Farfesa Tunde Oke ya gabatar da lakcar NSUK karo na 60

Spread the love

Daga JOHN D WADA a Keffi

Wani ƙwararren farfesar shawarwari wato professor of counseling a turance dake babbar jami’ar jihar Nasarawa a birnin Keffi wato Farfesa Tunde Oke ya buƙaci gwamnatin tarayya ta haɗa tsarin shawara a cikin kundin tsarin shugabancin Najeriya.

Farfesa Tunde Oke ya ba da wannan shawara ne a lokacin da yake gabatar da laccar na musamman da farfesoshi ke gudanarwa a jami’ar karo 60 a jiya Laraba.

A cikin laccar sa ɗin, Farfesan ya ce bincike ya tabbatar cewa shawara ita ce hanya mafi sauƙi da za a iya bi wajen warware matsalolin da ke faruwa a harkokin shugabancin ƙasar nan don haka kamata yayi a saka tsarin a cikin fannonin karatu da shugabancin ƙasar.

Farfesa Tunde Oke ya cigaba da bayyana cewar” zai zama wajibi ga gwamnatin tarayya ta ƙara ƙaimi a cikin wannan batun na bai wa al’ummar ta shawarwari na musamman akai-akai domin halin da ‘yan Najeriya suka tsinci kansu ciki a yanzu dole ne a riƙa basu shawarwari na musamman don guje wa ɗaukan munanan matakai da zai sa su yin dana-sani daga baya musamman irin na kisan kai da sauran su” in ji shi.

Farfesan shawarwarin na babbar jami’ar ta gwamnatin jihar Nasarawa Tunde Oke ya kuma yi amfani da damar inda ya bayyana wasu daga cikin munanan sakamako da aka gano tattare da duk wani da baya samun shawarwari cewa sun haɗa da ɗaukan bahagon matakai da basu dace da abinda mutum yasa a gaba ba da kisan kai da mutuwar aure da kawo saɓani iri daban-daban cikin al’umma da dai sauran su, kana ya shawarci al’ummar jihar Nasarawa dama ƙasa baki ɗaya su tabbatar suna nemo shawarwari musamman gun ƙwararru irinsa a duk lokaci da buƙatar hakan ya taso kafin su ɗauki kowanne irin mataki.

Tun farko da take jawabin maraba shugabar jami’ar ta Nasarawa Farfesa Sa’adatu Hassan Liman wace aka wakilce ta a wajen laccar bayan ta yaba wa Farfesa Tunde Oke game da gagaruman gudumawa da tace ya daɗe yana bayarwa wajen inganta fannin na shawarwari a jami’ar ta kuma buƙaci gwamnatin tarayya da sauran gwamnatoti a duka matakai su tabbatar sun aiwatar da duka kiraye-kirayen dake ƙunshe a ƙasidar Farfesan don ceto ɗimbin al’ummar ƙasar nan ta kyawawan shawarwarin.

Sauran manyan baƙi da na kusa da Farfesan da suka yi jawabi duk suma sun yaba masa kana suka buƙace shi ya cigaba da ayukan agajin wa bil Adam baki ɗaya.

Wakilin mu ya kuma ruwaito cewa abubuwa da aka gudanar a ƙarshen laccar sun haɗa da bai wa Farfesa Tunde Oke lambar yabo na musamman da shugabar jami’ar ta yi da ɗaukan hotuna da sauran su.

By ukarofi