Zan maida hankali kan rashin tsaro, noma, samar da ayyuka, cewar sabon Gwamnan Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Sabon Gwamnan Jihar Zamfara, Dr. Dauda Lawal Dare, ya yi alƙawarin bayar da muhimmanci kan fannonin tsaro, noma, samar da ayyukan yi da samar da ababen more rayuwa domin cigaban jihar.

Gwamna Dauda ya bayyana haka ne a wajen bikin rantsar da gwamnatinsa da aka gudanar a cibiyar kasuwanci ta Zamfara ranar Litinin .

A cewarsa, an samu rahoton rashin tsaro a jihar Zamfara sakamakon ayyukan ‘yan ta’adda, don haka akwai buƙatar gwamnatinsa ta haɗa kai da Gwamnatin Tarayya domin ceto jihar don a samun dawamammen zaman lafiya.

“Za mu tsara duk dabarun da za a bi don shawo kan matsalar rashin tsaro da ta addabi jihar sama da shekaru 10 domin dawo da zaman lafiya da cigaban tattalin arzikin jihar,” in ji shi.

Ya ci gaba cewa, gwamnatinsa za ta ba da muhimmanci sosai a fannin noma da samar da ayyukan yi don tabbatar da ci gaban tattalin arzikin jihar.

A cewarsa, zai haɗa hannu da hukumomin bada tallafi da masu zuba jari na ƙasashen waje domin bunƙasa jihar.

Ya ce, “Gwamnatina za ta haɗa hannu da hukumomin bayar da tallafi da masu zuba jari na ƙasashen waje domin bunƙasa jihar ta fuskar samar da ababen more rayuwa da ci gaban bil’adama duba da yadda jihar Zamfara ta zamo koma baya wajen rashin isassun hanyoyin samun kuɗin shiga domin bunƙasa jihar.”

Ya kuma yi kira ga al’ummar jihar da su bai wa gwamnatinsa haɗin kan da ya dace domin cimma manufofin gwamnatinsa.

“Ina so in yi kira ga ɗaukacin al’ummar jihar Zamfara cewa, Zamfara ba ta da kwanciyar hankali kuma za mu yi duk mai yiwuwa don ceto jihar daga halin da take ciki,”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *