Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Wata Kwalejin Kimiyya da ke Ibadan ta haramta wa ɗalibai mata masu juna biyu da masu shayarwa kawo jarirai zuwa ajujuwa da ɗakunan kwanan ɗalibai.
An bayyana hukuncin na kwalejin ne a cikin ƙa’idar ɗabi’a da majalisar gudanarwa ta sa hannu.
Makarantar ta ce, za a dakatar da ɗaliban da ke tare da juna a bainar jama’a a harabar jami’ar har tsawon zango ɗaya.
Adewole Soladoye, mai magana da yawun kwalejin, ya tabbatar da tsauraran ƙa’idojin.
“Makarantar ba gidan jinya ba ce. Shin daidai ne a kawo jarirai a cikin ajujuwan lacca? Lallai abin shagaltuwa ne. Suna da ‘yanci su haifi jarirai. Amma su nemi wurin kula da jariransu,” inji shi.
Majalisar gudanarwar makarantar ta ce, za a ba da takardun shaida ne kawai ga ɗalibai masu gaskiya a fagen neman ilimi da kuma ɗabi’u masu kyau, inda ta buƙace su da su guji sanya tufafin da ba su dace ba.