*Buhari ya nemi majalisa ta ba shi damar ƙara ciwo bashi
*Ya na son ciwo qarin bashin Naira biliyan 368.7 ne
*Kwanaki 16 suka rage masa a gadon mulki
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Ƙungiyar Malaman Jami’o’i a Nijeriya (ASUU) ta bayyana buƙatar Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari na neman Majalisar Dattawa ta sahale masa ya ciwo bashin Naira Biliyan 368.7 a matsayin wani abin da bai dace ba kwanakin kaɗan kafin barin shi mulki.
Farfesa Emmanuel Osodeke, Shugaban Ƙungiyar ASUU na Ƙasa, ya bayyana haka ne a jiya Alhamis yayin da yake jawabi a wajen bikin bayar da lambar yabo ta ɗalibai masu zuwa gida da kuma ƙaddamar da wani ajin zamani na Naira miliyan 100 daga Sashen Ilimi na Jami’ar Nnamdi Azikiwe dake Awka a Jihar Anambra.
Ya ce, buƙatar ta fito ƙarara ta nuna rashin muhimmancin gwamnatin da Buhari ke yi wa ilimi.
A ranar Laraba ne Buhari ya rubuta wa Majalisar Dattawa, inda ya buƙaci ta amince da sabon neman rancen Dala Miliyan 800 (daidai da Naira Biliyan 368.7) da za a yi amfani da shi wajen bunƙasa tsarin samar da zaman lafiya a ƙasa da za a samu daga Bankin Duniya.
Sai dai Shugaban na ASUU ya ce, adadin kuɗin da ya kai ga yajin aikin na watanni takwas ya yi nisa ga rancen da Shugaban Ƙasar ke nema.
Ya ce: “mu na cikin ƙasar da tsarin da ake bi na nuna ko-in-kula da ilimin ’yan ƙasa ne. A jiya ne dai wani Shugaban Ƙasa da ya rage kwanaki 18 ya sauka daga mulki ya aika da takarda zuwa Majalisar Dattawa, domin ba shi bashi Dala miliyan 800 wanda ya yi daidai da Naira biliyan 600.
“A halin yanzu, dalilin da ya sa mu ka shiga yajin aikin na tsawon watanni takwas shi ne saboda muna neman ƙasa da Naira biliyan 200. Duk da haka, za ku iya ɗaukar Naira biliyan 600 don tallafa wa iyalai da 5000. Me Naira 5000 zai iya yi wa iyalai? Me ya sa ba za a saka hannun jarin wannan ga cibiyoyin ilimi don tabbatar da inganci da ingantaccen ilimi ba?”
Yayin da ya yaba da kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin malaman makarantar da tsofaffin ɗaliban makarantar, Osodeke ya danganta hakan ga yadda aka yi wa ‘ya’yan ƙungiyar a lokacin karatunsu, inda ya buƙace su da su ci gaba da hakan.
Mataimakin Shugaban Jami’ar, Farfesa Charles Esimone ya bayyana a matsayin babban gudunmawar tsofaffin ɗaliban kowace jami’a, inda ya yi alƙawarin ci gaba da tallafa wa ƙungiyar.
“Gwamnatina ta nemi sa hannun mutane da ƙungiyoyi masu kishin ƙasa wajen cimma wannan buri tare da ƙarfafa gwiwar malamai da ma’aikatan jami’a da su yi hakan.
“Na yi farin ciki da ganin cewa abubuwan da suka faru a kwanan nan a cikin cibiyoyin, ciki har da wannan taron, sun nuna ƙara fahimtar ƙungiyar tsofaffin ɗaliban jami’a game da rawar da ake sa ran su na cimma burina,” inji shi.
Tun da farko, Shugaban taron, Chief Emeka Nwabueze ya buƙaci Mataimakin Shugaban Jami’ar da ya tuntuɓi ‘yan kasuwa don taimaka masa wajen bunƙasa jami’ar.