A baya akasarin manyan marubuta suna hantarar ƙanana masu tasowa – Gimbiya Amrah

“Marubutan littafi da na onlayin gudunmawa ɗaya suke bayarwa”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Gimbiya Amrah Auwal Mashi, fitacciyar marubuciyar online ce daga Jihar Katsina. Tana daga cikin matasan marubutan da suka ciri tuta, a fannin rubuce-rubucen almara da jarumta. Tun da ta rungumi alƙalami a shekarar 2014 har yau ba ta ajiye ba. Rubutu take yi babu kama hannun yaro, a ƙalla yanzu tana da littattafan da ta rubuta sun fi 20. A zantawarta da wakilin Manhaja Blueprint, Gimbiyar ta bayyana irin nasarorin da ta riqa samu a gasanni daban-daban, ciki har da Gasar Hikayata, Mu Gani A Ƙasa, da kuma Gasar Ɗangiwa da ba a daɗe da sanar da sakamako ba. Ta bayyana fatan ganin an samu ƙaƙƙarfar alaƙa tsakanin tsofaffin marubuta da masu tasowa da ke cin kasuwar su a yanar gizo. A sha karatu lafiya.

MANHAJA: Ina son ki gabatar mana da kanki.

AMRAH: Sunana Amrah Auwal Mashi, wacce a duniyar rubutu aka fi sani da Princess Amrah. Ni ‘yar kasuwa ce, ina sana’ar kayan maƙulashe, irin dangin su cake, samosa, doughnut da sauransu. Sannan ina rubuce-rubuce a yanar gizo dangane da abin da ya shafi girke-girke, da bayani kan abubuwan da ake soyawa na abinci da abin sha, wato dai ni Food Blogger ce. Ina watsa bidiyoyin girke-girkena a kafofin sadarwa irin su TikTok, Instagram, YouTube, da kuma Whatsapp.

Ko za mu san wani abu game da tarihin rayuwarki?

To, ni dai asalina ýar Jihar Katsina ce daga Ƙaramar Hukumar Mashi. An haife ni kimanin shekaru ashirin da biyar da suka gabata a Mashi. Na fara karatuna na firamare a nan Mashi, sannan na qarasa a Argungu ta Jihar Kebbi. Na yi karatun sakandire ɗina a wata makaranta da ake ce wa Saldefi International School, a cikin garin Katsina, na kammala a shekarar 2014.

Daga nan na shiga Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua da ke birnin Katsina, inda na karanci ilimin koyar da kimiyyar halittu, wato Biology Education. Na yi aure a shekarar 2020, a garin Abuja, sannan ina da yaro guda ɗaya a halin yanzu.

Me ya ja hankalinki ki ka fara tunanin zama marubuciya?

Asali rubutun wasan kwaikwayo a makaranta nake yi, kuma sannu a hankali sai abin ya fara shiga raina, ganin yadda ake yabawa da yadda nake rubutun. Tun daga nan sai na cigaba da rubutu, ina samun littafi ina tsara labarai, amma ba ni da hanyar fitarwa. Sai a shekarar da na kammala sakandire ne a 2014 na fara ganin ana sanya labarai a yanar gizo. Sai na ce kenan ni ma zan iya watsa nawa labaran kamar yadda wasu suka fara? Daga nan sai in ɗauki wanda yake cikin littafi in kwafe shi zuwa kan wayata, sai na fara tura shi a wani group da nake ciki mai suna ‘Mu Farka Mata’. Kamar wasa sai labarin ya fara samun karɓuwa, sai kuwa na cigaba da yin shi yana ta yawatawa a zauruka daban-daban, har a Facebook ma. Wannan shi ne mafari.

Wanene ya fara taimaka miki lokacin da za ki fara rubutu?

Gaskiya ba zan ce ga wanda ya taimaka min ba, domin kuwa ni dai da ka na shiga harkar rubutu. A karan-kaina na shiga, a karan-kaina kuma na bi hanyoyin koyonshi daga baya.

Wanne labarin ki ka fara rubutawa, kuma wanne ƙalubale ki ka fuskanta lokacin rubutawa?

Na fara da labarin ‘Mahaƙurci’, kuma babban ƙalubalen da na fuskanta shi ne, ba na son a san ina yi daga gidanmu, a ɓoye nake yi, kuma abin ka da yarinta, na san fa ba hana ni za a yi ba amma har tsakiyar dare ina farkawa in kwafa daga littafina in mayar cikin waya, sannan in tura a sauran zaurukan da nake.

Kawo yanzu kin rubuta littattafai nawa, ba mu labarin wasu daga ciki?

Ba zan iya tuna wasu ba kasantuwar an ɗan jima. Amma zan iya tunawa aƙalla ina da littattafai da na rubuta sun haura ashirin, ban da gajerun labarai. A cikin su akwai ‘Mahaqurci’, ‘Yarima Saifullah’, ‘Dodon Jatau’, ‘Dr Rafeeq’, ‘Fadila Da Nabila’, ‘Jinnul Ashiq’, ‘Zafin So’, ‘Shi Ne Sila’, ‘Ummu Haidar’, ‘Gimbiya Sa’adiyya’, ‘Ina Zan Ga Kadeey?’, ‘Wata Shari’a’, ‘Ɗaukaka Daga Allah’, ‘Xan Bautar Qasa’, ‘Ramuwar Gayya’, ‘Tsantsar Zalunci’, ‘Amrah Nake So’, ‘Wata Duniya’, ‘Bakuwar Fuska’, ‘Matar Amir, ‘Dafin So’, da sauransu. Sai ‘Hakkin Uwa’ wanda shi kuma bugagge ne ma ba iya yanar gizo ya tsaya ba.

Shi littafin ‘Amrah Nake So’, labari ne da aka gina shi a kan cutar Sikila,wato cutar Sankarar Jini, wanda ake kamuwa da ita a dalilin auren da iyaye ke yi ba tare da an yi gwajin qwayar halittar jini ta genotype ba. To, a ƙarshe dai Amrah ta faɗa cikin masu ɗauke da cutar sikila, tun tana ‘yar ƙanƙanuwarta take fama da cutar, har lokacin da ta bar duniya. A takaice dai labarin yana nuni ne da illolin da ke bibiya bayan an yi aure ba tare da gwajin genotype ba.

Shi kuma littafin Wata Duniya labarin wata baiwar Allah ne da tun tana yarinya take kaunar halittar maciji. Ta hadu da wani maciji ashe aljani ne, ta dauki tarin alkawurra a kan wannan maciji. Har bayan ta girma ya ci gaba da kashe duk wani wanda zai nuna yana ƙaunarta. A hankali har ya samu nasarar aurenta, ya mayar da ita can wata duniya, inda aljannu ne kawai suke rayuwa a cikinta. Khalid, ɗaya ne daga cikin manemanta shi ne kaɗai ya samu nasara a kan wannan aljani ta hanyar mahaifinshi da ya kasance babban malami. Ta dawo duniyarta, sannan ta ci gaba da rayuwarta bayan ta auri Khalid.

Sannan shi kuma littafin Haƙƙin Uwa wanda na ce maka an buga shi labari ne na yarinya mai suna Safiyya, wadda ta ɗauki son duniya ta ɗora a rayuwarta, ta guji mahaifiyarta a lokacin da take da tsananin buƙatarta. A karshe dai ta faɗa tafkin da-na-sani, inda ta bi wani kafiri ba tare da ta san cewa shi kafirin ba ne, ta aure shi. Daga baya da iyayenshi suka gane, babu irin wahalar da ba su gana mata ba har dai ta yi nasarar guduwa ta koma wurin mahaifiyar tata. Sai dai ta makara, ta koma a lokacin da rai ya yi halinsa, mahaifiyar tata kuma ta koma ga mahaliccinta.

Me ya ja hankalinki ki ka fara amfani da salon labarin almara na ban tsoro?

Ni mutum ce mai yawan kallon finafinan ban tsoro, sannan ina son karatunsu. To, dai abin da ya ja hankalina kenan har ni ma na fara yin ire-irensu. Kuma mabiyana ma suna son su, don haka sai na mayar da hankalina sosai a kansu.

Wacce gudunmawa shafin Aji Na Musamman da ke manhajar WhatsApp ke bayarwa wajen koyar da matasan marubuta na online sanin ƙa’idojin rubutu?

Lallai Aji Na Musamman, aji ne na musamman, kamar yadda sunansa yake haka yake da wani matsayi na musamman a zuciyata. Wata irin gudummuwa ce yake bayarwa wacce ba za ta bayyanu ba. Sai dai zan iya cewa tun da nake a duniyar rubutu, wannan zaure shi ne wuri na biyu da nake matukar farincikin kasancewa a cikinsa, bayan zauren Marubuta, saboda ina matukar ƙaruwa a cikinsa. Sannan Alhamdulillah, nima ana amfanuwa da nawa gajeren ilimin.

Kin gamsu da ƙoƙarin da tsofaffin marubuta ke bayarwa a zauruka daban daban, wajen rainon marubuta masu tasowa?

A baya akasarin manyan marubuta suna hantarar ƙanana masu tasowa, waɗanda ke neman ravarsu, don tallafa musu da ba su shawarwari. Kodayake yanzu an samu wayewar kawuna gaskiya, abubuwa sun canza. Ka ga ko ni nan an tava hantara ta har ana min gorin wai na je neman suna. Tun daga wannan lokacin ne sai na ja tsummokarana na ƙara gaba na ja girmana, a hankali yau sai gashi yanzu muna girmama juna. Yanzu Alhamdulillahi, ana samun fahimtar juna tsakanin mu matasan da ake kira marubutan online da su tsofaffin marubutan masu talifi, suna kokarin jan mu a jiki ba kamar da ba. Ana samun wasu tsofaffin marubutan da ke shigowa sahun ýan onlayin, mu ma a namu ɓangaren ana samun masu buga littafi, suna gwada yin talifin ɗaya biyu.

Wanne ƙalubale marubutan online suke fuskanta a tsakaninsu da kuma tsakaninsu da masu karatu?

Babban ƙalubalen shi ne yadda wasu ke ɗauka cewa marubuta online ba asalin marubuta ba ne, masu buga littafi a zahiri su ne marubuta na sosai. Kusan kowa haka yake ɗauka, alhalin kuma ba hakan ba ne. Da mai gurza littafi ya shigar kasuwa, da mai rubutawa a yanar gizo duk sunansu marubuta, kuma gudunmawa iri ɗaya suke bayarwa a cikin al’umma.

Yaya ki ke kallon tasirin manhajojin kasuwancin littattafai na online da ake samarwa, wajen tallata littattafan Hausa?

Gaskiya suna da tasiri sosai, domin kuwa wata hanya ce sosai ta tallata littattafai, sannan ana ƙara ƙarfafa gwiwar marubuta yanar gizo. Mutum ba zai yi rubutu kurum a karanta a wuce wurin ba, zai samu ‘yan sulallanshi.

Tsakanin hanyar da marubutan online suka saba bi na sayar da littafin su ga masu karatu, ta shafukan sada zumunta, da wannan sabon tsarin na manhajojin Hikaya da ArewaBooks, wanne ya fi samar da riba ga marubuta?

Gaskiya ni dai gare ni, gwara in shigar da littattafaina a manhajojin da aka fito da su, saboda za su fi samun kariya. A taƙaice, sai kin so su fita sannan za su fita. Amma idan wannan hanyar da muka saba bi ce, yanzun nan za ki tura wa waɗanda suka biya kuɗi, yanzu za ki ganshi yana yawo wurare daban daban.

Yaya ki ke kallon ƙalubalen satar fasaha a harkar rubutun adabi, inda wasu ke ɗaukar rubutun wasu marubuta su karanta a YouTube ba izini, ko da kuɗi ƙalilan?

Gaskiya wannan kuskure ne mai girman gaske. Ina jin ciwo in ga an yi wa wasu satar fasaha ko da ba ni aka yi wa ba. Da ciwo mutum ya sadaukar da lokacinshi ya yi rubutu amma ba tare da izini ba sai kawai wasu su yi amfani da shi ba tare da izinin mai shi ba.

Wasu na ganin bai dace a yi rubutu don kasuwanci ba, sai don faɗakarwa, menene ra’ayinki a kai?

To, ai ko sallah ma don lada ake yin ta. Ni ina ganin ko mutum zai yi faɗakarwa yana da kyau ya nemi kuɗin ma a tare. Don haka ni ban goyi bayan wannan batu ba. A faɗakar din, sannan a nemi kuɗin ma.

Wanne cigaba ƙungiyoyi da kafafen sadarwa ke bayarwa wajen shirya gasar gajeren labari a tsakanin marubuta, wanne tsari ya kamata a ce ana amfani da shi, don cigaban harkar baki ɗaya?

Wannan babban ci gaba ne sosai, domin kuwa a baya duk ba a san wannan ba, ba a san wani abu wai shi zama a shirya gasa tsakanin marubuta ba. Amma a yanzu ido ya buɗe sosai, an samu ci gaba ta yadda marubuta ke dafifin shiga gasanni, kuma abin burgewa wasu ba ma cikin ƙungiyar suke ba. Ina ba da shawara da a ƙara ba da himma, sannan a dinga neman shawarar manyan marubuta wurin shirya waɗannan gasanni, sai kuma a samu alƙalai waɗanda suka san ta kan abin sosai.

Kin taɓa shiga wata babbar gasa, wacce gasa ce a wanne shekara?

Na sha shiga gasanni. Amma gasar da na fara shiga ita ce Gasar Hikayata ta BBC Hausa, wacce na shiga a shekarar 2018 da labarina mai suna Rubutaccen Al’amari. Kuma na samu nasara tunda labarina yana ɗaya daga cikin waɗanda suka samu lambar yabo, har ma aka karanta shi a BBC. Sannan a bara ma, 2022 na shiga da labarina mai suna Komai Nisan Jifa…, shi ma kuma na ƙara samun nasara an karanta labarin nawa. Akwai gasanni ire-iren su Gusau Institute (duk da ban samu nasara ba), sannan gasar Mun Gani A Kasa, na zo gwarzuwa ta uku da labarin da na yi mai suna Shugaba Nagari. Har wa yau a 2022 ne na samu nasara a Gasar Ɗangiwa, inda cikin yardar Allah na zama gwarzuwa, wato na ɗauki kambun ta ɗaya. Alhamdulillah.

Ana samun marubuta da ke canza sheƙa daga rubutun littafi, zuwa na fim, shin kina da ra’ayin rubutun finafinai ke ma?

E, babu shakka ana samu. A baya kaɗan nima na fara koyon rubutun fim, lokacin da wani mai shirya fim ɗin Hausa ya tava neman na rubuta masa labarin da zai yi fim. Na ce masa ban taɓa yi ba, sai ya ce ai kuwa ya kamata in koya. To, daga nan sai na fara koyo. Ban sani ba ko don abin bai dame ni sosai kamar rubutun littafi ba ne ya sa na kasa mayar da hankalina kanshi yadda ya kamata. Ban dai tava yi ba gaskiya, amma ina fatan nan gaba ni ma a dama da ni.

Wanne lokaci ki ka fi samun damar yin rubutu cikin natsuwa?

Na fi samun damar yin rubutu da sanyin safiya, ina jin daɗin rubutu a lokacin, sannan ba ni da uzuri da zai hana ni yi.

Wacce shawara ki ke fi son baiwa marubuta, da za ta kawo musu cigaba?

Ina ba su shawara da su yi biyayya ga na sama da su. Duk wanda suka ga ya fi su su zama masu ƙasƙantar da kansu, domin su koya. Wanda duk ya yi wa na sama da shi ya fi ganin daidai a rayuwarshi, shi kanshi rubutun za ka fi samun ilimin yin sa. Sannan kafin mutum ya faɗa harkar rubutu ka’in da na’in ya zamana ya nemi ilimi a kansa, kar ya faɗa masa ta ka. Sai kuma su zama makaranta, domin ba za su taɓa zama cikakkun marubuta ba, sai sun zama masu karatu su ma.

Wacce karin magana ce take tasiri a rayuwar ki?

Ɗan Hakin Da Ka Raina…domin tabbas ɗan hakin da ka raina shi yake tsole maka ido. Ba zan manta da yadda na faro ba da farko, sai ga shi Alhamdulillahi komai ya zamto labari. Sunana ya zaga inda kafafuwana ba su taɓa mafarkin zuwa ba.

Na gode.

Ni ma na gode.