An rantsar da Raɗɗa a matsayin sabon Gwamnan Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina

An rantsar da Dakta Dikko Umar Raɗɗa a matsayin sabon Gwamnan Jihar Katsina da mataimakinsa, Faruq Lawal Jove, a ranar Litinin da misalin ƙarfe 10:40 na safe.

Bikin rantsarwar ya gudana ne a filin wasa na Muhammadu Dikko da ke Katsina, babban birnin jihar.

Babban mai shari’a na jihar, Musa Ɗanladi Abubakar ne ya rantsar da Gwamnan tare da mataimakinsa a gaban ɗimbin magoya baya.

Raɗɗa shi ne wanda Jam’iyyar APC ta tsayar takarar gwamna a jihar a babban zaɓen da ya gabata.

Inda a ranar 18 ga watan Mayu, 2023, Hukumar Zaɓ INEC, ta sanar da shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar da ƙuri’a 859,892.

Raɗɗa shi ne na biyar a jerin gwamnonin da za su mulki jihar a ƙarƙashin tsarin dimokaraɗɗiya, ya kuma riƙe mukamin shugaban hukumar ƙanana da matsakaitan masana’antu ta ƙasa, (SMEDAN). Sannan ya taɓa kasancewa tsohon shugaban ma’aikata na fadar gwamnatin jihar, ya kuma shugabanci Ƙaramar Hukumar Charanchi dake jihar.

Gwamna mai barin gado, Aminu Bello Masari da mataimakinsa Mannir Yakubu da sauran manyan jami’an gwamnati na daga cikin waɗanda suka halarci bikin rantsuwar.

Sauran manyan baƙi a wurin sun haɗa da Gwamnan Jihar Maraɗi ta Nijar, Abubakar Shuaibu da tsohon Gwamnan jihar ta Katsina, Ibrahim Shehu Shema da tsohon Gwamnan Kaduna Abba Musa Rimi da sauransu.