Editor

9513 Posts
Ɗan ta’adda ya kashe kansa da bom a Kaduna

Ɗan ta’adda ya kashe kansa da bom a Kaduna

Wani da ake zargin ɗan Boko Haram ne ya yi ƙunar baƙin wake inda ya tada bom ya kashe kansa a Kaduna. Bayanan da Manhaja ta kalato sun ce, ɗan ta'addan ya kashe kansa ne gudun kamun jami'an tsaro. Lamarin ya faru ne da safiyar ranar Litinin a ƙauyen Keke, cikin Ƙaramar Hukumar Chikun, Jihar Kaduna kamar yadda jaridar News Point Nigeria ta rawaito. Kakakin 'yan sandar jihar, Muhammed Jalige, ya tabbatar da faruwar hakan. Majiyar News Point Nigeria ta ce, da ma ɗan ta'addan na daga jerin ɓata-garin da jami'an tsaron yankin ke nema ruwa a jallo. Majiyar ta…
Read More
Dandalin shawara: Mijina ya ba ni zaɓi; ko gidan da na mallaka ko igiyar aurena

Dandalin shawara: Mijina ya ba ni zaɓi; ko gidan da na mallaka ko igiyar aurena

Daga AISHA ASAS  TAMBAYA: Assalamu alaikum warahamullah. Sunana…….don Allah Ina neman shawara. Gidan yawa muke, na yi aure da mijina yana da mata biyu, na zama ta uku, kuma bayan ni sai ɗaya ta zaka, mun koma huɗu kenan. Ya'yan gidan gari guda, don su 44 na. Babu zaman lafiya a gidan. Kullum ta sahiya daban da ta marece. Shi ko maigidan in ka kai qara ma ba wani katavus ya ka yi ba. Sai dai idan ta yi masa daɗi ya tara ya yi ta wa'azin da iya bakinshi ne. Ɗiyanshi har sun san ko sun ci mutuncin matar…
Read More
Farashin kayayyaki ya ƙaru da kashi 22.22 a Nijeriya – NBS

Farashin kayayyaki ya ƙaru da kashi 22.22 a Nijeriya – NBS

A halin da ake ciki, farashin kayayyakin masarufi a Nijeriya ya ƙaru zuwa kashi 22.22 a watan Afrilu saɓanin 22.04 a watan Maris. Bayanin haka na ƙunshe ne cikin sanarwar da Hukuma Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS), ta fitar a ranar Litinin. A cewar Hukumar, ƙididdigar hauhawar farashi ta watan Afrilun 2023, ta nuna an samu ƙarin kashi 0.18 na tsadar kayayyaki idan an kwatanta da watan Maris da ya gabata. NBS ta ce bisa la'akari da sheka-shekara, an samu hauhawar farashi mai yawa a Afrilun bana idan aka kwatanta da yadda lamarin yake a Afrilun 2022, wato kashi 16.82. Hukumar…
Read More
Mutuwa rigar kowa!

Mutuwa rigar kowa!

Assalam alaikum. Da farko ina roƙon Allah Ya jiƙan Jamilu Yakub (Markaz). Mutuwa ƙarar kwana ce, domin kuwa, kowa da tanadin kwanakin da aka yi masa. Ke nan muna iya cewa, mutuwa riga ce da kowa sai ya sanya ta ko mai matsayi ko iko. Wannan ne ya sanya mutuwa ta kasance wa’adi da kowa ke jiran nasa. Saboda haka muna iya cewa mutuwa ƙa’ida ce da kowa sai ya cika, matuƙar an hura masa rai. Bisa irin wannan tunani ne waɗansu ke ganin mutuwa hutu ce ga kowane mamaci, musamman idan aka yi la’akari da kujuba-kujubar da mutane ke…
Read More
CAN ta buƙaci ’yan siyasar da suka yi nasara su rungumi kowa

CAN ta buƙaci ’yan siyasar da suka yi nasara su rungumi kowa

Daga JOHN D. WADA a Lafiya A yanzu da aka kammala duka zaɓukan gama-gari na 2023, an yi kira na musamman ga ’yan siyasa a dukka matakai a jihar Nasarawa da ƙasa baki ɗaya su tabbatar sun rungumi aƙidar zaman lafiya da haɗa kawunan al’umma maimakon ta da zaune tsaye da sauran su. Shugaban Ƙungiyar Mabiya Addinin Kirista ta Ƙasa (CAN), reshin Jihar Nasarawa Dokta Sunday Emmah ne ya yi wannan kira a lokacin da yake tattauna da wakilinmu a gidan sa dake Lafiya fadar gwamnatin jihar a ƙarshen makon da ya gabata. Ya ce, ba shakka kiran yazama wajibi…
Read More
Tsadar rayuwa: Kamfanin MTN zai ƙara kuɗin kira da farashin data

Tsadar rayuwa: Kamfanin MTN zai ƙara kuɗin kira da farashin data

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Kamfanin Telecomms na MTN, ya ce, yana shirin ƙara farashin ayyuka a layinsa saboda hauhawar farashin kayayyaki a wuraren aiki. An bayyana hakan ne a cikin rahoton kafanin na farko da aka shigar a kasuwar hada-hadar hannayen jari ta Johannesburg a ranar Alhamis. A hasashen da ta yi na sauran shekarar 2023, kamfanin ya MTN ya ce, “Muna sa ran cewa yanayin kasuwanci a faɗin kasuwanni zai ci gaba da zama ƙalubale har zuwa ƙarshen shekarar 2023 kuma za mu ci gaba da aiwatar da matakan da za mu ɗauka don shawo kan ƙalubalen da ke…
Read More
Hajjin Bana: NAHCON da kamfanonin jirgin sama sun amince da ƙarin kuɗin Hajji $250

Hajjin Bana: NAHCON da kamfanonin jirgin sama sun amince da ƙarin kuɗin Hajji $250

Shugaban Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON), Zikrullah Hassan, ya ce kamfanonin jirgin sama na cikin gida da aka amince su yi jigilar maniyyatan Hajjin bana, sun buƙaci a ƙara kuɗin Hajji da $250. A cewarsa, kamfanonin da suka buƙaci ƙarin sun haɗa da Air Peace, Azman, Max Air da kuma Aero Contractors. Ya ƙara da cewa, sun buƙaci hakan ne sakamakon rikicin da ke aukuwa a ƙasar Sudan, wanda hakan zai tilasta musu yin zagaye da tafiya mai nisan zango kafin isa Saudiyya a lokacin jigilar maniyyatan. Wannan ne ma ya sa kamfanonin suka ƙi sanya hannu a yarjejeniyar aiki…
Read More
ASUU ta caccaki Buhari kan sake cin bashi

ASUU ta caccaki Buhari kan sake cin bashi

*Buhari ya nemi majalisa ta ba shi damar ƙara ciwo bashi*Ya na son ciwo qarin bashin Naira biliyan 368.7 ne*Kwanaki 16 suka rage masa a gadon mulki Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ƙungiyar Malaman Jami’o’i a Nijeriya (ASUU) ta bayyana buƙatar Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari na neman Majalisar Dattawa ta sahale masa ya ciwo bashin Naira Biliyan 368.7 a matsayin wani abin da bai dace ba kwanakin kaɗan kafin barin shi mulki. Farfesa Emmanuel Osodeke, Shugaban Ƙungiyar ASUU na Ƙasa, ya bayyana haka ne a jiya Alhamis yayin da yake jawabi a wajen bikin bayar da lambar yabo ta…
Read More
Nijeriya ta ƙetare iyaka a cin bashi, cewar Ofishin Kasafin Kuɗi

Nijeriya ta ƙetare iyaka a cin bashi, cewar Ofishin Kasafin Kuɗi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shugaban Kasafin Kuɗi na Tarayya, Ben Akabueze ya koka kan shirin karɓar rancen Nijeriya, inda ya ce, al’ummar ƙasar na iya shiga matsala. Akabueze ya yi wannan jawabi ne ranar Laraba a wajen taron ƙaddamar da sabbin zaɓaɓɓun ’yan majalisar wakilai na ƙasa karo na 10, a ɗakin taro na ƙasa da ƙasa (ICC) da ke Abuja. Damuwa da fargabar nasa na zuwa ne a daidai lokacin da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya miƙa sabon buaatar neman lamunin dala miliyan 800 ga Majalisar Dokokin ƙasar domin biyan buaatun matsugunan gidaje miliyan 10.2 akan naira 5,000 kowanne.…
Read More
Ba mu da masaniyar bai wa Emefiele izinin barin ƙasa – Fadar Shugaban Ƙasa

Ba mu da masaniyar bai wa Emefiele izinin barin ƙasa – Fadar Shugaban Ƙasa

Fadar Shugaban Ƙasa ta ce ba ta da masaniyar izinin fita waje ƙaro ilimi da aka ce Shugaba Muhammadu Buhari ya bai wa Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele. Babban Hadimin Shugaban Ƙasa Kan Harkokin Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a, Malam Garba Shehu ne ya faɗi hakan, yayin amsa tambayar jaridar Daily Trust ta ranar Lahadi. A baya, an rawaito Shehu na cewa, “Idan ma Shugaba Buhari ya bai wa Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele, izinin fita ƙaro ilimi, ba mu san da haka ba. “Haka nan, sakatariyar Shugaban Ƙasar ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban…
Read More