A fara koyon mulki da baki kafin a fara koyon mulki da hannu

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Yanzu dai kusan za a iya cewa, sabuwar gwamnati ta fara kankama sosai, yayin da ake cigaba da naɗe-naɗen masu dafa wa ayyukan gwamnati, da zaɓen shugabannin Majalisar Ƙasa zango na goma.

’Yan siyasa da masu riƙe da muƙaman gwamnati sun yi rawar gani wajen tabbatar da cewa, waɗanda za a bai wa waɗannan muƙamai masu muhimmanci ba su ta fi a ɓangare guda ba. Babu ma kamar yadda aka riƙa qorafin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta Musulmi da Musulmi ce, saboda yadda gambizar Shugaban Ƙasa da Mataimakinsa, ɗan Kudu da ɗan Arewa, duk suka zama mabiya addinin Musulunci ne.

Mai yiwuwa ƙoƙarin wanke kansu da canza tunanin ’yan Nijeriya na ganin gwamnatin su ba za ta yi wa wani ɓangare na ’yan ƙasar adalci ba, ya sa a kwanakin baya Mataimakin Shugaban Ƙasa Sanata Kashim Shettima yayin wani taron musanyen ra’ayoyi tsakanin ’yan Majalisar Dattijai dangane da batun zaɓar shugabannin da za su jagoranci majalisar a Zango Na Goma, ya yi wasu kalamai da ke nuna goyon bayansa ga zaɓen Sanata Godswill Akpabio da Sanata Barau Jibrin, a matsayin shugaba da mataki, kalaman da suka zame masa qalubale a siyasar sa.

Kodayake Fadar Shugaban Ƙasa ta bakin kakakinta, mai kula da harkokin watsa labarai da samar da bayanai a ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Olusola Abiola, ta ce an murguɗa zancen ne don wani son zuciya na siyasa.

An jiyo Mataimakin Shugaban Ƙasar na cewa, “A halin da wannan gwamnati ke ciki a yanzu baragurbin Kirista ɗan Kudu ya fi Musulmi ɗan Arewa cancanta da shugabancin Majalisar Dattijai a zango na goma.”

Waɗannan kalamai sun yi matuƙar harzuƙa Musulmi a cikin Nijeriya, musamman ‘yan siyasar Arewa da magoya bayan su, waɗanda ke ganin kamar Mataimakin Shugaban Ƙasar ya watsa musu ƙasa a ido ne. Ko kuma ya fifita wanda ba Musulmi ba, kan ɗan uwansa mai Sallah.

Sai dai fadar Shugaban Ƙasa ta ce, an siyasantar da jawabin nasa ne kawai, amma ba wai yana fifita Kirista ko Ɗan Kudu a kan Ɗan Arewa Musulmi ba ne.

Yana bayani ne game da muhimmancin samar da haɗin kai da fahimtar juna a tsarin tafiyar da gwamnati, domin bai wa kowanne ɗan qasa damar bayar da tasa gudunmawa a cikin wannan sabuwar gwamnatin.

Masu hikimar magana suna cewa, Magana Zarar Bunu Ce. Dole ne shugabanni su zama masu hikimar sarrafa harshe da iya siyasa cikin maganganun su, ta yadda za su kaucewa yin suvul da baka a yayin da suke gaban jama’a, kan idon ‘yan jarida da abokan adawar siyasa. Duk da irin yadda fadar Shugaban Ƙasa da shi kansa Mataimakin Shugaban suka yi ta ƙoƙarin canja ma’anar abin da ya faxa don su fahimtar da jama’a abin da yake nufi a kalaman nasa, za a daɗe ba a daina zargin Kashin Shettima da raunin imani ko fifita ra’ayin siyasa kan na addini ba.

Kamar dai yadda aka riƙa yi wa wasu kalamai da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya tava yi kan ko Allah na amsa addu’ar talakawa. Na san wasun mu sun iya tunawa da abubuwan da suka faru a lokacin.

Yana daga cikin ƙa’idojin zama shugaba nagari, a samu mutumin da ya iya maganganu na girmamawa da dattaku, wanda kalamansa ke ƙarfafa zukata, suke ƙara ƙwarin gwiwa, da haɗe kan mabiyansa, ta hanyar amfani da zaɓaɓɓun kalmomi na hikima da azanci.

Mutumin da idan yana magana za a ji babu ƙarya ko yaudara, ko nuna ƙyama da wariya.

Shugabanni da dama na duniya sun samu ƙarfin iko da tasiri a zukatan jama’ar su ta dalilin yadda kalamansu ke tava zuciyoyin jama’a, idan sun yi magana ana samun natsuwa da sa ran faruwar wani abu na alheri a kusa.

Tsohon Shugaban Ƙasar Amurka, Ronald Reagan na Daga cikin irin waɗannan shugabannin, saboda yadda jama’a ke girmama shi da jin daɗin azancin kalamansa.

Faruwar wannan al’amari ya sa jama’a musamman manazarta daga ’yan Arewa suka fara bayyana muhimmancin ‘yan siyasarmu na Arewa da shugabanni su iya bakinsu.

Su san irin maganganun da za su yi, da inda ya dace su furta, babu ma kamar idan ya shafi magana ta addini ko vangaranci, wanda yake saurin sosa zukatan jama’a.

Hikimar iya magana da amfani da kalmomi na kwantar da hankali da jan ra’ayin masu sauraro. Kamar yadda masu azancin magana ke cewa, kyakkyawar magana na mayar da Zaki Akuya.

Yadda shugaba yake magana yana iya ɗaga darajarsa ko zubar da kimarsa a idon mabiyansa ko masu sauraronsa.

Wannan dambarwa sai ta tuna min da wani labari a littafin Magana Jari Ce, wanda aka yi wa taken darasin mu na wannan mako, fara koyon mulki da baki kafin a fara koyon mulki da hannu.

’Yan uwana almajirai ma’abota karatun littattafan Hausa ba za su kasa sanin wannan labari mai cike da darrussan masu yawa ba, wato labarin Gauraka da Kunkuru.

Labari ne da ke koyar da zamantakewa da kuma iya kawar da kai daga surutan mutane. Gauraku dake hawa bishiyar ɓaure suna ci suna zubarwa a ƙasa, har Kunkurun da ke qasan bishiyar yana samun na kalaci. Ya yi zaton suna zubo masa da vauren qasa ne don zumunci, bai san kubce musu vauren yake ba.

Bayan janyewar damina, da ƙafewar rafuka, da ƙarewar vaure a kan bishiya, ya sa Gauraku shirin yin ƙaura zuwa wani waje mai damshi, sai Kunkuru ya ce shi ma zai bi su, duk kuwa da kasancewar ba shi da fukafuki. Har sun so nuna rashin yiwuwar hakan, amma sai ya kawo musu wata dabara na amfani da kara, inda kowanne Gauraki zai kama gefe da bakinsa, shi kuma Kunkuru zai kama tsakiya da bakinsa, amma bisa sharaɗin Kunkuru zai kame bakinsa ya yi shiru, ko me za a ce, kuma ko me zai gani. Sai dai kash, Kunkuru bai samu iya cin wannan jarabawa ba, domin kuwa lokacin da suka zo wucewa ta saman kasuwar wani ƙauye, mutane suka hango wucewarsu, sai suka fara nuna su da hannu suna mamakin abin da ke faruwa. Sai Kunkuru ya kasa daurewa ya buɗe baki ya yi magana, nan take kuwa ya suvuto ya faɗo ƙasa. Gaurakun nan kuwa suka wuce suka bar Kunkuru a ƙasa.

Masu son karanta cikakken labarin za su iya neman littafin Magana Jari na ɗaya, don karanta wannan labari da wasu da dama. Amma dalilin kawo shi cikin wannan rubutu shi ne in ja hankalin mai karatu da shugabanni su gane muhimmancin yin maganar da ta dace a wurin da ya kamata.

Idan aka ce yau wane shugaba ne to, wajibi ne ya san irin dabaru da hikimar da ake buƙata a wajen shugaba. Ba kowacce magana zai furzar ba, kuma ko ya dace ya yi maganar to, ya san kalmomin da zai yi amfani da su, domin kare mutuncinsa, da matsayin da yake riƙe da shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *