƙaramar hukumarsa. Yana kuma samarwa da matasa aiki sosai. Ga shi da halin girma da dattako.

Ban san Abba Bichi a zahiri ba. Ba ni da alaƙa da shi, amma Ina ganin hotonsa da ayyukansa, Ina kuma jin labarin ayyukansa daga mutanen da suke Bichi da sauran mutane ma na Jihar Kano.

Daga ganin hotonsa ka san mutum ne mai kamala da muhibba. Mawuyacin abu ne ka same shi da hauragiya ko wata badaƙala irin ta siyasa. Don haka idan har maganar cancanta ake yi. Abba Bichi shi ya fi dacewa a ba wa Mataimakin Gwamnan Jihar Kano. 

A hasashena da hangena idan har an ba wa Abba Bichi za a samar da Kano sabuwa, don zai kawo ayyukan cigaba sosai cikin Jihar Kano da kewayenta ta yadda Kano za ta zama zakaran gwajin dafi wajen manyan ayyukan da za a gani a yaba a tabbatar da ana ayyuka masu muhimmanci ga talakawan Jihar Kano. 

Sannan Abba Bichi ba ya siyasar hauragiya ko ya tara ’yan daba a yadda nake samun labari tunda ban san shi ba ban taɓa ganin sa ba. An ce, mutum ne aƙili mai kamun kai da tarbiyya gami da dattako. 

Don haka kira ga mai girma gwamna da yan majalisun dokoki na Jihar Kano, kada idonku ya rufe wajen zaɓen Mataimakin Gwamna, ku zaɓo wa Jihar Kano bara-gurbin Mataimakin Gwamna. Ku Tsaya ku nutsu sosai ku samar mata da mutum nagari ku yi duba ga Abba Bichi, ku yi nazari sosai a kansa. Mutum ne da zai kawo wa Kano cigaba sosai ta kowacce fuskar siyasa. 

Larabi, marubuci ne a Kano mai sharhi kan harkokin siyasa da yau da kullum. Za a iya samun sa a 08065418892

Lahadi, 5 Afrilu, 2026

By ukarofi