Jirgin ƙasan Abuja-Kaduna zai fara aiki ran Litinin, cewar Gwamnati

Daga BASHIR ISAH

Gwamnatin Tarayya ta ba da sanarwar jirgin ƙasan Abuja–Kaduna zai dawo da aiki ya zuwa ranar Litinin, 5 ga Disamba.

Shugaban Hukumar Kula da Jiragen Ƙasa ta Nijeriya (NRC), Fidet Okhiria ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) hakan ranar Alhamis.

Ya ce, yanzu an kammala duk wani shiri da ya kamata don jirgin ya dawo ya ci gaba da aiki.

Sai dai Okhiria, ya shawarci masu sha’awar su bi jirgin da su sabunta manhajar sayen tikitin jirgin da ke wayoyinsu daga ranar 3 ga Disamba don cimma nasara.

Ya ƙara da cewa, za a soma aikin ne da jirage guda biyu.

A cewarsa, “Jirgi AK 1 zai bar tashar Idu da ƙarfe 9:45 na dafe ya isa tashar Rigasa da ƙarfe 11:53 na safe.

“Jirgi KA 2 kuwa zai bar tashar Rigasa da ƙarfe 8:00 na safe sannan ya isa tashar Idu da ƙarfe 10:17 na safe.

“Jirgi AK 3 zai bar tashar Idu da ƙarfe 03:30 na rana, ya isa tashar Rigasa da ƙarfe 05:38 na yamma.

”Sannan jirgi KA 4 zai baro tashar Rigasa da ƙarfe 02:00 na rana ya isa Idu da ƙarfe 04:07 na rana,” inji jami’in.

Kazalika, ya bai wa fasinjoji tabbacin ingantaccen tsaro daga ɓangaren Gwamnatin Tarayya.