14
May
Fitaccen jarumi a masana’antar shirya fina-finai ta Nollywood, Saint Obi, ya bar duniya yana da shekara 57. Jarumin ya rasu ne bayan fama da rashin lafiya. Bayanai sun ce jarumin ya cika ne a ranar Lahadin da ta gabata, 7 ga Mayu, a gidan wata 'yar uwarsa. A cewar rahotanni, rashin jituwa a tsakanin ‘yan uwansa ya haifar da tsaiko wajen sanar da rasuwar marigayin a hukumance. Majiya ta ce bayan rasuwar marigayin a ranar Lahadin, an ɗauke gawarsa zuwa ɗakin adana gawarwaki na Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos (JUTH). Jaridar Intel Region ta rawaito cewar, a baya-bayan nan Saint…
