Editor

9513 Posts
An sauya wa Kakakin ‘yan sandan Katsina wurin aiki

An sauya wa Kakakin ‘yan sandan Katsina wurin aiki

Daga UMAR GARBA a Katsina Babban Sufeton 'Yan Sandan Nijeriya, Usman Baba, ya bada umarnin sauya wa Kakakin rundunar 'yan sanda na jihar Katsina, CSP Gambo Isah, wurin aiki. An sauya shi daga hedikwatar rundunar 'yan sanda ta jihar Katsina zuwa shiyya ta 14, inda zai ci gaba da riƙe muƙamin na kakakin 'yan sanda a jihohin Katsina da Kaduna da ke shiyyar ta 14. Sauyin wurin aikin na zuwa ne bayan da wata 'yar jarida Ruƙayya Aliyu Jibiya ma'aikaciya a tashar Tambarin Hausa, ta fallasa cewar Kakakin rundunar ya ci zarafinta bayan da ya jagoranci wata tawagar 'yan sanda,…
Read More
KAROTA za ta baza jami’ai 1,000 domin yin aiki a bikin rantsuwar Kano

KAROTA za ta baza jami’ai 1,000 domin yin aiki a bikin rantsuwar Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Jihar Kano, KAROTA, ta ce, ta ware jami’anta guda 1,000 da za su kula da zirga-zirgar ababen hawa a ranar bikin rantsuwar sabon gwamna da zai gudana ranar Litinin. Shugaban hukumar kuma Daraktanta na Mulki, Alhaji Abdullahi Yahuza, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Nabilusi Abubakar Kofar Nai’sa, ya fitar a ranar Asabar. Nabulusi ya ce, an ware jami’an KAROTA ne domin kula da kaiwa da komowar ababen hawa. Ya kuma ce, “Za a rufe wasu daga cikin titunan da…
Read More
Buhari da Tinubu: Ta faru ta ƙare!

Buhari da Tinubu: Ta faru ta ƙare!

*Yayin da Tinubu ya kammala shirin amsar mulki…*Buhari ya yi sabbin naɗe-naɗe 33 kwanaki shida kafin miƙa mulki*Dalilin da ya sa Buhari ke ta ɗaukar matakai – Fadar Shugaban Ƙasa *Ana shirin kawo cikas ga bukukuwan miƙa mulki a jihohi da ƙasa, inji DSS*Sa'o'i kafin miqa mulki Buhari ya umarci ministocinsa su cigaba da aikinsu*Ƙananan ministoci ba su da amfani a gwamnatin Buhari – Keyamo Daga MAHDI M. MUHAMMAD A ranar Litinin, 29 ga Mayu, 2023, gwamnatin sabon Shugaban Nijeriya mai jiran gado, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, za ta fara aiki a matsayin halastacciyar zaɓaɓɓiyar gwamnatin farar hula, yayin da…
Read More
RTEAN ta yunƙura domin rage aukuwar haɗurra

RTEAN ta yunƙura domin rage aukuwar haɗurra

Daga BASHIR ISAH Ƙungiyar Masu Motocin Sufuri ta Nijeriya (RTEAN), ta gabatar da shiri na musamman don kulawa da kafin da baya aukuwar haɗurra a hanyoyin ƙasar nan domin rage yawan asarar rai sakamakon hatsarin abubuwan hawa. Sa'ilin da yake ƙaddamar da shirin a ranar Laraba a Abuja, Shugaban RTEAN na ƙasa, Dr Musa Maitakobi, ya bayyana cewa shirin na da manufar samar da sukuni game da tafiye-tafiye a hanyoyi ba tare da fuskantar wata matsala ba. Shugaban wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Ambasada Muhammad Abubakar, ya ce an tsara shirin da kuma samar da shi ne daidai da Dokar…
Read More
Buhari ya naɗa Sha’aban Sharaɗa a matsayin Babban Sakataren Hukumar Almajirai ta Ƙasa

Buhari ya naɗa Sha’aban Sharaɗa a matsayin Babban Sakataren Hukumar Almajirai ta Ƙasa

Daga IBRAHIM HAMISU Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya amince da naɗin ɗan majalisar wakilai mai barin gado mai wakiltar Ƙaramar Hukumar birnin Kano, Sha’aban Sharaɗa a matsayin Babban Sakataren Zartarwa na sabuwar Hukumar Almajirai ta Ƙasa. Mai magana da yawun shugaban Buhari mai barin gado Malam Garba Shehu ne ya tabbatar da hakan a daren Lahadi a Abuja. A cewar Shehu, naɗin Sharaɗa ya biyo bayan amincewar da Shugaban Ƙasa ya yi ne na samar da hukumar kula da almajirai da ilmin yara ta kasa ta 2023. Sharaɗa ya yi Digiri na farko a fannin jarida a Jami’ar Bayero ta…
Read More
Kuskure ne ɗaukar doka a hannu kan waɗanda ake zargi da ƙwacen waya – Ashiru Yakasai

Kuskure ne ɗaukar doka a hannu kan waɗanda ake zargi da ƙwacen waya – Ashiru Yakasai

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Ƙungiyar masu hada-hadar sayar da wayar salula a Jihar Kano da aka fi sani da AMPAT ta koka akan matakin ɗaukar doka a hannu da al'ummar Kano suka soma ɗauka na ƙone babura masu ƙafa uku da ake zargin na masu ƙwacen waya ne da cewa kuskure ne. Kakakin ƙungiyar na AMPAT, Alhaji Ashiru Yusuf Yakasai ne ya bayyana hakan a cikin wata hira da ya yi da manema labarai. Ya ce ɗaukar irin wannan matakin bai kamata ba saboda za ta iya shafar wanda ba ruwansa. Ashiru Yusuf ya yi nuni da cewa abinda…
Read More
Abin da ya sa muka rinƙa ciyo bashi a shekaru takwas na mulkin Buhari – Minista

Abin da ya sa muka rinƙa ciyo bashi a shekaru takwas na mulkin Buhari – Minista

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari mai barin gado ta kare matakin da ta ɗauka na ciwo basussuka masu ɗimbin yawa a ciki da wajen ƙasar a shekaru takwas da ta shafe ta na mulki. Basussukan da ƙasar ta ciyo ya sa wasu 'yan Nijeriya da masana tattalin arziki sun nuna damuwa a kan matsalolin da ƙasar za ta iya fuskanta sakamakon yawan basussukan. Sai dai Ministar Kuɗi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki ta Ƙasa ta Nijeriya, Zainab Shamsuna Ahmed ta shaida wa BBC cewa gwamnati ta karvo bashin ne domin hana ƙasar faɗawa cikin mawuyacin hali…
Read More
CBN ta ƙwace lasisin wasu bankuna 132

CBN ta ƙwace lasisin wasu bankuna 132

Daga AMINA YUSUF ALI Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya amince da soke lasisin da aka ba wasu bankunan ƙananan kasuwanci 132 da suke harkokinsu a Nijeriya. Emefele ya amince da amshe lasisin a ranar Litinin ɗin da ta gabata, a cewar wani jawabi da CBN ɗin ya saki a ranar Talata. A cewar jawabin, Bankin ya ƙaddamar da hukunci a kan ƙananan bankunan kasuwanci bankunan da ba sa yin biyayya ga ƙa'idojin CBN da kuma sharuɗɗan amfani da lasisin. Daga cikin dalilan da ya sa bankin ya ƙwace lasisin, ya bayyana cewa ya ƙaddamar da wannan aikin…
Read More
Aski ya zo gaban goshi!

Aski ya zo gaban goshi!

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Akan ce idan aski ya zo gaban goshi ya fi zafi, amma da alamu irin askin wanzamai na asali a ke magana masu aiki da ask aba irin waɗannan masu aski a shagunan zamani a na kallon akwatin talabijin ko a kunna faifan kiɗa a cikawa mutane kunne. Manufa a nan ina son magana kan kammala mulkin shugaba Buhari na tsawon shekaru 8 da kuma shirin shigowar sabuwar gwamnati da Insha Allah kafin mu dawo sabon babi an fara ƙidayar kwanaki a sabuwar gwamnatin. Shin ko jami’an gwamnatin mai barin gado na son tafiya ko so…
Read More