An sauya wa Kakakin ‘yan sandan Katsina wurin aiki

Daga UMAR GARBA a Katsina

Babban Sufeton ‘Yan Sandan Nijeriya, Usman Baba, ya bada umarnin sauya wa Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Katsina, CSP Gambo Isah, wurin aiki.

An sauya shi daga hedikwatar rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina zuwa shiyya ta 14, inda zai ci gaba da riƙe muƙamin na kakakin ‘yan sanda a jihohin Katsina da Kaduna da ke shiyyar ta 14.

Sauyin wurin aikin na zuwa ne bayan da wata ‘yar jarida Ruƙayya Aliyu Jibiya ma’aikaciya a tashar Tambarin Hausa, ta fallasa cewar Kakakin rundunar ya ci zarafinta bayan da ya jagoranci wata tawagar ‘yan sanda, inda suka kama ta da ƙarfi suka jefa ta mota tare da fasa mata wayoyi kafin daga bisani suka miƙa ta fadar mai martaba Sarkin Katsina, daga nan kuma Sarkin ya bada umarnin a kai ta gidan gyara hali har sai ya neme ta.

Sai dai rahotanni na alaƙanta sauyin da CSP Isa ya samu, a matsayin hukunci ne ga Kakakin rundunar bayan da taƙaddama ta ɓarke tsakaninsa da Ruƙayya Jibiya.

Jaridar Daily Nigeria ta rawaito cewa bayanin sauya masa wurin aikin na ƙunshe ne cikin wata takarda mai ɗauke da kwanan wata 25 ga watan Mayu, 2023 mai lamba CH.5360/FS/FHQ/ABJ/V.TIl/210, inda sauyin wurin aikin ya shafi mutane 15, sai dai sunan CSP Isa ne a farkon takardar.

Jaridar ta ƙara da cewa an sauya masa wurin aiki ne saboda cin zarafin ‘yar jarida.

Idan za’a iya tunawa, Manhaja ta bada labarin yadda ‘yar jaridar ta yi ɓatan dabo bayan da rundunar ‘yan sanda a jihar ta bayar da belinta.

Sai dai daga baya, cikin wani faifan bidiyo ‘yar jaridar ta bayyana, inda ta ce rayuwarta na cikin hatsari shi ya sa ta ɓoye kanta, saboda rundunar ‘yan sanda a jihar na yi wa rayuwarta barazana.

Lamarin da ya ɗauki hankalin al’umma da dama musamman a kafafen sada zumunta na zamani.

rundunar ‘yan sandan ta tsare ‘yar jaridar bisa zarginta da amfani da shafinta na Tiktok, wajen warware tufkar da suke yi don magance matsalar tsaro a jihar.