Buhari da Tinubu: Ta faru ta ƙare!

*Yayin da Tinubu ya kammala shirin amsar mulki…
*Buhari ya yi sabbin naɗe-naɗe 33 kwanaki shida kafin miƙa mulki
*Dalilin da ya sa Buhari ke ta ɗaukar matakai – Fadar Shugaban Ƙasa

  • *Ana shirin kawo cikas ga bukukuwan miƙa mulki a jihohi da ƙasa, inji DSS
    *Sa’o’i kafin miqa mulki Buhari ya umarci ministocinsa su cigaba da aikinsu
    *Ƙananan ministoci ba su da amfani a gwamnatin Buhari – Keyamo

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

A ranar Litinin, 29 ga Mayu, 2023, gwamnatin sabon Shugaban Nijeriya mai jiran gado, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, za ta fara aiki a matsayin halastacciyar zaɓaɓɓiyar gwamnatin farar hula, yayin da daga ƙarfe 12:00 na tsakar dare ranar Lahadi, 28 ga Mayu, 2023, gwamnatin Shugaban Nijeriya mai barin gado, Muhammadu Buhari, ke ƙare wa’adinta na mulki.

Yayin da wa’adin ranar musayen gwamnatin ke ƙaratowa, abubuawa na cigaba da faruwa, musamman a cikin wannan mako mai ƙarewa da ma makonni ƙalilan da suka gabata, waɗanda ke haifar cece-kuce da ɓarin zance tare da luguden laɓɓa, saboda ganin yadda Gwamnatin Shugaba Buhari ke ta faman ɗaukar wasu matakai na ayyuka cikin gaggawa, waɗanda ba a saba ganin ta da himmar yi hakan ba a tsawon shekaru takwas da ta kwashe a gadon karagar mulki.

Kodayake dai an san cewa, bakin alƙalami ya riga ya bushe, ma’ana dukkan wasu matakai da za a iya ɗauka a wannan lokaci ba za su dakatar da komai game da bikin rantsar da sabuwar gwamnati ko ƙarewar wa’adin sabuwar gwamnati a Nijeriya ba, don haka ake kallon lamarin a matsayin tafu ta ƙare, wai an yi wa mai dami ɗaya sata!

Blueprint Manhaja ta tattaro wasu daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a lokacin da ake dab da miƙa mulki ga sabuwar gwamnatin Tinubu. A sha karatu lafiya!

Buhari ya yi sabbin naɗe-naɗe 33 kwanaki shida kafin miƙa mulki
Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya amince da naɗin sabbin daraktoci kusan 33 a hukumomi daban-daban kwanaki shida kafin miƙa wa sabuwar gwamnati mulki.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da aka sanya wa hannu a ranar Talata, 23 ga Mayu, 2023, ta hannun Shugaban Manema Labarai da Hulɗa da Jama’a na ma’aikatar Sufurin Jiragen Sama da Sararin Samaniya, Odatayo Oluseyi.

A cewar sanarwar, sabbin naɗe-naɗen za su taimaka wajen sake canja Hukumomin don yin ayyukansu na doka kamar yadda aka tanada a cikin Kundin Ayyuka da kuma taimakawa wajen magance matsaloli a wurare.

Sai dai sake fasalin ya sanya aka naɗa Kabir Yusuf Mohammed a matsayin sabon Manajan Darakta kuma Babban Jami’in Hukumar Filayen Jiragen Sama ta Nijeriya, FAAN.

Hakazalika, an naɗa Injiniya Tayib Odunowo a matsayin babban Manajan Daraktan Hukumar Kula da Sararin Samaniya ta Nijeriya (NAMA) da zai karɓi ragamar aiki daga hannun Matthew Lawrence Pwajok wanda ya koma babban matsayinsa na Daraktan Ayyuka na Hukumar.

Manyan darektoci na Hukumar Binciken Tsaro ta Nijeriya (NSIB), Injiniya Akin Olateru; Hukumar Kula da Yanayi ta Nijeriya (NiMet), Farfesa Mansur Matazu da Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Nijeriya (NCAA), Kyaftin Musa Nuhu ne za su gudanar da sauran ayyukansu kamar yadda dokar ta kafa hukumominsu.

Haka kuma, Shugaban Kwalejin Fasahar Jiragen Sama ta Nijeriya, Kyaftin Bako Mansur Modibo, an ƙara masa wa’adin shekara ɗaya, kamar yadda dokar kafa kwalejin ta tanada.

Ƙananan ministoci ba su da amfani a gwamnatin Buhari – Keyamo:

Ƙaramin Ministan Ƙwadago da Ayyuka na Nijeriya mai barin-gado, Festus Keyamo (SAN), ya gaya wa Shugaba Muhammadu Buhari mai barin-gado cewa naɗa muƙamin qaramin minista ya saba wa tsarin mulkin ƙasar.

Keyamo wanda babban lauya ne a Nijeriya ya faɗi hakan ne a ranar Laraba, lokacin da yake gabatar da jawabinsa a zaman majalisar zartarwa na ban-kwana domin kawo ƙarshen majalisar, wanda Shugaba Buhari ya jagoranta a Abuja.

Ƙaramin ministan ya nuna cewa wannan muqami da ake bai wa mutane yawanci da sunan gwamnatin haɗin kan qasa kusan ba ya aiki a zahiri ga yawancin waɗanda ake naɗawa a matsayin.

Domin ba wani ƙarfi na a-zo-a-gani da suke da shi, lamarin da a wani lokacin ma yake haɗa su rigima da wanda yake ainahin matsayin ministan.

Ya ƙara da cewa, yawancin waɗanda gwamnatocin baya suka naɗa wa a wannan muƙami sun ƙi fitowa su yi magana ne saboda kar a ga ba su gode wa shugabannin ƙasar da suka ba su muaamin ba.

Festus Keyamo shi ne kakakin rusasshen kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na Tinubu da Shettima.

Bikin rantsarwa: DSS ta bankaɗo aniyar masu son kawo cikas ga bikin:

Rundunar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta ce, tana sane da shirye-shiryen da wasu ɓata gari ke yi na tarwatsa bikin rantar da shugaban ƙasa da gwamnoni a ranar 29 ga watan Mayu a faɗin Nijeriya.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, Dakta Peter Afunanya, ya fitar a ranar Alhamis, 25 ga watan Mayu.

Afunanya ya ce, manufar ita ce kawo karan tsaye ga ƙoƙarin hukumomin tsaro wajen tabbatar da gudanar da bikin cikin zaman lafiya da haifar da tsoro da fargaba tsakanin al’umma.

Rundunar ta shawarci ’yan Nijeriya da su bi ƙa’idojin tsaro da aka gindaya da kyau yayin gudanar da bikin rantsarwar.

Kakakin rundunar ya ƙara da cewa, ana gargaɗin waɗanda ba a ba izini ba da su nisanci wuraren da aka keve da wasu wurare na musamman a wajen taron.

Wani ɓangare na sanarwar ta cewa,  “Idan za a iya tunawa a ranar 18 ga watan Mayun 2023, babban Sakataren Gwamnatin Tarayya kuma shugaban kwamitin miƙa mulki na shugaban ƙasa (PTC) ya gudanar da taron manema labarai inda ya bayyana tsare-tsaren rantsar da shugaban ƙasa.

Babban lamari a cikin tsare-tsaren shi ne rantsar da shugaban ƙasa a ranar 29 ga watan Mayun 2023 a Abuja. A wannan rana ne za a kuma rantsar da sabbin gwamnoni a yawancin jihohi.

“Saboda haka, rundunar na sane da shirye-shiryen da wasu ɓata-gari ke yi na kawo cikas ga shirin a yankunan ƙasar. Manufar shi ne daƙile ƙoƙarin hukumomin tsaro na tabbatar da an yi bukukuwan cikin zaman lafiya da kuma haifar da fargaba da tsoro a tsakanin al’umma.

“Bisa ga haka, ana shawartan ’yan aasa, kafofin watsa labarai da ƙungiyoyin jama’a da su bi ƙa’idojin tsaro yayin bukukuwan. Ana kuma umurtansu da su guje wa labaran ƙarya, karkatattun rahoto da labarai wanda ka iya rura wutar rabuwar kai, tayar da hankali da kuma varkewar rikici kafin da bayan taron. Hakan ya kasance ne saboda irin wannan ayyuka babu abun da zai amfani jama’a face lalata haɗin kan ƙasar.”

A halin da ake ciki, rundunar ta yi kira ga jama’a da su ci gaba da kwantar da hankalinsu sannan su bi doka inda ta ce za ta ci gaba da haɗa kai da sauran hukumomin tsaro don tabbatar da an yi bikin rantsarwar cikin nasara.

Dalilin da ya sa Buhari ke ta ɗaukar matakai – Fadar Shugaban Ƙasa:

Fadar Shugaban Ƙasa, da yammacin Laraba, ta bayyana cewa, shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ba da ƙudirin ƙarshe kwanaki kaɗan domin miƙa wa gwamnatin Bola Tinubu saboda gwamnati na buƙatar kuɗaɗen da za ta biya basuka.

Mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Femi Adesina ne ya bayyana haka a gidan talabijin na Channels na shirin ‘TV’s Politics Today’ wanda, yayin da yake bayyana ayyukan Buhari na tsawon shekaru takwas a kan karagar mulki.

“Gwamnati tana da wa’adi daga lokaci zuwa wani lokaci, wannan wa’adin ya kasance daga 2019 zuwa 2023, don haka gwamnati na aiki,” in ji shi.

A ranar Larabar da ta gabata ne shugaban ƙasar ya rubutawa Majalisar Dattawan wasiƙar neman amincewar buaatar biyan bashin da ake bin ƙasar a kan kuɗi dala miliyan 566,754,584, fam 98,526 da kuma naira biliyan 226.

A takardar da ya aike wa Shugaban Majalisar, Sanata Ahmad Lawan, Buhari ya bayyana cewa kuɗaɗen sun haɗa da Dala miliyan 566.8 da Fam miliyan 98.6 da kuma Naira biliyan 226.3.

Ya ce, za a biya bashin ne ta hanyar raba takardun lamuni, kamar yadda, “Ranar 29 ga watan Maris, 2023, Majalisar Zartawar ta Ƙasa ta amince a biya manyan basukan aikin shari’a da ake bin Hukumomi da Ma’aikatun Gwamnatin Tarayya ta hanyar takardun lamuni, daga bisani za a biya a hankali daga kasafin kuɗi.

“Don haka ake neman sahalewar majalisa, kuma Ministan Shari’a kuma Antoni Janar na Ƙasa tare da Ministar Kuɗi za su bayar da duk bayanan da ake buƙata.”

A ’yan makonnin nan dai shugaban da ministocinsa na ɗaukar wasu muhimman matakai da suke bayyana cewa bai saba doka ba, duk da cewa wa’adin gwamnatin ya kawo ƙarshe.

Sa’o’i kafin miƙa mulki Buhari ya umarci ministocinsa su cigaba da aikinsu:

A ranar Laraba ne Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, ya bulaci Ministocinsa su ci gaba da riƙe muƙamansu har zuwa ranar da za a rantsar da sabon Shugaban Ƙasa.

Mutane da dama sun yi tsammanin cewa shugaban zai rusa majalisar ministocinsa ne a taron Majalisar Zartarwa ta Ƙasa da ya jagoranta a Abuja.

A ranar 29 ga watan Mayun 2023 ce Buhari zai miqa ragamar mulki ga zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.

Akwai dai rahotannin da ke cewa Buhari ya sallami Ministocin a yayin taron Majalisar Zartarwa na bankwana da aka gudanar a Fadarsa da ke Abuja ranar Laraba.

To, sai dai da yake zantawa da ’yan jaridar Fadar Shugaban Ƙasa bayan kammala taron, Ministan Yaɗa Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed, ya ce, an umarci dukkan Ministocin su koma su ci gaba da ayyukansu a ma’aikatunsu.

Lai Mohammed ya ce, “Labarin da ake yaɗawa cewa an rushe Majalisar Ministoci ba gaskiya ba ne. Shugaban Ƙasa ya umarce mu mu ci gaba da aiki. Saboda haka ba a rushe mu ba, har yanzu muna nan.

“Labarin cewa an rushe mu ƙarya ne. Na tabbatar za mu ci gaba da aiki har nan da ranar 29 ga watan Mayu. Saboda haka ku yi watsi da wancan labarin, ba shi da tushe ballantana makama,” inji Ministan.

Ana shirin kawo cikas ga bukukuwan miƙa mulki a jihohi, inji DSS:

Hukumar Tsaro ta Farin Kaya a Nijeriya (DSS) ta bayyana cewa, akwai wasu da ke shirin tayar da zaune tsaye a lokacin bukukuwan miƙa mulki da za a yi a wasu jihohin ƙasar.

A wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis, 25 ga watan Mayu, 2023, hukumar ta ce, mutanen su na son daƙile aikin jami’an tsaro ne tare kuma da tayar da hankalin jama’a su jefa tsoro ga ‘yan ƙasar a lokacin.

A sanarwar wadda kakakinta, Peter Afunanya ya fitar, hukumar ta buƙaci jama’a da ’yan jarida da ƙungiyoyin farar hula da duk wasu masu ruwa da tsaki a harkar da su bi ƙa’idojin da aka tsara a lokacin bikin a ko ina a faɗin ƙasar.

Haka kuma, sanarwar ta shawarci jama’a da su yi watsi da labaran ƙarya ko na ƙanzon-kurege da na zuzuta al’amura da kuma duk wani abu na neman razanarwa.

Hukumar ta kuma shawarci duk wani mutum da ba shi da takardar izini ko ta tantancewa da ya kauce wa shiga wasu wuraren a lokacin da ake bikin.

DSS ta bai wa jama’a tabbacin ci gaba da aiki tare da sauran hukumomin tsaro domin ganin bukukuwan sun wakana lami lafiya cikin nasara a ko’ina a faɗin ƙasar.