26
May
Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shugaban Ƙasa Muhammmadu Buhari ya bai Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, lambar girma mafi daraja ta ƙasar wato 'Grand Commander of the Order of the Federal Republic' (GCFR). Hakazalika, Buharin ya bai wa mataimakin shugaban ƙasar mai jiran-gado, Kashim Shettima lambar girmamar ta biyu a daraja wato GCON 'Grand Commander of the Order of Niger'. Shugaban ya ba su lambobin da kuma takardun mulki ne a Abuja, a shirye-shiryen da ake yi na rantsar da sabuwar gwamnati, ranar Litinin 29 ga watan nan na Mayu, bayan kammala wa’adinsa na biyu na shekara huɗu-huɗu. Za a…
