Editor

9513 Posts
Taƙaitaccen bayani game da matsalar kafa ƙungiyar Hausawa zalla

Taƙaitaccen bayani game da matsalar kafa ƙungiyar Hausawa zalla

Daga ABDURRAHMAN ABUBAKAR GUSAU Gaskiya yau na ƙara fahimtar cewa matsalar arewa ita ce rashin samun wadatatun masana masu rubutu don mutane su gane ba don a gano su ba. Dakta Aliyu U. Tilde lallai cikkaken masani ne da ya kai. Saboda ƙoƙarinsa wajen yin cikkaken bayani a kan wannan matsalar cikin ilimi da hikima. Sai dai kash! Ba a nan gizo ke saƙar ba, yanzu an riga an baro kyau tun ranar haihuwa. Gaskiya ne a dokar Nijeriya kowa na da ikon kafa ƙungiya don kare martabar ƙabila ko addini. Sai dai wannan Abu da wasu ke yi da…
Read More
Ɗan takarar da Gbajabiamila ke son ya gaje shi barazana ce ga dimokuraɗiyyar Nijeriya – Hon. Nalaraba

Ɗan takarar da Gbajabiamila ke son ya gaje shi barazana ce ga dimokuraɗiyyar Nijeriya – Hon. Nalaraba

Daga SANI AHMAD GIWA Honorabul Abubakar Hassan Nalaraba ya bayyana cewa shirin da ake zargin Kakakin Majalisa, Femi Gbajabiamila na yi na ɗora Hon. Abbas Tajuddeen a matsayin wanda zai gaje shi a Majalisar Wakilai ta 10 yana da haɗari ga dimokuraɗiyyar Nijeriya. Ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da ya kira a Abuja, kan zargin dambarwa da ake yi wa ɗan takara a tsarin dimukoraɗiyya, inda ya bayyana hakan a matsayin savani, rashin bin tsarin dimokuraɗiyya, mulkin kama-karya da kuma babban hatsari ga dimokuraɗiyya, savanin ɗan takararsa, Honorabul Mukhtar Aliyu Betara da ba shi da tsara.…
Read More
Dalilan da ke sa matan aure suke cin amanar aure

Dalilan da ke sa matan aure suke cin amanar aure

Daga AMINA YUSUF ALI Barkanmu da haɗuwa a wani sabon makon a wannan jarida tamu ta Blueprint Manhaja. A wannan mako za mu kawo muku maudu’in nan mai matuqar ban mamaki na satar hanyar wasu matan auren ko ma na ce zina. A ƙasar Hausa ba ƙaramin abin mamaki ba ne da kunya a ce yau an kama matar aure tana zina. Abu ne da yake wahalar samu, amma akwai. Na zavi na yi wannan rubutu saboda faɗakarwa ɓangaren maza da na mata a game da dalilan da suke jawo zinar matan aure, da kuma haɗarorin da ke tattare da…
Read More
Tinubu ya gana da Kwankwaso a Faransa

Tinubu ya gana da Kwankwaso a Faransa

Daga BASHIR ISAH Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa mai jiran gado, Bola Ahmed Tinubu, ya gana da ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam'iyyar NNPP, Rabiu Kwankwaso, a Paris, babban birnin ƙasar Faransa. Bayanai sun ce Tinubu da Kwankwaso sun yi ganawar sirri bayan haɗuwar tasu inda suka shafe sa'o'i huɗu suna tattaunawa. Majiyarmu ta ce tattaunawar tasu ta shafi yadda za a yi tafiya tare da Kwankwaso a gwamnati mai jiran gado kasancewar Tinubu na da ra'ayin kafa gwamnati ta haɗin kan ƙasa. Kazalika, majiyar ta ce daga cikin batutuwan da suka tattauna har da batun shugabancin majalisar tarayya. Wadanda suka halarci…
Read More
Bincike ya nuna yin waya fiye da minti 30 a mako na saka hawan jini

Bincike ya nuna yin waya fiye da minti 30 a mako na saka hawan jini

Masana kiwon lafiya sun gano cewa yin waya na sama da minti 30 a mako guda na haddasa ƙaruwar cutar hawan jini da kashi 12. Rahoton da Ƙungiyar Likitocin Zuciya na Nahiyar Turai ta fitar a ranar Juma’a ya buƙaci jama’a da su takaita yin waya domin kare lafiyar zukatansu. Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa rahoton likitocin da aka wallafa a mujallar Digital Health yana nuna yin waya na sama da minti 30 a mako na ƙara barazanar kamuwa da cutar hawan jina da kashi 12 cikin 100. Mujallar, wadda a mayar da hankali a kan yadda…
Read More
Ku zauna da shirin karɓar baƙuncin EFCC, shawarar Ɗankwambo ga gwamnoni masu barin gado

Ku zauna da shirin karɓar baƙuncin EFCC, shawarar Ɗankwambo ga gwamnoni masu barin gado

Daga BASHIR ISAH Tsohon Gwamnan Jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo, ya shawarci gwamnoni masu barin gado da su zauna da shirin karɓar baƙuncin hukumar EFCC da ICPC da dangoginsu waɗanda za su yi musu tambayoyi masu buƙatar amsoshi. Ɗankwambo ya shawarci gwamnonin ne a wajen taron walimar ban-kwanan da da aka shirya musu a Otel ɗin Transcorp da ke Abuja a ranar Lahadin da ta gabata. Da yake jawabi a wajen taron, tsohon gwamnan Jihar Kwara, Bukola Saraki, ya yi kira ga gwamnoni 18 masu barin gado da su sai-saita kansu bayan barin mulki don cigaban ƙasa. Saraki ya ce, “Bayan…
Read More
Mansa Musa: Mutum mafi arziki a tarihin duniya

Mansa Musa: Mutum mafi arziki a tarihin duniya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Sarkin daular Mali, Mansa Musa, wanda a wasu lokutan akan kira shi da ‘Kanku Musa’ ya kasance mutum mafi ƙarfin arziki da aka taɓa samu a duniya. Wadatarsa ta ba shi damar mayar da Timbuktu cikin birni mai ban mamaki. Ya yi sarauta tsakanin shekarar 1313 zuwa 1337. Mansa Musa shi ne Sarki na goma a jerin sarakunan masarautar Mali, kuma yana da arzikin da a yanzu darajarta ta haura dala biliyan 400. An haifi Kanku Musa a shekara ta 1280 a garin Manden. Koda yake ana yawan kiran shi Kankan Musa, amma ainihin sunansa 'Kanku'.…
Read More
Daraja da girmamawar da ake bai wa mawaƙa ba ta kai yadda ake buƙata ba – Tijjani Gandu

Daraja da girmamawar da ake bai wa mawaƙa ba ta kai yadda ake buƙata ba – Tijjani Gandu

(Ci gaba daga makon jiya) Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU A satin da ya gabata, mun faro firarmu da neman sanin ko waye mawaƙi Tijjani Gandu, kafin mu garzaya kan dalilin tattaunawar tamu, wato waƙoƙi, inda ya yi mana bayyanin yadda ya faro da kuma yadda ya sauya akalan waƙoƙinsa daga na soyayya da kuma yabon fiyayyen halitta zuwa na siyasa, da ma wanda ya zama silar faruwar hakan. Kamar yadda muka yi alƙawarin kawo maku ci gaban wannan tattaunawa, Allah Ya kawo mu, lokaci ya yi, don haka a sha karatu lafiya. MANHAJA: Shin kana ganin ýan siyasa na rama…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Likitoci sun kammala shirin fara yajin aikin gargaɗi

Da Ɗumi-ɗumi: Likitoci sun kammala shirin fara yajin aikin gargaɗi

Ƙungiyar Likitoci ta Ƙasa (NARD), za ta fara yajin aikin gargaɗi na kwana biyar. Ƙungiyar ta ce ta ɗauki wannan mataki ne bayan da Gwamnatin Tarayya ta gaza wajen cimma buƙatun mambobinta. Sanarwar da ƙungiyar ta fitar ranar Litinin ta ce, an cimma shawarar fara yajin aikin ne bayan taron da shugabanin ƙungiyar suka gudanar ta bidiyo inda suka shafe sa'o'i shida da rabi suna tattaunawa Likitocin sun ce yajin aikin zai fara ne daga ƙarfe 8:00 na safiyar ranar Larba, 17 ga Mayu, sannan ya ƙare ran Litinin, 22 ga Mayu da ƙarfe 8:00 na safe. Kafin wannan lokaci…
Read More
Amurka ta haramta wa wasu ‘yan Nijeriya biza kan yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasa

Amurka ta haramta wa wasu ‘yan Nijeriya biza kan yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasa

Gwamnatin Amurka ta ce ta ɗauki matakan haramta wa wasu 'yan Nijeriya bizar shiga ƙasar saboda yi wa tsarin dimokuraɗiyya zagon ƙasa a lokacin zaɓuɓɓukan 2023 a ƙasar. Bayanin haka na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Anthony Blinken, ya fitar a ranar Litinin, 15 ga Mayu, 2023, wadda aka wallafa a shafin intanet na gwamnatin Amurka. A cewar Sakataren “A yau, ina sanar da cewa mun ɗauki matakan ƙaƙaba takunkumin biza ga wasu 'yan Nijeriya saboda aikata zagon ƙasa ga tsarin dimokradiyya a lokacin zaɓukan Nijeriya na 2023." Blinken ya ƙara da cewa, "Amurka…
Read More