An kafa dokar hana fita a Balanga saboda rikicin ƙabilanci

Daga WAKILINMU

A Talatar da ta gabata Gwamnatin Jihar Gombe ta kafa dokar hana zirga-zirga na sa’o’i 24 a wasu ƙauyukan jihar da suka haɗa da Nyuwar, Jessu, Heme, Yolde Gelentuku, Sikam, Wala-Lunguda da kewaye.

Matakin sanya dokar ya biyo bayan sabon rikicin ƙabilancin da ya ɓarke ne tsakanin ƙabilar Lunguda da Waja da ke yankin Ƙaramar Hukumar Balanga ran Talata.

Sakataren Gwamnatin Jihar, Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi, shi ne ya ba da sanarwar kafa dokar, tare da cewa buƙatar kafa dokar ta taso ne don dawo da zaman lafiya a yankunan da rikicin ya shafa.

Ya ce tuni an tura jami’an tsaro don kula da lamurra a yankunan da lamarin ya shafa.

Ya ƙara da cewa dokar hana zirga-zirgar ta soma aiki ne nan take wadda kuma za ta ci gaba da aiki har sai abin da Allah Ya yi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *