Editor

9513 Posts
Ƙarancin mai ya kunno kai sa’o’i bayan da Shugaba Tinubu ya sanar da cire tallafin mai

Ƙarancin mai ya kunno kai sa’o’i bayan da Shugaba Tinubu ya sanar da cire tallafin mai

Da alama layukan ababen hawa a gidajen mai ya dawo a Jihar Legas sa'o'i bayan da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya sanar da cire tallafin mai. Bayanai sun ce an ga cinkoson ababen hawa a gidajen mai ɗin NNPC a yankunan Ikeja da Alausa waɗanda ke jiran su sha mai. Ya zuwa haɗa wannan labari, an ga da daman gidan mai masu zaman kansu a yankunan ba su sayar da mai. A jawabinsa, Shugaba Tinubu ya ce masu ƙumbar susa kaɗai ke amfna da tallafin mai amma ban da talakawa. Ya ce, “Mun yaba da ƙoƙarin gwamnati mai barin gado…
Read More
Shugaba Tinubu ya yi naɗe-naɗen farko a bayan shan ratsuwa

Shugaba Tinubu ya yi naɗe-naɗen farko a bayan shan ratsuwa

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi naɗaɗen farko a matsayinsa na Shugaban Ƙasa. Wannan na zuwa ne a ranar da ya sha rantsuwar kama aiki, wato Litinin 29 ga Mayu, 2023. Waɗanda ya naɗa sun haɗa da Ambasafa Kunle Adeleke Babban Jami'in Tsare-tsare (SCOP) ga Shugaban Ƙasa, Dele Alake a matsayin Kakakin Shugaban Ƙasa, sannan Olusegun Dada a matsayin Mai Bada Shawara Kan Sha'anin Yaɗa Labarai na Zamani. Sa'ilin da yake jawabi jim kaɗan bayan shan ratsuwar kama aiki, Tinubu ya yi alƙawarin kafa majalisarsa cikin 'yan kwanaki ko makonni.
Read More
Zan bar Nijeriya fiye da yadda na same ta a 2015 – Saƙon Buhari na bankwana ga ‘yan Nijeriya

Zan bar Nijeriya fiye da yadda na same ta a 2015 – Saƙon Buhari na bankwana ga ‘yan Nijeriya

Daga AMINA YUSUF ALI A cikin abin da ya kira da aikinsa ba ƙarshe a gadon mulki, Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya roƙi 'yan Nijeriya yafiya idan akwai inda aka samu wani tsari daga tsarukan da gwamnatinsa ta gudanar da ya yi wa wani a cikinsu ciwo a cikin shekaru 8 da ya shafe a kan gadon mulki. Shugaban kasar ya yi wannan kira ne a wani jawabi da ya yi a wani shiri da ya gabatar kai tsaye a ranar Lahadin da ta gabata. Buhari zai mika ragamar mulki ga sabuwar gwamnati a ranar Litinin. A cikin jawabinsa na…
Read More
Zan maida hankali kan rashin tsaro, noma, samar da ayyuka, cewar sabon Gwamnan Zamfara

Zan maida hankali kan rashin tsaro, noma, samar da ayyuka, cewar sabon Gwamnan Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Sabon Gwamnan Jihar Zamfara, Dr. Dauda Lawal Dare, ya yi alƙawarin bayar da muhimmanci kan fannonin tsaro, noma, samar da ayyukan yi da samar da ababen more rayuwa domin cigaban jihar. Gwamna Dauda ya bayyana haka ne a wajen bikin rantsar da gwamnatinsa da aka gudanar a cibiyar kasuwanci ta Zamfara ranar Litinin . A cewarsa, an samu rahoton rashin tsaro a jihar Zamfara sakamakon ayyukan ‘yan ta’adda, don haka akwai buƙatar gwamnatinsa ta haɗa kai da Gwamnatin Tarayya domin ceto jihar don a samun dawamammen zaman lafiya. "Za mu tsara duk dabarun da za…
Read More
RTEAN ta naɗa shugaban riƙo na Legas

RTEAN ta naɗa shugaban riƙo na Legas

Ƙungiyar Masu Motocin Sufuri ta Nijeriya, RTEAN, ta naɗa Areshola Kudus a matsayin shugaban riƙon ƙwarya na RTEAN na Jihar Legas. Bayanin naɗin na ƙunshe ne cikin sanarwar manema labarai da ƙungiyar ta fitar mai ɗauke da sa hannun Babban Sakataren Ƙungiyar na Ƙasa, Comared Yusuf Ibrahim Adeniyi Mataimakin Shugaban RTEAN na uku na shiyyar Kudu maso Yamma, Barista Samuel Olugbenga Agbede, ya shaida wa manema labarai cewa an cimma matsayar naɗa Kudus a wannan matsayin yain taron da shugabancin ƙungiyar ƙarƙashin jagorancin Dr. Musa Muhammed Maitakobi ya gudanar a ranar 24 ga Mayu, 2023 ya gudanar a RTEAN House.…
Read More
Kano ta zama ta Gwamna Abba Kabir a hukumance

Kano ta zama ta Gwamna Abba Kabir a hukumance

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano An rantsar da Injiniya Abba kabir Yusuf a matsayin Gwamnan Jihar Kano a ranar Litinin. Taron rantsuwar ya gudana ne a filin wasa na Sani Abacha da ke Ƙofar Mata a birnin Kano. An rantsar da shi ne tare da mataimakinsa, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, wanda suka gaji kujerar daga Dr Abdullahi Umar Ganduje da Mataimakinsa, Dr Nasiru Yusuf Gawuna. Dubunnan magoya bayan jam'iyyar NNPP ne suka halarci biki sanye da fararen kaya, huluna da jajayen rawunna ga maza, su kuma mata ke sanye da jajayen ɗan-kwali, wasu kuma jan mayafi, yayin da wasu suka…
Read More
An rantsar da Raɗɗa a matsayin sabon Gwamnan Katsina

An rantsar da Raɗɗa a matsayin sabon Gwamnan Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina An rantsar da Dakta Dikko Umar Raɗɗa a matsayin sabon Gwamnan Jihar Katsina da mataimakinsa, Faruq Lawal Jove, a ranar Litinin da misalin ƙarfe 10:40 na safe. Bikin rantsarwar ya gudana ne a filin wasa na Muhammadu Dikko da ke Katsina, babban birnin jihar. Babban mai shari'a na jihar, Musa Ɗanladi Abubakar ne ya rantsar da Gwamnan tare da mataimakinsa a gaban ɗimbin magoya baya. Raɗɗa shi ne wanda Jam'iyyar APC ta tsayar takarar gwamna a jihar a babban zaɓen da ya gabata. Inda a ranar 18 ga watan Mayu, 2023, Hukumar Zaɓ INEC, ta…
Read More
Buhari da mai ɗakinsa sun bar Abuja zuwa Daura

Buhari da mai ɗakinsa sun bar Abuja zuwa Daura

Daga UMAR GARBA a Katsina Tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bar babban birnin tarayya Abuja a ranar Litinin bayan da ya halarci rantsar da sabon Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tunubu a dandalin taro na Eagle Square a Abuja. Jirgin tsohon shugaban ƙasar ya ɗaga sama da misalin ƙarfe 12 na rana zuwa mahaifarsa, Daura, a jihar Katsina. Jirgin saman sojojin Nijeriya mai lamaba 5N FGW ne ya ɗauke shi. Buhari yana tare da maiɗakinsa, Aisha Buhari da kuma ɗansa Yusuf sai kuma kaɗan daga cikin masu yi masa hidima. Majiyar Manhaja ta ƙara da cewa, jim kaɗan bayan tashin…
Read More
Shugabancin Kano: Zan binciki bashin N241bn, cewar Abba Kabir ga Ganduje

Shugabancin Kano: Zan binciki bashin N241bn, cewar Abba Kabir ga Ganduje

Sabon Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sha alwashin gudanar da bincike kan bashin da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta ciyo na Naira biliyan 241. Gwamna Yusuf ya ce takardun bayanan gwamnati da Ganduje ya miƙa ta hannun Sakataren Gwamnatin Jihar mai barin gado, ba su wadatar ba. Ya caccaki Ganduje kan rashin tasayawa ya miƙa ragamar mulki da kansa, amma ya wakilta wani maimakon haka. A cewar Yusuf: “Takardun bayanan gwamnatin sun yi mana kaɗan. Haka ma bayanan kwamitin miƙa mulki ba su da yawa. “Babu abin da za mu iya yi a matsayinmu na wakilan jama'a, ba…
Read More
An rantsar da Dauda Lawal a matsayin Gwamnan Zamfara

An rantsar da Dauda Lawal a matsayin Gwamnan Zamfara

An rantsar da Dauda Lawal Dare a matsayin sabon gwamnan Jihar Zamfara a hukumance. Bikin rantsarwar ya gudana ne a ranar Litinin a filin kasuwar baje koli da ke Gusau, babban birnin jihar. Dauda ya zama sabon gwamnan jihar ne bayan da ya lashe zaɓen gwamnan jihar ƙarƙashin Jam'iyyar PDP inda ya samu ƙuri'u 377,726. Dauda ya doke babban abokin hamayyarsa Jam'iyyar APC kuma gwamnan jihar a wancan lokaci, Bello Matawalle, wanda ya tsira da ƙuri'u 311,976.
Read More