Kano ta zama ta Gwamna Abba Kabir a hukumance

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

An rantsar da Injiniya Abba kabir Yusuf a matsayin Gwamnan Jihar Kano a ranar Litinin.

Taron rantsuwar ya gudana ne a filin wasa na Sani Abacha da ke Ƙofar Mata a birnin Kano.

An rantsar da shi ne tare da mataimakinsa, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, wanda suka gaji kujerar daga Dr Abdullahi Umar Ganduje da Mataimakinsa, Dr Nasiru Yusuf Gawuna.

Dubunnan magoya bayan jam’iyyar NNPP ne suka halarci biki sanye da fararen kaya, huluna da jajayen rawunna ga maza, su kuma mata ke sanye da jajayen ɗan-kwali, wasu kuma jan mayafi, yayin da wasu suka sanya jan hijabi.

Jagorori daban-daban daga jihar da ma sarakunan jihar tare da Injiniya Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, sun halarci taron.

Abba Kabir Yusuf na Jam’iyyar NNPP shi ne wanda ya yi nasara a zaɓen da aka gudanar ranar 18 ga watan Maris inda ya doke ɗan takarar jam’iyya mai mulki, APC, Nasiru Yusuf Gawuna.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *