Editor

9513 Posts
Ba za mu amince da hatsaniya ranar rantsar da Gwamnan Kano ba – CP Gumel

Ba za mu amince da hatsaniya ranar rantsar da Gwamnan Kano ba – CP Gumel

Daga RABIU SANUSI a Kano Rundunar 'Yan Sandan Jihar Kano ƙarƙashin kwamishinanta CP Muhammad Usaini Gumel ta tabbatar da cewa ba za ta amince dukkan wani nau'i na kawo tashin hankali ko tarzoma a bikin rantsar da gwamnan jihar Kano a ranar 29 ga watan Mayun nan da sauran 'yan majalisar jiha da tarayya. Wannan batun na zuwa ne a wata sanarwa da Kakakin Rundunar SP Abdullahi Kiyawa ya raba wa manema labarai a ranar Talatar nan da ta gabata. Sanarwa tabce kwamishinan ya kuma ja kunnen dukkan magoya bayan waɗannan jam'iyyu da iyayen gidansu kan batun tsatsauran ra'ayi na…
Read More
An kashe Naira Biliyan 224 akan ƙidayar ƙasa da aka ɗage

An kashe Naira Biliyan 224 akan ƙidayar ƙasa da aka ɗage

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shugaban Hukumar Ƙidaya ta Ƙasa, Alhaji Nasir Isa Kwarra, a ranar Alhamis da ta gabata, ya yi tsokaci kan yadda aka kashe Naira biliyan 224 da Gwamnatin Tarayya ta fitar, domin gidanar da ƙidayar gidaje da yawan jama’a a shekarar nan ta 2023. Kuɗaɗen farko da aka ware domin gudanar da atisayen sun kai Naira Biliyan 800, amma an ɗage bayan ɗage babban zaɓe ƙasa. Isa Kwara ya bayyana hakan ne a Abuja yayin wani taron karin kumallo da wasu zaɓaɓɓun shugabannin kafafen yaɗa labarai cewa, “an kashe Naira biliyan 224 wajen shirye-shiryen gudanar da atisayen…
Read More
Za a jinginar da filayen jirgin saman Kano da Abuja

Za a jinginar da filayen jirgin saman Kano da Abuja

*Za a ƙara ciwo bashin Dala miliyan 800*Za a nutsar da kuɗin a shirin rage raɗaɗin cire tallafin fetur Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin Nijeriya ta amince a jinginar da filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja da kuma Malam Aminu Kano da ke Kano. Gwamnati ta amince da wannan mataki ne a taron majalisar koli da aka gudanar ranar Laraba a Abuja. Ministan Sufirin Jiragen Sama a Nijeriya, Hadi Sirika, ya shaida wa BBC cewa za a jinginar da filin jirgin Abuja na shekara 20, sannan na Kano na tsawon shekara 30. Sirika ya ce taron…
Read More
Buhari zai karrama Tinubu da Shettima da manyan lambobin yabo na ƙasa

Buhari zai karrama Tinubu da Shettima da manyan lambobin yabo na ƙasa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja A ranar Alhamis, 25 ga Mayu, 2023, ne Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari zai karrama zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa mai jiran gado, Bola Ahmed Tinubu, da kuma Kashim Shettima, Zaɓaɓɓen Mataimakin Shugaban Ƙasa. Tinubu dai za a ba shi babban kwamandan oda na Tarayyar Nijeriya (GCFR) yayin da Shettima za a karrama shi da Grand Commander of the Order of the Niger (GCON). Tolu Ogunlesi, mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa kan harkokin sadarwar zamani da sabbin kafafen yaɗa labarai, ya sanar da ci gaban a ranar Alhamis.
Read More
Mu na cigiyar masu yi wa gwamnatin Ganduje kwarmato – NNPP

Mu na cigiyar masu yi wa gwamnatin Ganduje kwarmato – NNPP

Daga RABI'U SANUSI Kano An buƙaci al'ummar Jihar Kano da su taimaka wa gwamnati mai jiran gado a ƙarƙashin jagorancin Abba Kabir Yusif da bayanai kan yadda aka gudanar gwamnati mai barin gado a jihar a ƙarƙashin jagorancin Dr. Abdullahi Umar Ganduje. Wannan na zuwa ne daga bakin shugaban kwamitin karɓar mulki na gwamnan Kano mai jiran gado, Dr. Baffa Bichi, inda ya buƙaci al’ummar jihar Kano da su taimaka wa gwamnati mai mai zuwa da bayanai game da gwamnatin Abdullahi Ganduje. Dr Baffa Bichi ya bayyana haka ta hannu babban sakataren yaɗa labarai na gwamnan mai gado Malam Sanusi…
Read More
Shekaru biyar za a kwashe a jere ana fama da tsananin zafi- Bincike

Shekaru biyar za a kwashe a jere ana fama da tsananin zafi- Bincike

Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa, tun daga shekarar da muke ciki ta 2023 zuwa 2027 za su kasance masu tsananin zafi da ba a taɓa samu ba a tarihi, sakamakon yadda tiriri mai gurɓata muhalli ke ci gaba da yawaita. Ƙwararrun majalisar kan yanayi sun bayyana cewa, duniya za ta ga shekaru biyar a jere da za a yi tsananin zafi wanda ke da nasaba da ɗumamar yanayi da ke ci gaba da barazana ga halittun ban ƙasa. Bayan wani taro da tawagar ƙwararrun ta gudanar, biyo bayan dogon bincike game da tsananin zafin da duniya ke gani,…
Read More
An kafa ƙungiyar mata masu kasuwancin intanet a Kano

An kafa ƙungiyar mata masu kasuwancin intanet a Kano

Daga AMINA YUSUF ALI Mata masu gudanar da kasuwanci a shafukan intanet a jihar Kano da ke Arewacin Najeriya sun kafa wata ƙungiya mai suna Women Online Vendors Association (WOVA) da za ta samar da aminci tare da kyautata hulɗa tsakanin mai saye da mai sayarwa. Shugabar ƙungiyar ta WOVA Hajiya Ayat Uba Adamu ta bayyana wa majiyarmu cewa sun kafa ƙungiyar ne da nufin haɗa kan matan da suke gudanar da kasuwancinsu a shafukan intanet tare kuma da samar da aminci tsakanin masu saye da sayarwa. “Samar da aminci tsakanin masu saye da sayarwa ta hanyar karkaɗe ɓata gari…
Read More
Sheikh Idris Dutsen Tanshi da jami’an tsaro su ka cafke a Bauchi ya samu belin kotu

Sheikh Idris Dutsen Tanshi da jami’an tsaro su ka cafke a Bauchi ya samu belin kotu

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Babbar Kotun Majistare ta ɗaya a Jihar Bauchi wacce Mai Shari'a Abdul Fatah Ba Shakoni ke jagoranci a ranar Talata da ta gabata ne ta bayar da belin wani firaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Idris Abdul'aziz akan kuɗi Naira miliyan ɗaya da madadin su na fitattun mutane uku. Kotun ta zayyana mutanen da za su karɓi belin shehin malamin da suka haɗa da Hakimi da shehin ke mazauni a ƙarƙashin mulkinsa, babban sakatare dake cikin mulkin gwamnatin jihar Bauchi wanda zai nuna takardar mallakar kadara da kuɗin ta ba zai gaza Naira miliyan biyar ba,…
Read More
Blinken ya tattauna da Tinubu ta wayar tarho don ƙara inganta hulɗar difilomasiyya tsakanin Nijeriya da Amurka

Blinken ya tattauna da Tinubu ta wayar tarho don ƙara inganta hulɗar difilomasiyya tsakanin Nijeriya da Amurka

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Antony J. Blinken, ya tattauna da Zaɓaɓɓen Shugaban Nijeriya Bola Tinubu. Blinken ya kira Tinubu ne ta wayar tarho a safiyar Laraban nan da ta gabata, inda ya nuna zimmarsa na ganin Amurka ta qara ƙarfafa hulɗar dangataka da Nijeriya, musamman ma da gwamnati mai zuwa. Ya ce ƙasashen biyu sun ɗauki tsawon lokaci suna hulɗa mai kyau, inda ya ce yana so ya ga ɗorewar hakan ƙarƙashin mulkin Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasar Tinubu. Tinubu da Blinken sun kuma tattauna kan muhimmancin gudanar da gwamnatin da za tafi da duka 'yan…
Read More
Bauchi ta ƙaddamar sabuwar kotun bin ba’asin haƙƙoƙin jama’a

Bauchi ta ƙaddamar sabuwar kotun bin ba’asin haƙƙoƙin jama’a

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Babbar Kotun Shari'a ta Jihar Bauchi, ƙarƙashin jagorancin Babbar mai Shari'a ta jiha, Mai Shari'a Rabi Talatu Umar a makon daya gabata ne ta ƙaddamar da wata sabuwar ƙaramar kotu mai bin ba'asin ƙananan haƙƙoƙin jama'a, musamman waɗanda suka jiɓanci bashin kadarori ko kuɗaɗe ko majiɓantan lamuran kasuwanci. Wannan sabuwar kotun bin ba'asin haƙƙoƙin jama'a tana da rassa guda uku, guda biyu a shiyyar Bauchi, guda a shiyyar Katagum, waɗanda Alƙalan lardi (Majisri) za su jagoranta da suka haɗa da Alkali Abdullahi Garba, Alkali Kawu Bala da Alkaliya Zainab Shu'aibu. Da take ƙaddamar da sabuwar…
Read More