KAROTA za ta baza jami’ai 1,000 domin yin aiki a bikin rantsuwar Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Jihar Kano, KAROTA, ta ce, ta ware jami’anta guda 1,000 da za su kula da zirga-zirgar ababen hawa a ranar bikin rantsuwar sabon gwamna da zai gudana ranar Litinin.

Shugaban hukumar kuma Daraktanta na Mulki, Alhaji Abdullahi Yahuza, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Nabilusi Abubakar Kofar Nai’sa, ya fitar a ranar Asabar.

Nabulusi ya ce, an ware jami’an KAROTA ne domin kula da kaiwa da komowar ababen hawa.

Ya kuma ce, “Za a rufe wasu daga cikin titunan da suka shafi kewayen filin da za a gudanar da taron”.

Alhaji Abdullahi Yahuza, ya ja hankalin jami’an da su gudanar da ayyukansu cikin nutsuwa tare da nuna ƙwarewar aiki,

Kazalika, ya roƙi al’umma da su bai wa jami’an hukumar haɗin kai tare da bin dokokin da aka shimfiɗa kafin, yayin da kuma bayan kammala taron bikin rantsuwar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *