A bar ce-ce-ku-ce kan yawan shekarun Tinubu, mulki ba dambe ba ne – Masari

Daga UMAR GARBA a Katsina

Gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari ya bayyana cewar gwamnonin Arewa suna goyon bayan ɗan takarar Shugaban Ƙasa a Jam’iyyar APC ba don ya ba su muƙamai ba idan ya yi nasarar lashe zave a shekara ta 2023.

Masari ya faɗi haka ne a zantawarsa da DCL Hausa inda ya bayyana cewar gwamnonin na goyon bayan ɗan takarar jam’iyyar na su ne don ƙasar nan ta ci gaba.

“Ai ba muƙami muke nema ba yadda ƙasar za ta ci gaba muke magana, gwamnan Kebbi yana takarar Sanata,wane muƙami kuma zai nema? Gwamnan Zamfara zai sake komawa kan kujerarsa, gwamnan Jigawa yana takarar Sanata.

“Haka zalika da ni (Masari) da Malam Nasiru da kuma Ganduje ba mu ce muna neman wani muƙami ba,,” Inji shi.

Daga nan sai Gwamna Masari ya yi kira ga ‘yan ƙasa da su daina la’akari da yawan shekarun ɗan takarar jam’iyyar ta su ta APC, inda ya bayar da misalin wasu daga cikin shugabannin Amurka da suka kawo wa ƙasar cigaba alhalin ba matasa ba ne.

Masari ya cigaba da cewa mulki ba dambe ba ne kuma ba kokawa ba ne, don haka yake ganin babu abun ce-ce-ku-ce dangane da shekarun tsohon gwamnan Jihar Legos dake fatan ganin ya ɗare kujerar shugabancin ƙasar nan a shekara ta 2023.

“Ba dambe ba ne, ba kokawa ba ne, waye zai iya kawo cigaba a ƙasa saboda akwai manyan da ƙwaƙwalwar su tana aiki fiye da ta matasa,” inji shi.

Gwamna Masari ya ce madadin kallon yawan shekarun Tinubu kamata ya yi mutane su dubi muqaman da Tinubu ya riƙe da kuma cigaban da ya kawo.

A cewar masari ɗan takarar shugaban ƙasar na jam’iyyar su ya samar da tsaro a Jihar Legas gami da tsaftace birnin ya kuma shugabanci kowane ɗan ƙabila a ƙasar nan lokacin da yake gwamnan Jihar Legas don haka ne gwamnonin Arewa ke goyon bayan takarar sa.