Editor

9513 Posts
An kai malama kotu bisa zargin cin zarafin ɗaliba ‘yar shekara tara

An kai malama kotu bisa zargin cin zarafin ɗaliba ‘yar shekara tara

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wata malama, Aderonke Makonde, a ranar Laraba aka gurfanar da ita a wata kotun majistare da ke Ikeja a Jihar Legas bisa zargin laifin cin zarafin wata ɗalibar makarantar mai shekara tara. Rundunar 'yan sanda ce ta gurfanar da Makonde, mai shekaru 35 kuma malama a makarantar Westgate Land Emperial Creche Nursery and Primary School da ke Mushin, Legas bisa laifin cin zarafi. Sai dai matar ta musanta zargin da ake mata. Lauyar masu shigar da ƙara, DSP Kehinde Ajayi, ya shaida wa kotun cewa Makonde ta ci zarafin ɗalibar ne ta hanyar “shasshauɗa…
Read More
EFCC ta kama tsohon ministan lantarki, Saleh Mamman kan zargin karkatar kuɗi

EFCC ta kama tsohon ministan lantarki, Saleh Mamman kan zargin karkatar kuɗi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Jami’an hukumar yaƙi da cin hanci da hana yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta’annati sun kama tsohon ministan lantarki na Nijeriya, Injiniya Saleh Mamman, wata majiya a ma’aikatar lantarki ta tarayya ta shaida wa BBC. Kafofin yaɗa labaran ƙasar sun ce EFCC ta kama Saleh Mamman ne tun da sanyin safiyar Laraba inda suke ci gaba da tsare da shi a shalkwatar hukumar da ke Abuja. Sun ce kamen na da alaƙa da zargin almundahanar wasu kuxaxie kimanin naira biliyan 22. A cewarsu, jami’an Hukumar EFCC sun kama Saleh Mamman ne game da jerin…
Read More
Jam’iyyar NNPP na zargin Ganduje da sayar wa da ɗansa kadarorin gwamnati

Jam’iyyar NNPP na zargin Ganduje da sayar wa da ɗansa kadarorin gwamnati

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Jam’iyyar NNPP a Kano, ta zargi gwamnatin APC ƙarƙashin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, da siyar da wasu kadarori mallakin gwamnatin jihar. Zargin wanda ake kallon gwamnatin jihar na siyar da kadarorin ga ɗan gwamna ba bisa ƙa’ida ba, abin da Jam'iyyar NNPP ta ce ba za ta lamunta ba. Har ma jami’iyyar ta ce za ta yi bincike da tabbatar da hukunci da zarar sun karɓi mulkin Kano a ranar 29 ga watan Mayu. Jawabin hakan na zuwa ne ta bakin shugaban kwamitin karɓar mulkin jihar Kano na Jam’iyyar NNPP Abdullahi Baffa Bichi, yayin wata…
Read More
Isra’ila da Islamic Jihad sun yi wa juna ruwan makaman roka cikin dare

Isra’ila da Islamic Jihad sun yi wa juna ruwan makaman roka cikin dare

Sojojin Isra’ila da mayaƙan Islamic Jihad a yankin Gaza sun sake shafe tsawon dare suna kai wa juna hare-haren manyan makamai dai dai lokacin da alƙaluman Falasɗinawan da aka kashe cikin kwanaki 2 da faro rikicin ke tasamma 22. Rikicin wanda ke matsayin mafi muni da aka gani tsakanin ɓangarorin biyu a watannin baya-bayan nan kowanne ɓangare na ci gaba da harba makaman roka ta yadda babu abin da ake jiyowa sai ƙarar harbawa da kuma tarwatsewarsu, kamar yadda majiyoyin labaran da ke sanya idanu kan rikicin ke bayyanawa a wani yanayi da Masar ke shige da fice don ganin…
Read More
Rashin biyan alawus ya sa Majalisar Dokokin Binuwai dakatar da zamanta

Rashin biyan alawus ya sa Majalisar Dokokin Binuwai dakatar da zamanta

'Yan Majalisar Dokokin Jihar Binuwai sun dakatar da zaman Majalisar saboda rashin biyansu ariyas na albashi da alawus-alawus na wata shida. Dakatar da zaman ya sa wata dokotar fansho da Gwamnan jihar, Samuel Ortom, ya aika wa majalisar don neman amincewarta na fuskantar tsaiko. Sabuwar dokar ta fansho na neman a riƙa bai wa tsofaffin gwamnonin jihar sabbin motoci guda huɗu duk shekara huɗu da kuma gida na din-din-din. Kazalika, dokar na neman a bai wa tsaffin gwamnonin damar ɗaukar ma'aikata shida da kuma ma'aikata uku ga mataimakansu. Hon. Bem Mngutyo ya faɗa a ranar Alhamis cewar, Majalisar "ta yanke…
Read More
Ba ni ba sake fitowa takara bayan na kammala wa’adina na biyu, inji Gwamna Abdullahi Sule

Ba ni ba sake fitowa takara bayan na kammala wa’adina na biyu, inji Gwamna Abdullahi Sule

Daga JOHN D. WADA a Lafiya Gwamnan Jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule, ya ce da zarar ya kammala wa’adinsa na biyu a matsayin gwamnan jihar, ba zai sake fitowa takarar kujerar siyasa ba har ƙarshen rayuwarsa. Gwamnan ya sanar da haka ne a lokacin da yake karɓar baƙuncin ‘ya’yan ƙungiyar masu aiko da rahoto wato Correspondents Chapel a turance na ƙasa reshen jihar ta Nasarawa waɗanda suka kai masa ziyarar taya shi murnar bikin ƙaramar Sallah da aka gudanar kwanan nan a gidansa dake garin Gudi dake yankin Ƙaramar Hukumar Akwanga a jihar. Ya ce a yanzu Alhamdu lillah da…
Read More
Dangote ya kusa ƙaddamar da katafariyar matatar mai a Legas

Dangote ya kusa ƙaddamar da katafariyar matatar mai a Legas

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ana sa ran Kamfanin Matatar Man Fetur na Dangote na biliyoyin daloli zai kawo mafita ga al'amuran matatar mai a Nijeriya. An ruwaito wata majiya ta bayyana cewa, shugaba Buhari zai ƙaddamar da kamfanin. A baya dai, kamfanin Dangote ya yi nuni da cewa, za a ƙaddamar da matatar man a Legas kafin ƙarshen wa’adin mulkin shugaba Buhari a ranar 29 ga watan Mayun 2023. Babban jami’in hulɗa da jama’a na kamfanin Dangote, Mista Anthony Chiejina, a wata sanarwa da ya fitar ya ƙaryata rahotannin da ke cewa matatar na daga cikin ayyukan da Buhari zai…
Read More
Busquets zai yi bankwana da Barcelona a ƙarshen kakar nan

Busquets zai yi bankwana da Barcelona a ƙarshen kakar nan

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Sergio Busquets ya tabbatar da zai bar Barcelona a ƙarshen kakar nan, bayan shekara 18 yana buga wa ƙungiyar wasa. Tsohon ɗan ƙwallon tawagar Sifaniya, mai taka leda daga tsakiya ya yi wa Barca karawa 718 – shi ne na uku a yawan buga wasa a ƙungiyar. Ɗan ƙwallon ya lashe kyautuka da yawa a Barca ciki har da ɗaukar La Liga takwas da Copa del Rey bakwai da Spanish Super Cup bakwai da Champions League uku. Busquets ya koma Barca a 2005 a matakin matashin ɗan awallo daga nan har ya koma babbar ƙungiyar, inda…
Read More
Mahaifiyar marubuci Ayuba M. Ɗanzaki ta kwanta dama

Mahaifiyar marubuci Ayuba M. Ɗanzaki ta kwanta dama

Daga ADAMU YUSUF INDABO a Kano Ayuba Muhammad Ɗanzaki dai fitaccen marubucin hikaya ne da yake yin rubutunsa cikin harshen Hausa na zube da kuma rubutacciyar waƙa musamman ta yabo ga Fiyayyan Halitta (S.A.W.). Ya wallafa littafai da dama, waɗanda suka haɗa da 'Shingen Ƙauna, Adawar So, Rayuwar Bilkisu, Fadar So, Kurman Hisabi' da dai sauransu. Mahaifiyar ta marubuci Ayuba Muhammad Ɗanzaki dai wato Hajiya Salamatu Garba Zakirai, wadda aka fi sani da Hajiya Talatuwa Ɗanzaki ta rasu ne ranar da ta gabata daidai da 4/5/2023, da ƙarfe Sha Biyu na dare (12:00AM). Cikin tattaunawar da wakilinmu ya yi da…
Read More
A ganina ƙungiyoyin marubuta ba su da wani tasiri – Hafsat Rano

A ganina ƙungiyoyin marubuta ba su da wani tasiri – Hafsat Rano

"Akwai bambanci tsakanin rubutun fim da na zube" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Rubutu babbar baiwa ce da ba kowa ke samunta ba, sai wasu ƙalilan daga cikin mutane. Ko su ma marubutan za ka tarar kowa da irin hikima ko basirar da yake da ita wajen zalaƙar sarrafa harshe da fikirar jawo hankalin mai karatu, da riƙe tunanin sa har sai ya kammala karanta saƙon da ake son isar masa. Hafsat Kabir Umar da aka fi sani da Hafsat Rano daga Jihar Kano na daga cikin irin marubuta ýan baiwa da Allah ya yi wannan babbar kyauta. Tun tana yi…
Read More