Gbajabiamila ya umarci Abejide ya tsaya a ADC domin rikita jam’iyyar

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila, ya buƙaci ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazaɓar Yagba, Leke Abejide, da kada ya fice daga jam’iyyar ADC, sai dai ya ci gaba da zama a cikinta domin ƙara dagula tafiyar haɗakar jam’iyyar da Daɓid Mark ke jagoranta.

Gbajabiamila, tsohon Kakakin Majalisar Wakilai, ya bayyana hakan ne yayin bikin cikar shekaru 50 da haihuwar matar Abejide da aka gudanar a Abuja, inda wani bidiyo daga taron ya karaɗe kafafen sada zumunta.

A cikin faifan bidiyon, ya yaba wa Abejide kan jajircewarsa a siyasa, yana mai cewa ya san shi a matsayin mai ƙwazo da rashin amincewa da zalunci. Sai ya ƙara da cewa, mafi alherin da zai yi shi ne ya ci gaba da zama a cikin ADC, yana fafutuka daga ciki.

“Ka tsaya a cikin jam’iyyarka. Ka yi gwagwarmaya, ka tarwatsa su, kada ka bar ADC,” inji Gbajabiamila, yana ƙarfafa masa gwiwa da ya ci gaba da riƙe jam’iyyar da ya taimaka wajen gina ta.

Wannan kira na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyar ADC ke fama da rikicin cikin gida, inda ɓangarori daban-daban ke fafatawa kan shugabanci, musamman tsakanin ɓangaren da Nafiu Bala Gombe ke jagoranta da kuma wanda ke biyayya ga Daɓid Mark.

A nasa ɓangaren, Abejide ya jaddada cewa yana da alaƙa mai ƙarfi da jam’iyyar APC duk da kasancewarsa a ADC, yana mai cewa siyasa ba ta hana zumunci ba. Ya kuma bayyana goyon bayansa ga Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, inda ya ce shi ne zai zaɓa a zaɓen 2027.

A makon da ya gabata, Abejide tare da Bala Gombe sun jagoranci zanga-zanga zuwa hedikwatar Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC), suna roƙon hukumar da ta yi watsi da ɓangaren Daɓid Mark, suna zargin su da yunƙurin ƙwace ragamar jam’iyyar ba bisa ƙa’ida ba.

Masu zanga-zangar sun nace cewa dole ne a bi tsarin doka da kundin jam’iyya, suna mai zargin wasu ‘yan siyasa da ƙoƙarin shigowa ta bayan gida domin karɓe iko.

Rikicin da ke cikin ADC na ƙara ɗaukar zafi ne yayin da ake tunkarar babban zaɓen shekarar 2027, lamarin da ke jefa makomar jam’iyyar cikin wani yanayi na rashin tabbas.

By ukarofi