Editor

9513 Posts
Gurɓatattun gwamnoni na shirin tserewa kafin rantsar da sabuwar gwamnati – EFCC

Gurɓatattun gwamnoni na shirin tserewa kafin rantsar da sabuwar gwamnati – EFCC

Hukumar EFCC ta bayyana cewa, wasu da ake zargin gurɓatattun gwamnoni da 'yan siyasa na shirin ficewa daga Nijeriya kafin ranar 29 ga Mayu inda za a rantsar da sabuwar gwamnati. Mai magana da yawun hukumar ta EFCC, Wilson Uwujaren, shi ne ya bayyana haka cikin sanarwar da ya fitar ranar Juma'a, 19 ga Mayu, 2023. EFCC ta ce tuni ta fara haɗa kai da takwarorinta na ƙetare domin tabbatar da haƙar gurɓatattun 'yan siyasar ba ta cimma ruwa ba. Hukumar ta sha alwashin tabbatar da dukkan gurɓatattun 'yan siyasar sun girbi abin da suka shuka sa'ilin da suke riƙe…
Read More
Abin da Kwankwaso da Tinubu suka tattauna a ƙasar waje

Abin da Kwankwaso da Tinubu suka tattauna a ƙasar waje

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Ƙasa mai jiran gado, Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri da ɗan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Kwankwaso a ƙasar Faransa. Wata majiya mai tushe ta ce Tinubu ya yi wa Kwankwaso tayin tafiya tare da shi a sabuwar gwamnati da kuma duba yiwuwar sulhu tsakaninsa da Gwamnan Kano mai barin gado, Abdullahi Ganduje. A ranar Litinin, mako biyu kafin Tinubu ya karɓi rantsuwar fara aiki, suka shafe sama da awa huɗu suna ganawar sirrin da Kwankwaso a birnin Paris na ƙasar Faransa. Majiyarmu ta ce a yayin ganawar,…
Read More
Xherdan Shaqiri ya zama ɗan wasa mafi yawan albashi a MLS ta Amurka

Xherdan Shaqiri ya zama ɗan wasa mafi yawan albashi a MLS ta Amurka

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Wasu bayanai na nuna cewa ɗan wasan gaba na Switzerland Xherdan Shaqiri shi ne ɗan wasa mafi ɗaukar albashi a Lig ɗin MLS da ke Amurka. Bayanan da aka fitar a ranar Talata sun nuna cewa, Shaqiri da ke taka leda da Chicago Fire na ɗaukar albashin dala miliyan 8 da rabi yayin da Lorenzo Insigne da ke taka leda da Toronto ke ɗaukar albashin dala miliyan 7 da rabi kana Javier Hernandez na Los Angeles Galaxy a matsayin na 3 da albashin dala miliyan 7. Shaqiri mai shekaru 31 wanda ya taka leda da ƙungiyoyin…
Read More
Majalisar Wakilai ta amince wa Buhari karɓar bashin N368bn daga Bankin Duniya

Majalisar Wakilai ta amince wa Buhari karɓar bashin N368bn daga Bankin Duniya

Majalisar Tarayya ta Ƙasa ta amince wa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da ya kinkimo bashin Naira biliyan 368.7 (Dala miliyan 800) daga Bankin Duniya. Mamba a Kwamitin Majalisar Wakilai kan Sha'anin Bashi da Tallafi, Abubakar Yunusa Ahmad, shi ne ya bayyana haka a wani shiri da Tashar Channels Television ta yi da shi a ranar Juma'a. Sai dan majalisar ya ce ba za a yi amfani da bashin ba a gwamnatin Buhari mai ƙarewa. Yana mai cewa, gwamnati mai jiran gado ce za ta sarrafa bashin don cimma manufar da ta sa aka ciyo shi. A cewarsa, game da Dala…
Read More
Ba a biya mu kuɗin aikin zaɓen 2023 ba, cewar wasu masu aikin wucin-gadi na INEC

Ba a biya mu kuɗin aikin zaɓen 2023 ba, cewar wasu masu aikin wucin-gadi na INEC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wasu daga cikin ma’aikatan wucin-gadi da suka yi aikin zaɓen 2023 a Nijeriya sun koka kan rashin biyan su kuɗaɗen alawus-alawus na aikin da suka yi. Ma’aikatan waɗanda suka ce suna da yawan gaske a faɗin ƙasar sun nemi Hukumar Zaven, INEC ta taimaka ta biya su haƙƙoƙinsu. A watannin Fabarairu da kuma Maris ɗin shekarar 2023 ne aka gudanar da zaɓukan Shugaban Ƙasa da na ‘yan majalisu da kuma gwamnoni a Nijeriyar. Ɗaya daga cikin irin waɗannan ma'aikatan na wucin-gadi daga jihar Kano ya shaida wa BBC cewa a jihar kaɗai akwai abokan…
Read More
Rikici ya ɓarke a Majalisar Wakilai kan zargin karkatar da maƙudan kuɗaɗe

Rikici ya ɓarke a Majalisar Wakilai kan zargin karkatar da maƙudan kuɗaɗe

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Mambobin Majalisar Wakilai na shirin yin kaca-kaca da Kakakin Majalisar, Femi Gbajabiamila bisa zargin karkatar da wasu maƙudan kuɗaɗe da suka kai dala miliyan 15 daga ɓangaren zartarwa na gwamnati. ’Yan majalisar da suka fusata sun yi zargin cewa Gbajabiamila ya ƙulla yarjejeniya da ɓangaren zartaslrwa a madadin majalisar na zartar da hanyoyin da za a bi wajen karɓo bashi daga babban bankin Nijeriya (CBN) na Naira tiriliyan 22.7, amma sai ya gajarce daga abokan aikinsa wajen raba dala miliyan 15 da aka bai wa Majalisar don jin daɗin yarjejeniyar. Rikicin da ake fama da shi,…
Read More
Yarima Harry na Birtaniya da matarsa sun tsallake rijiya da baya

Yarima Harry na Birtaniya da matarsa sun tsallake rijiya da baya

Yarima Harry da matarsa Meghan sun tsallake rijiya da baya a lokacin da motarsu ta kusa yin taho mu gama da wasu motocin, sa'ilin da masu ɗaukar hoto ke bin su a mota. Lamarin ya faru ne a lokacin da yariman da matarsa suka bar wurin wani bikin bayar da kyatuka a birnin New York na Ƙasar Amurka. Wata sanarwa da ta samu sa hannun mai magana da yawun yariman, ta ce masu faukar hoton sun rinƙa bin ma’auratan a guje cikin mota har tsawon kusan sa’a biyu. Sanarwar ta ce, hakan ya sanya motar da suke ciki ta kusa…
Read More
An kashe mutane aƙalla 85 a rikicin yankin tsakiyar Nijeriya – Rahoto

An kashe mutane aƙalla 85 a rikicin yankin tsakiyar Nijeriya – Rahoto

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Sama da mutane 3,000 ne suka rasa matsugunansu a tsakiyar Nijeriya bayan da aka kashe mutane 85 a rikicin makiyaya da manoma, a cewar wani rahoto a ranar Alhamis. Rikicin ya ɓarke ne a ranar Litinin da ta gabata, inda aka kashe mutane 30, a ƙauyuka da dama na Jihar Filato, yankin da ya kwashe shekaru yana fama da rikicin ƙabilanci da addini. Rikicin dai ɗaya ne daga cikin ɗimbin ƙalubalen tsaro da ke fuskantar zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, wanda zai karɓi ragamar mulkin ƙasar da ta fi yawan al’umma a Afirka a ƙarshen wannan…
Read More
Ma’aikacin Leadership Hausa, Sabo Ahmad ya rasu

Ma’aikacin Leadership Hausa, Sabo Ahmad ya rasu

Jaridar Leadership Hausa ta rasa shugaban sashen fassara, Malam Sabo Ahmed Kafin-Maiyaki wanda ya rasu a ranar Alhamis 18 ga watan Mayu, 2023 yana da shekaru 54 a duniya bayan doguwar jinya. A cewar Leadership Hausa, sanarwar da iyalansa suka fitar, Malam Sabo ya rasu ya bar mata biyu da ‘ya’ya 10 da kuma ɗan uwa guda ɗaya. Sanarwar ta kuma bayyana cewa, za a yi jana’izarsa a ranar Juma’a, 19 ga watan Mayu, 2023 a Samaru, Zariya, a Jihar Kaduna. Da yake ƙarin haske, Editan Leadership Hausa, Abdulrazaq Yahuza Jere, ya bayyana Malam Sabo a matsayin babban ginshiƙin sashen…
Read More
Muna da kyakkyawar fata Atiku Abubakar zai nasarar zama Shugaban Ƙasa a kotu – Mai-Nasiha

Muna da kyakkyawar fata Atiku Abubakar zai nasarar zama Shugaban Ƙasa a kotu – Mai-Nasiha

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Wani ɗan Jam'iyyar PDP a Jihar Kano, Alhaji Salman Mai Nasiha ya bayyana cewa a yadda suke ganin ana gudanar da shari'ar ƙorafin zaven Shugaban Ƙasa a Babbar Kotun Abuja, suna kyautata zaton Atiku Abubakar zai yi nasara. Mai-Nasiha ya bayyana hakan ne yayin da yake hira da 'yan jarida, inda kuma ya yi nuni da cewa al'ummar ƙasar nan sun yi wa Buhari kyakkyawan zato a mulkinsa za su samu saulin rayuwa da walwala amma sai ga shi ya jefa mutane a mafi ƙuncin rayuwa da ba a tava tsammani ba. Ya ƙara da…
Read More