Editor

9513 Posts
Kamfanin KAEDCO zai iya rasa lasisinsa sakamakon Bashin Naira biliyan 51.93

Kamfanin KAEDCO zai iya rasa lasisinsa sakamakon Bashin Naira biliyan 51.93

Daga AMINA YUSUF ALI Kamfanin rarraba wutar lantarki na jihar Kaduna (KAEDCO) yana fuskantar barazanar rasa lasisin gudanar da kamfanonin saboda bashin Naira biliyan 51.93. Kamfanin KAEDCO ya amshi sanarwa daga hukumar kula da ƙa'idojin wutar Lantarki (NERC) a ranar Litinin xin da ta gabata. Inda ake umartar Bankin game da niyyar NERC na soke lasisinsa na gudanarwa. Wasu rahotanni da suka bayyana a ranar Talatar da ta gabata sun bayyana cewa, KAEDCO ta tara wa kanta bashin Naira biliyan 41.49 a tsakanin shekaru 2015 zuwa 2021, wanda Hukumar rarraba wutar ta Nijeriya a kan sari (NBET) da MO suka…
Read More
Man City ta kai wasan ƙarshe a gasar Zakarun Turai

Man City ta kai wasan ƙarshe a gasar Zakarun Turai

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Manchester City ta lallasa Real Madrid mai riƙe da kambun gasar Zakarun Turai a wasan daf da na ƙarshe, nasarar da ta bai wa jagorar Firimiyar damar kai wa wasan ƙarshe na gasar inda za ta haɗu da Inter Milan a Istanbul. An dai ta shi wasan na ranar Laraba ƙwallaye 4 da nema wanda ke nuna huce haushin City kan tawagar ta Carlo Ancelotti da ta fitar da ita daga gasar sau 2 a irin wannan mataki, kuma a jumulla Manchester City ta yi nasara da ƙwallaye 5 da 1 idan…
Read More
Majalisar Dattawa ta tsawaita bincike kan zargin NDDC da yin mu’amalar kuɗaɗe ba tare da izini ba

Majalisar Dattawa ta tsawaita bincike kan zargin NDDC da yin mu’amalar kuɗaɗe ba tare da izini ba

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Majalisar Dattijai ta bada ƙarin lokaci ga kwamitin wucin-gadi da ta kafa domin binciken wasu maƙudan kuɗaɗe da ake zargin Hukumar Raya Yankin Neja Delta (NDDC) ta yi mu'amalarsu ba tare da izini ba. Kwamitin wanda Yusuf Yusuf (APC, Taraba ta Tsakiya) ya jagoranta, an kafa shi ne a zaman majalisar a ranar Talatar da ta gabata, domin gudanar da bincike kan ma’amalolin da hukumar ta NDDC ta yi a kasafin kuɗinta na 2021 da 2022 ba tare da amincewar majalisar dattawa ba. Majalisar dattijai ta umarci kwamitin da ya gabatar da rahotonsa cikin…
Read More
Na bar ‘ya’ya na uku domin saduwa da iyayena – Cewar ɗalibar Chibok da aka ceto

Na bar ‘ya’ya na uku domin saduwa da iyayena – Cewar ɗalibar Chibok da aka ceto

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Kwamandan Operation Haɗin Kai, Manjo Janar Ibrahim Ali, ya ce sun ceto wata ‘yar makarantar Chibok, Saratu Dauda, wadda ta bar ‘ya’yanta uku tare da ‘yan ta’adda a dajin Sambisa da ke jihar Borno. Hakan ya zo ne kwanaki kaɗan bayan wasu abokan karatunta guda biyu Esther Marcus da Hauwa Maltha, sun tsere, inda sojojin Nijeriya suka same su tare da kai su ga gwamnatin jihar Borno. Ali, yayin da yake miƙa Saratu ga kwamishiniyar harkokin mata ta jihar Borno, Zuwaira Gambo, a ranar Litinin ɗin da ta gabata, ta ce sojoji sun cetota…
Read More
Hukumar DSS ta yi ram da Baffa Hotoro

Hukumar DSS ta yi ram da Baffa Hotoro

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Jami'an tsaron farin kaya na DSS a Kano sun cafke matashin nan Baffa Hotoro da ake zargi da yin sakin baki ga Manzon Tsira (S.A.W) Tun a watan azumin da ya gabata ne dai Gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya sanar da cewa an kama matashin amma daga bisani Baffan ya fito a bidiyo ya musanta hakan, inda ya ce yana Saudiyya aikin Umara. Amma a ranar Alhamis hukumar DSS a Kano ta tabbatar wa da gidan Radio Freedom Kano cewa suna tsare da Baffa Hotoro.
Read More
‘Yan bindiga sun sace masu yi wa ƙasa hidima a Ribas

‘Yan bindiga sun sace masu yi wa ƙasa hidima a Ribas

Daga BASHIR ISAH 'Yan bindiga sun sace wasu masu yi wa ƙasa hidima (NYSC) a kan hanyarsu ta zuwa Fatakwal bayan sun sallami sansanin 'yan yi wa ƙasa hidima a Jihar Ondo. Rahotanni daga yankin sun ce, waɗanda lamarin ya shafa wanda ba a tantance yawansu ba, an yi garkuwa da su ne a ranar Talata da misalin ƙarfe 9 na dare. Wani ganau wanda 'yar uwarsa na daga cikin waɗanda aka yi garkuwa da su ɗin, ya tabbatar wa wani gidan rediyon Fatakwal faruwar hakan a ranar Laraba. Ya ce lamarin ya auku ne a yankin Rumuji cikin Ƙaramar…
Read More
Babu mahalukin da zai hana rantsar da Tinubu – Sarkin Musulmi

Babu mahalukin da zai hana rantsar da Tinubu – Sarkin Musulmi

Daga BASHIR ISAH Mai Alfamar Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Ƙoli ta Harkar Muslunci a Nijriya, (NSCIA), Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III, ya ce babu wani mahalukin da zai dakatar da rantsar da Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Asiwaju Bola Tinubu, ya zuwa ranar 29 ga Mayu. Basaraken ya bayyana hakan ne sa’ilin da yake jawabi a wajen wani taro da Bankin Duniya ya shirya a Abuja ranar Laraba. Ya ce maimakon ƙoƙarin dagula wa rantsawar lissafi kamata ya yi ’yan Nijeriya su himmantu da yi wa gwamatin Tinubu addu’a da fatan nasara. A cewarsa: “Dole a samu canji, saboda nan da…
Read More
Hukumar NDLEA ta cafke ‘yan zaman sheƙe aya 84 a Kano

Hukumar NDLEA ta cafke ‘yan zaman sheƙe aya 84 a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi, NDLEA, shiyyar Kano, ta cafke mutane 84 yayin samamen da ta kai wani wurin shaƙatawa mai suna Bubble Club. Hukumar, ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, ASN Sadik Muhammad Maigatari, ya fitar ranar Talata. ASN Sadik ya ce, sun samu ƙorafe-ƙorafe daga mazauna yankin cewa suna zargin an mayar da wurin na shaye-shayen miyagun ƙwayoyi wanda hakan ya sa Kwamandan hukumar Abubakar Idris, ya fara tura jami’an hukumar na farin kaya domin tabbatar da zargin, kuma daga bisani…
Read More
Tsakanin Fulani da Bahaushe: InnalilLahi wa inna ilaihir rajiun!

Tsakanin Fulani da Bahaushe: InnalilLahi wa inna ilaihir rajiun!

Daga FATUHU MUSTAFA Abinda masu wannan tunani suka dogara da shi na cusa wutar gaba tsakanin Hausawa da Fulani abu biyu ne, Jihadin Shehu da kuma ta'addancin da Fulani suke yi a yau. Musamman a Arewa maso Yamma na ƙasar nan. Na yi iya ƙoƙari na in ga na kauce wa wannan shirme, amma na kasa daurewa, musamman da naga wani mutum da nake ganin ya girmi wannan shirmen Ahmad Musa Jingau ya yi wani rubutu da har yake cewa, 'Fulani most be a pariah'. Wannan magana ta bani tsoro matuqa ƙwarai. Domin kuwa ni ban ga yadda za ka…
Read More
Buɗaɗɗiyar wasiƙa ga al’ummar Kano game da ƙidaya

Buɗaɗɗiyar wasiƙa ga al’ummar Kano game da ƙidaya

Daga ABDULBAQI ALI AHMAD SHARIFAI Assalamu alaikum al'ummar jihata ta Kano mai albarka, da fatan kuna cikin ƙoshin lafiya. Bayan haka, na rubuta wannan buɗaɗɗiyar wasiƙa ne gare ku a kan abinda yake tunkarar mu na ƙidayar al'ummar ƙasar nan da za a fara a wata mai kamawa. Ku sani, ta wannan hanya ce ake rabon arzikin ƙasa gwargwadon yawan jama'a, ta haka ne kuma gwamnati ke aiwatar da ayyukan raya ƙasa. Muna da ƙalubale mai tarin yawa da muke buƙatar kulawar gwamnati musamman ta la'akari da yawanmu. Sai dai kash, sakacin shugabanni da talakawanmu na janyo mana asara mai…
Read More