Daga AISHA ASAS
Tsayin lokaci da aka ɗauka ana yekuwa tare da wayar da kan al’umma kan illar yin aure a dunƙule wato ba tare da gwajin lafiya ba ga dukan alamu ya yi tasiri, ganin yadda matasa ke ƙoƙarin haɗa soyayya da ilimi. Ma’ana ba wa gwajin lafiya gurbi a cikin soyayyar da suke yi.
Sai dai duk da wannan yunƙuri, har yanzu akwai wani babban giɗi da ke ci gaba da zama barazana ga lafiyar iyalai, musamman idan aka zo batun gwajin jini kafin aure.
Maikaratu barkanmu da kasancewa da ku a shafin iyali na wannan makon. Kuma sannunku da jimirin bibiyarmu.
Na san wataƙila darasin namu na wannan makon zai ɗan rikitar, amma idan ku ka ba mu aron hankalinku za ku fahimci inda muka sa gaba.
A mafi yawan lokuta, ana takaita wannan gwaji ne ga abubuwa biyu: kwayar halittar jini wato genotype, da kuma cutar Kanjamau. Duk da muhimmancin su, masana sun nuna cewa wannan fahimta da ta tsayu a iya su na ƙara tabbatar da har yanzu akwai sauran rina a kaba, domin akwai wasu muhimman abubuwa da ake watsi da su waɗanda sakamakon su kan bayyana ne bayan aure, lokacin da gyara ya riga ya makara.
Abin da ya fi jan hankali shi ne yadda mutane da yawa ke ɗaukar cewa idan genotype ya yi daidai, kuma babu HIV, to komai ya kammala.
Likitoci sun sha ganin ma’aurata da suka shiga aure cikin kwanciyar hankali bisa waɗannan gwaje-gwaje biyu, amma daga baya suka tsinci kansu cikin matsaloli masu tsanani, ko dai a ɗangaren lafiyar uwa, ko kuma lafiyar jariran da aka haifa.
Genotype, wanda ke da alaƙa da cutar Sickle Cell Disease, babu shakka yana da matuƙar muhimmanci. Ya taimaka ƙwarai wajen rage haihuwar yara masu sikila a al’umma.
Haka ma gwajin kanjamau ya taka rawar gani wajen rage yaɗuwar cutar tsakanin ma’aurata, ko haihuwar yara zauke da cutar. Amma tambayar ita ce: shin me yasa har yanzu ake samun matsalolin haihuwa ko na jarirai duk da an yi waɗannan gwaje-gwaje?
A nan ne batun blood group ke fitowa fili, wani ɗangare da yawancin mutane ba sa ba shi muhimmancin da ya dace.
Blood group ba kawai sanin A ko B ko O ba ne don idan ka buƙaci jini a san irin wanda za a saka ma ba ne.
Akwai abin da ake kira Rh factor, wato positive ko negative. Wannan ƙaramin alamar da mutane ke ɗauka da wasa na iya zama babbar matsala a rayuwar aure.
Misali, idan mace tana da jini mai alamar negative, yayin da namiji ke da positive, akwai yiwuwar jaririn da za a haifa ya gaji wannan positive ɗin. A irin wannan yanayi, jikin uwa na iya ɗaukar jinin jaririn a matsayin wani abu na waje, ya fara yaƙi da shi.
Wannan ba zai iya bayyana nan take ba; sau da yawa yana bayyana ne daga ciki na biyu ko na gaba, inda matsaloli kamar zubewar ciki, wato bari, ko haihuwar jarirai masu fama da matsananciyar rashin lafiya, ko ma mutuwa ke iya faruwa.
Abin tausayi shi ne, waɗannan matsaloli da dama ana iya kauce musu tun kafin aure, da a ce an yi cikakken bincike tare da fahimtar sakamakon gwaje-gwajen da kyau. Amma rashin wayar da kai, ko kuma ɗaukar al’amarin ba wani abin damuwa ba, na sa a shiga cikin wannan hali ba tare da shiri ba.
Baya ga wannan, akwai wasu gwaje-gwaje da suka shafi lafiyar jiki gaba ɗaya waɗanda ya kamata a kula da su kafin aure. Ma’ana a san da su a tsakanin masoyan da ke shirin aure wanda ta hakan ne za su san abinda ya kamace su ko adalcin da ya kamata su yi wa yaran da za su haifa.
Ku biyo mu a mako na gaba don jin wasu daga cikinsu
