RTEAN ta yunƙura domin rage aukuwar haɗurra

Daga BASHIR ISAH

Ƙungiyar Masu Motocin Sufuri ta Nijeriya (RTEAN), ta gabatar da shiri na musamman don kulawa da kafin da baya aukuwar haɗurra a hanyoyin ƙasar nan domin rage yawan asarar rai sakamakon hatsarin abubuwan hawa.

Sa’ilin da yake ƙaddamar da shirin a ranar Laraba a Abuja, Shugaban RTEAN na ƙasa, Dr Musa Maitakobi, ya bayyana cewa shirin na da manufar samar da sukuni game da tafiye-tafiye a hanyoyi ba tare da fuskantar wata matsala ba.

Shugaban wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Ambasada Muhammad Abubakar, ya ce an tsara shirin da kuma samar da shi ne daidai da Dokar Majalisar Ɗinkin Duniya ta Kiyaye Haɗurra ta 2021-2030.

Ya ce, “Ida za a iya tunawa da farko mun samar da shirin Inshorar Hatsarin Matafiya (TAIS) inda dukkan waɗanda hatsarin mota ya ritsa da su a motocin RTEAN za su samu kulawa da kuma tallafi.

“Amma bayan nazari mai zurfi a kan shirye-shiryen, sai muka ga dacewar sake samar da wani shiri domin tallafa wa shirye-shiryenmu na farko don tabbatar da nasarorin da aka sa a gaba.

“Don haka aka yanke shawarar ƙirƙiro da shirin Kulawa da Kafin da Bayan Aukuwar Haɗurra a Hanyoyi Don Rage Yawan Asarar Rayuka,” in ji shi.

Maitakobi ya ce a Satumban 2020, MƊD ta amince da samar da shirin na musamman ƙarƙashin A/RES/74/299 mai taken “Inganta Kiyaye Haɗurra a faɗin duniya“ na 2021- 2030.