Editor

9513 Posts
Hada-hadar kasuwar ’yan wasan ƙwallon ƙafa

Hada-hadar kasuwar ’yan wasan ƙwallon ƙafa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ɗan wasan gaba a Portugal Cristiano Ronaldo na son barin ƙungiyar Al Nassr ta Saudiyya, babu mamakin ya dawo Turai. Juventus ta jadadda cewa ɗan wasanta, Dusan Vlahovic mai shekara 23 daga Serbia ba na sayarwa ba ne, ta fitar da wannan sanarwa ne ganin rububin da aka soma a kansa. Ƙungiyar Fenerbahce ta Turkiyya na kan gaba a cinikin saye ɗan wasan Belgium da Ac Milan Divock Origi, wanda ke cika shekara guda da barinsa Liverpool. Tottenham na duba yiwuwar tuntuɓar kocin Feyenoord, Arne Slot. Slot na iya zama sabon kocin Tottenham idan aka daidaita…
Read More
Soja da ’yan sandan bogi sun shiga hannun ’yan sandan asali a Kano

Soja da ’yan sandan bogi sun shiga hannun ’yan sandan asali a Kano

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja ’Yan sanda sun cafke wasu mutum uku da ke yin sojan-gona a matsayin soja ɗan sanda da kuma jami’in kwastam da suka addabi mazauna birnin Kano da kewaye. Kakakin rundunar ’yan sandan Kano, Abdullah Haruna Kiyawa ne, ya tabbatar wa manema labarai cewa an kama jami’an tsaron na bogi ne a lokuta daban-daban suna muzgunawa jama’a tare da damfarar jama’a. A cewarsa “A ranar 22 ga watan Mayu, 2023 da misalin ƙarfe 11:00 ne wata tawagar sa ido da ke sintiri ta kama wani mazaunin Filin Mushe a Kano sanye da kakin sojoji yana…
Read More
Ƙungiyar Raya Garin Tafawa Ɓalewa ta gindaya wa Sayawa sharuɗɗan samun masarauta

Ƙungiyar Raya Garin Tafawa Ɓalewa ta gindaya wa Sayawa sharuɗɗan samun masarauta

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi An gindaya wa al'ummar Sayawa dake cikin ƙananan hukumomin Tafawa Ɓalewa da Bogoro na Jihar Bauchi sharuɗɗa na cimma buƙatar su ta samun masarauta da 'yancin cin gashin kai kamar yadda hukumar Shari'a ta Alƙali Babalakin ta shawarta dangane rikicin ƙabilanci da ya faru a garin Tafawa Ɓalewa a ranar Litinin 22 ga watan Afrilu na shekara ta 1991. Ƙungiyar raya garin Tafawa Ɓalewa wacce ta zayyana waɗannan sharuɗɗa, ta kuma fayyace su ɗaya bayan ɗaya da suka haɗa da bin ƙa'idoji kamar yadda shuɗaɗɗiyar gwamnatin Isa Yuguda ta yi a shekara ta 2011. Ƙungiyar…
Read More
Gwamnatin Kano ta wanke Ado Doguwa daga zargin kisan kai

Gwamnatin Kano ta wanke Ado Doguwa daga zargin kisan kai

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ma'aikatar Shari'a ta Jihar Kano ta ce binciken da ta gudanar kan tuhumar da ake yi wa ɗan majalisar wakilan tarayya, Alhassan Ado Doguwa kan laifin kisan, ya nuna cewa ba a same shi da laifin da ake zargi ba. Lokacin da ya yi wa manema labarai bayani, kwamishinan shari'a na jihar Kano, Lawan Musa Abdullahi ya ce an samu saɓani da dama cikin bayanan da aka samu daga wurin shaidu. Ya ƙara da cewa a yayin da suke gudanar da bincike sun gano cewa ma'aikatan asibiti ba su yi cikakken bincike kan mutanen…
Read More
Majalisa ta amince da ƙudurin dokar da za ta bai wa gwamnati damar bai wa ɗalibai bashi

Majalisa ta amince da ƙudurin dokar da za ta bai wa gwamnati damar bai wa ɗalibai bashi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Majalisar Dokokin Nijeriya ta amince da ƙudurin dokar da za ta bai wa gwamnati damar bai wa ɗalibai bashi don su yi karatun gaba da sakandare. Bashin yin karatun wani tsari ne da gwamnatin Nijeriya ke son ɓullowa da shi na bai wa ɗalibai bashi domin su cigaba da karatunsu na gaba da sakandare, kazalika bashin ana bayar da shi ne ga ɗalibin da yake karatu a Nijeriya kama tun daga matakin difiloma har zuwa digiri. A Shekarar 2019 Femi Gbajabiamila ya gabatar da ƙudirin dokar da yake so a riƙa bai wa ɗalibai…
Read More
Ranar Lahadi Buhari zai yi wa ‘yan Nijeriya jawabin bankwana

Ranar Lahadi Buhari zai yi wa ‘yan Nijeriya jawabin bankwana

A ranar Lahadi da safe ake sa ran Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, zai yi wa 'yan ƙasa jawabin bankwana sakamakon ƙarewar wa'adin mulkinsa. Mai magana da yawun Buhari, Femi Adesina ne ya bayyana haka cikin sanarwar da ya fitar ranar Asabar. Adesina ya ce za a yaɗa jawabin Shugaban kai tsaye a tashoshin talabijin da rediyo da sauran kafafe da misalin ƙarfe 7:00 na safe. Ya zuwa ranar Litinin, 29 ga Mayun 2023 ake sa ran ƙarewar wa'adin mulkin Buhari inda kuma za a rantsar da magajinsa domin ɗorawa daga inda ya tsaya.
Read More
BURIN ZUCIYA: Muƙamin siyasa da nake nema wajen zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Katsina, Dr. Dikko Umar Raɗɗa

BURIN ZUCIYA: Muƙamin siyasa da nake nema wajen zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Katsina, Dr. Dikko Umar Raɗɗa

Daga Engr. KABIRU EL-HUSSAIN RUMAH, MNSE, MNIMechE, MNIM, MISPON! Da alama, bisa la’a’kari da yanda aka yi wa zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Katsina, Dr. Dikko Umar Raɗɗa, PhD, yawa wajen hada-hadar neman muƙaman siyasa daga gwamnatinshi, idan na ce zan nemi muƙamin Kwamishina, to lallai, da alama gonar wasu da yawa, wanda suke ganin sun fi ni kusanci da Dr. Dikko Umar Raɗɗa zan shiga, haka nan ma, idan na ce zan nemi muƙamin siyasa na Mai Bada Shawara na Musamman (wato Political Adviser) da kuma shugabancin dukkan ɗaya daga cikin ɓangarori da hukumomi 84 na Jihar Katsina, da waɗanda ke…
Read More
Ambaliyar: SEMA da UNICEF sun gudanar da taron masu ruwa da tsaki a Kano

Ambaliyar: SEMA da UNICEF sun gudanar da taron masu ruwa da tsaki a Kano

Daga RABI'U SANUSI a Kano Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Jihar Kano SEMA, tare da haɗin gwiwar UNICEF sun gudanar da taron masu ruwa da tsaki game da tunkarar daminar bana tare da hora da al'umma hanyar da ya kamata su bi don rage afkuwar iftila'in ruwan sama. Da yake bayani ga manema labarai yayin taron na yini ɗaya, Babban Sakataren hukumar ta SEMA na Jihar Kano Alhaji Saleh Jili ya ce kamar yadda hukumar binciken hasashen yanayi da kula da yanayi ta gudanar da bincike kan yuwuwar samun ruwan sama mai yawa a wannan damuna ta bada ya sa…
Read More
Alba na shirin barin Barcelona kafin ƙarewar kwantaraginsa

Alba na shirin barin Barcelona kafin ƙarewar kwantaraginsa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Barcelona da Jordi Alba sun cimma yarjejeniyar raba gari tun kan kwantiraginsa ya ƙare a ƙungiyar. Alba, mai shekara 34 ya koma Camp Nou a 2012 daga Valencia, ya kuma lashe La Liga shida da Copa del Rey biyar da gasar Zakarun Turai a 2015. Ya buga wa Barcelona wasanni 458 har da 29 a kakar nan da ƙungiyar Camp Nou ta ɗauki La Liga na bana na 27 jimilla. Alba ya zama na biyu da zai bar Barcelona a aarshen kakar nan, bayan kyaftin, Sergio Busquets. Barcelona ta kai ga cimma wannan matsaya, bayan da…
Read More
Gwamnati ta ayyana Litinin hutun gama-gari

Gwamnati ta ayyana Litinin hutun gama-gari

Gwamnantin Tarayya ta ayyana Litinin, 29 ga Mayu a matsayin ranar hutun gama-gari ga ɗaukacin ma'aikata a faɗin ƙasa. Ministan Harkokin Cikin Gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, shi ne ya bayyana haka a madadin gwamnatin ranar Juma'a a Abuja. Babban Sakataren Ma'aikatar, Dokta Shuiab Belgore, ya ce an ɗauki wannan mataki ne domin bai wa 'yan Nijeriya damar shagalin bikin rantsar da zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasar Nijeriya na 16. Sakataren ya ce, “Ministan na taya 'yan Nijeriya murnar wannan al'amari mai muhimmnci, tare da yaba musu game da tsayin dakan da suka yi wajen zaɓen da ya bai wa Bola Tinubu da mataimakinsa…
Read More