Editor

9513 Posts
Tasirin motsa jiki ga lafiya (1)

Tasirin motsa jiki ga lafiya (1)

Daga AISHA ASAS Motsa jiki wata ɗabi’a ce da har yau ba ta gama zama ‘yar gida a Ƙasar Hausa ba. Har a wannan lokacin akwai waɗanda ke kallon sa a layin ɗaya daga cikin gutsiri-tsoma da bature ke rajin karewa tare da ba shi muhimmanci, wanda a wurin su duk rashin aikin yi ne. Da yawa ba su amince cewa, atisaye na taka muhimmiyar rawa a layifar gangar jikinsu ba. Wannan ne ya sa jaridar Manhaja ta zaqulu wannan darasin don ya zama wayar da kai ga waɗanda suka jahilce shi, ya kuma ƙara wa masu yi karsashi, sannan…
Read More
Muhimmancin kunya a rayuwar Bahaushe

Muhimmancin kunya a rayuwar Bahaushe

Assalam alaikum. Idan mai karatu na biye da mu a wasiƙunmu na baya-bayan nan, mun yi magana ne akan matsayin kunya a al'adar Bahaushe sannan daga bisani kuma muka gangaro muka duba asalin waɗanda shi wanna al'adar tafi shafa a cikin al'umma. Yadda kunya ta kasance a rayuwar Bahaushe jiya, ba haka ta ci gaba da kasancewa a yau ba, domin kuwa ta samu ’yan sauye-sauye, sakamakon mu’amalar wasu da wasu baƙin ƙabilu da suka shigo ƙasar Hausa, suka mamaye. Manyan al’umma da suka fi tasiri a kan rayuwar Bahaushe su ne Larabawa da Turawa. Larabawa: Larabawa da suka shigo…
Read More
A riƙa kula da masu lalurar ƙwaƙwalwa

A riƙa kula da masu lalurar ƙwaƙwalwa

Asslama alaikum. Barka da Juma'a, ’yan uwa musulmi. A farko dai, daga cikin alamomin da ake iya kula a gane mutum na dauke da wannan damuwa, ko kuma a ce hankalin sa ya fara tavuwa, a cewar wani ƙwararren likitan ƙwaƙwalwa, Dr Maigari Yusuf Taru, idan aka ga halayyar mutum na canja wa daga wani yanayi da aka saba da shi zuwa wasu halaye da ba san shi da su ba, kamar idan an ga mutum mai tsafta ya fara zama ƙazami, ko mutum mai shiru-shiru, a ga ya koma magana barkatai, ko idan yana da son shiga jama'a sai…
Read More
CBN ya ci tarar Bankin Sterling miliyan 218 saboda karya dokoki tara

CBN ya ci tarar Bankin Sterling miliyan 218 saboda karya dokoki tara

Daga AMINA YUSUF ALI An ci tarar Bankin Sterling kimanin kuɗi har Naira miliyan 218 million saboda saɓa wa dokoki har guda tara na Babban Bankin Nijeriya (CBN). Wannan bayanin ya bayyana ne a cikin jawabin kuɗi na bankin na shekarar 2021 wanda aka saki a mako biyu da suka gabata. CBN ya ci tarar Bankin Sterling Naira miliyan 62 saboda sanya bankin a ƙarƙashin NEMSF. Haka Babban bankin ya caji Bankin Sterling ɗin ƙarin wasu kuɗaɗe 56 da kuma Naira miliyan 52 a kan sauran dokokin da ta karya. Hakazalika, Bankin Sterling ɗin kuma ya bayyana cewa, CBN ɗin…
Read More
Masu ƙwacen waya sun tsallake rijiya da baya a Kano

Masu ƙwacen waya sun tsallake rijiya da baya a Kano

Daga RABI'U SANUSI a Kano A ci gaba da fafutukar ganin cewa jami'an tsaro sun samu nasarar kawo ƙarshen masu ƙwacen waya a Jihar Kano da ma wasu maƙwabtan jihar, kawo yanzu al'ummar jihar sun fara ɗaukar matakin kare kansu daga ta'addancin 'yan fashin wayar inda a wasu lokutan sukan yi kisa da jikkata mutane. A ranar Asabar da misalin ƙarfe 10:30 na dare, wasu 'yan ƙwacen wayar suka yi ta'asa a kan titin Kabuga. Lamarin da ya sanya al'umma yin ƙoƙarin kama su a cikin babur din adai-daita sahu amma suka tsere. Bayanai sun ce jama'a sun samu damar…
Read More
Mutun huɗu sun mutu sakamakon fashewa mai ƙarfi a Sakkwato

Mutun huɗu sun mutu sakamakon fashewa mai ƙarfi a Sakkwato

Aƙalla mutum huɗu aka tabbatar sun mutu, sannan wasu uku sun jikkata sakamakon fashewar da ta auku a wani shagon mai welda a yankin Ƙaramar Hukumar Isa, Jihar Sakkwato. Wani mazaunin yankin ya shaida wa manema labarai cewar, "Na ɗauka 'yan bindiga ne suka shigo a lokacin da na ji ƙarar fashewar" wadda ta auku a ranar Lahadi da rana. Da aka nemi jin ta bakinsa, Kakakin 'yan sandan jihar, DSP Sanusi Abubakar, ya tabbatar da aukuwar hakan. Ya ce mutum huɗu ne suka mutu sakamakkn iftila'in. A cewar Abubakar, "Fashewar ba ta da alaƙa da matsalar tsaron da ta…
Read More
Hada-hadar kasuwar ’yan wasan ƙwallon ƙafa

Hada-hadar kasuwar ’yan wasan ƙwallon ƙafa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ɗan wasan tsakiya na Arsenal da Norway Martin Odegaard na shirin ƙulla sabuwar yarjejeniya da ƙungiyar kasancewar kwantiraginsa na yanzu zai kare a 2025. Kocin Bayer Leverkusen Xabi Alonso ya bayar da tabbacin ci gaba da zama a ƙungiyar ta Jamus a kaka ta gaba bayan da aka riƙa danganta tsohon ɗan wasan na Liverpool da aikin kocin Tottenham da ba kowa a yanzu. Ɗan wasan Arsenal Albert Sambi Lokonga, mai shekara 23, zai so tafiya Burnley domin sake haɗewa da kociya Vincent Kompany, wanda ya koyar da ɗan Belgium ɗin a Anderlecht. Ɗan wasan Ivory…
Read More
Ba zan ci amana ba – Shugaba Buhari

Ba zan ci amana ba – Shugaba Buhari

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Amana dai tana da muhimmanci wajen tabbatar da adalci a tsakanin jama’a. Adalci a fasasrarsa a shari’a shi ne sanya kowane a inda ya dace da shi da miƙa haƙƙi ga mai haƙƙi. In an zo raba arzikin ƙasa a yi adalci. Duk dan ƙasa ya amfana da arzikin ƙasarsa daidai gwargwadon abun da ya dace da shi. Matuƙar za a yi adalci to kusan kowa ko akasarin jama’a za su samu ingancin rayuwa. Akasin adalci shi ne zalunci. Duk wata ƙasa a duniya na buƙatar adalci don samun cigaba mai ma’ana. Aa tarihi mai zurfi…
Read More
MTN na shirin ƙara kuɗin kira da farashin data

MTN na shirin ƙara kuɗin kira da farashin data

Kamfanin sadarwa na MTN ya ce yana shirin ƙara kuɗin kira da farashin Data saboda tsadar rayuwa da yawan harajin da aka ɗora wa kamfanin. Bayanin haka na ƙunshe ne cikin rahoton zangon farko na da kamfanin ya fitar kwanan nan. Kamfanin ya ce da alama yanayin kasuwanci a ragowar 2023 zai kasance mai tattare da ƙalubale. Don haka kamfanin ya ce shi ma zai duba sannan ya yi abin da ya dace don iya tafiyar da harkokinsa a wannan lokaci na ƙalubale. Kamfanin ya ƙara da cewa, ƙarin farashin shi ne mafita a wannan hali, saboda ta haka ne…
Read More
Tinubu ya ƙalubalanci Atiku kan yaɗa shari’ar zaɓen Shugaban Ƙasa kai-tsaye

Tinubu ya ƙalubalanci Atiku kan yaɗa shari’ar zaɓen Shugaban Ƙasa kai-tsaye

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Zaɓaɓɓen Shugaban Nijeriya mai jiran gado, Bola Tinubu, na adawa da buƙatar da ɗan takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya yi na watsa shirye-shiryen kai tsaye kan yadda zaɓen ke gudana. A martanin da aka gabatar a ranar Laraba, Tinubu da mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ta hannun tawagar lauyoyinsu ƙarƙashin jagorancin Wole Olanipekun, sun ce buƙatar ta cin zarafin kotu ne. Sun buqaci Kotun Sauraron Ƙararrakin Zaven Shugaban Ƙasa da ta yi watsi da bukatar, suna masu cewa agajin da masu neman zaɓen suka nema bai kai yadda kotu za…
Read More