Editor

9513 Posts
Gwamna Buni ya rusa majalisar zartaswarsa

Gwamna Buni ya rusa majalisar zartaswarsa

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Damaturu Gwamnan Jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni, ya rushe majalisar zartaswar jihar tare da dukkanin masu riƙe da muƙaman siyasa a jihar a ranar Juma'a. A cikin wata sanarwar manema labaru mai ɗauke da sa-hannun mai magana da yawun Gwamnan, Alhaji Mamman Mohammed, inda ya ƙara da cewa an umurci Sakataren Gwamnatin Jihar (SSG) ya miƙa ragamar gudanar da ofishin sa ga Sakataren Din-din-din na fannin mulki. Haka shi ma Shugaban Ma'aikatan Fadar Gwamnatin jihar, an umarce shi da ya miƙa tafiyar da harkokin ofishin ga Babban jami'in gidan gwamnatin. Sanarwar ta ƙara da cewa,…
Read More
Abba Kabir ya gabatar wa Kotun Ma’aikata bayanin kadarorinsa da bashin ake bin sa

Abba Kabir ya gabatar wa Kotun Ma’aikata bayanin kadarorinsa da bashin ake bin sa

Daga RABI'U SANUSI a Kano Zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kano mai jiran gado, Engr. Abba Kabir Yusuf, ya bayyana kadarorinsa da kuma kuɗaɗen da ake bin sa ga Kotun Ma'aikata (CCB) ranar Juma’a a Kano Abba gida-gida wanda ya samu tarba daga Daraktar CCB ta jihar, Hajia Hadiza Larai Ibrahim, ta ce yadda ya bayyana kadarorinsa na nuna gaskiya da riƙon amana da zai zama ginshiƙin gwamnati mai zuwa a jihar Kano. “A yau, na cika haƙƙin da tsarin mulki ya ɗora min na bayyana kadarorina kafin in shiga ofis a ranar Litinin 29 ga Mayu,” in ji Kabir Yusuf. Zaɓaɓɓen…
Read More
‘Yan bindiga sun kashe manoma sama da 20 a Zamfara

‘Yan bindiga sun kashe manoma sama da 20 a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau Wasu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun kashe manoma sama da 20 a yankin Gidan Goga da ke karamar hukumar Maradun a jihar Zamfara. Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar wa wakilinmu faruwar hakan ta wayar tarho. A cewarsa, ‘yan bindigar sun kai farmaki kan manoman ne bayan da suka shagaltu da aikin noma a ranar Laraba inda suka yi yunƙurin yin garkuwa da wasu daga cikinsu. “’Yan bindigar sun far musu ne a ƙoƙarinsu na yin garkuwa da wasu manoma amma sun fahimci cewa manoman sun fara…
Read More
Ku zamo jakadun ƙwarai a ƙasa Mai tsarki, kiran Gwamnan Zamfara ga maniyyan jihar

Ku zamo jakadun ƙwarai a ƙasa Mai tsarki, kiran Gwamnan Zamfara ga maniyyan jihar

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Mohammed Matawalle, ya yi kira ga maniyyatan aikin hajjin bana na jihar da su zama jakadu nagari yayin da suke ƙasa mai tsarki. Ya yi wannan kiran ne a ranar Juma'a yayin da yake bankwana da maniyyatan jihar su 428 da za su tashi a jirgin farko zuwa Saudiyya don sauke farali. Gwamna Matawalle wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Sanata Hassan Nasiha, ya ce gwamnatinsa ta yi duk wani shiri na tabbatar da jin daɗi da walwalar alhazan jihar yayin da suke ƙasa mai tsarki. "Muna kira ga maniyyatanmu da su…
Read More
Hajjin Bana: Maniyyatan Binuwai sun yi hatsari a hanyarsu ta zuwa Abuja

Hajjin Bana: Maniyyatan Binuwai sun yi hatsari a hanyarsu ta zuwa Abuja

Wata mota mai ɗauke da maniyyatan Hajjin 2023 daga Jihar Binuwai ta yi hatsari. Hatsarin ya auku ne a ranar Juma'a yayin da maniyyatan ke kan hanyarsu ta zuwa birnin tarayya, Abuja inda a nan ake sa ran za su shiga jirgi zuwa ƙasa mai tsarki. Sakataren Hukumar Alhazai na Jihar Binuwai, Mustafa Ibrahim, shi ne ya tabbatar da faruwar hakan ga Hajj Reporters. Tare da cewa zai ba da ƙari bayani kan batun nan gaba.
Read More
Zargin amfani da takardun ƙarya: Kotu ta yi barazanar kulle Fani-Kayode

Zargin amfani da takardun ƙarya: Kotu ta yi barazanar kulle Fani-Kayode

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Kotun hukunta manyan laifuka da ke zamanta a Ikeja, Legas, ta ce, za ta bayyana tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, a matsayin wanda ake nema ruwa-a-jallo idan har ya kasa bayyana a rana mai zuwa da ta ɗage sauraron shari’arsa. Mai shari’a Olubumni Abike-Fadipe ya koka kan rashin bayyanar da wanda ake tuhuma a kai a kai, inda ya bayyana cewa a karon ƙarshe da ya kai kotu shi ne ranar 4 ga watan Nuwamba, 2022. Fani-Kayode dai yana fuskantar shari’a kan tuhume-tuhume 12 da suka haɗa da amfani da takardun ƙarya, yin amfani…
Read More
ASUU ta tsunduma yajin aiki a Binuwai

ASUU ta tsunduma yajin aiki a Binuwai

Ƙungiyar Malaman Jami'o'i ta Ƙasa (ASUU) reshen Jami'ar Jihar Binuwai ta sanar da fara yajin aikin sai baba-ta-gani. Shugaban ASUU na Jami'ar Jihar (BSU), Dokta Kwaehfan Tarmombo, shi ne ya sanar da hakan ranar Juama'a. Tarmombo ya alaƙanta yajin aikin nasu da matsalolin da mambobin ƙungiyar ke fuskanta da shugabancin jami'ar.
Read More
Newcastle za ta shiga gasar Zakarun Turai karon farko cikin shekaru 20

Newcastle za ta shiga gasar Zakarun Turai karon farko cikin shekaru 20

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Newcastle ta samu damar kaiwa matakin iya taka leda a gasar kofin Zakarun Turai karon farko cikin shekaru 20, kasa da kakar wasa biyu bayan ƙungiyar ta kwaci kanta da kyar daga rukunin ’yan daga aji na teburin firimiya, wanda ya kai ga sayar da ita. Newcastle United dai na shirin kammala kakar ta bana a matsayin ta 3 a teburin firimiyar Ingila bayan da ta yi canjaras da Leicester City a jiya Litinin wanda ke nuna yanzu ta na da maki 70 ne bayan doka wasanni 37 tazarar maki 1 tsakaninta…
Read More
Gwamnati ta buƙaci bankuna su fara bayar da katin ɗan ƙasa haɗe da ATM

Gwamnati ta buƙaci bankuna su fara bayar da katin ɗan ƙasa haɗe da ATM

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Gwamnatin Tarayya ta ba wa bankunan kasuwanci izinin fara ba wa abokan hulɗarsu katin cirar kuɗi na ATM da ke haɗe da katin shaidar ɗan ƙasa a wurin guda. Ministan Sadarwa, Isa Ali Pantami, ya sanar cewa Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta amince bankuna su fara bayar da katin na bai-daya ba tare da sun caji kwastomomi ko sisi a kan kuɗin katin ATM da aka saba ba. Ya ƙara da cewa“An ba wa bankuna izinin buga katunan Mastercard ko Visa da za su yi amfani a matsayin katin shaidar ɗan ƙasa ba tare da sun…
Read More