Editor

9513 Posts
Kotu ta ɗage shari’ar su Atiku zuwa 18 ga Mayu

Kotu ta ɗage shari’ar su Atiku zuwa 18 ga Mayu

Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓe ta ɗage sauraren shari'ar ƙarar da jam'iyyar PDP da ɗan takararta na shugabancin ƙasa, Atiku Abubakar, suka shigar kan nasarar da Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, ya samu yayin babban zaɓen da ya gudana. Yayin zaman kotun a ranar Alhamis ƙarƙashin jagorancin Mai Shari'a Haruna Tsammani, Kotun ta ɗage ci gaba da sararen ƙarar ya zuwa ranar 18 ga Mayu, 2023. Ƙorafin da suka shigar kotu mai lamba CA/PEPC/05/2023, PDP da Atiku na ƙalubalantar bayyana Tinubu da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta yi a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugabancin ƙasa. Manhaja ta rawaito cewa,…
Read More
Sauraren Ƙararrakin Zaɓe: Atiku Abubakar ya halarci zaman kotu

Sauraren Ƙararrakin Zaɓe: Atiku Abubakar ya halarci zaman kotu

Ɗan takarar Shugaban Ƙasa ƙarƙashin Jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya halarci zaman shari'ar da Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓe ki yi a Abuja a wannan Alhamis ɗin. Atiku ya halarci Kotun ne domin jin yadda za ta kaya kan ƙarar da ya shigar inda yake ƙalubalantar nasarar da ɗan takarar shugabancin ƙasa na Jam'iyyar APC, Bola Tinubu, ya samu a babban zaɓen da ya gudana. Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasar shi ne ya zo na biyu a babban zaɓen da aka yi ran 25 ga Fabrairu, yayin da Peter Obi na Jam'iyyar Labour ya zo na uku. Atiku yana zargin an tafka…
Read More
Buhari zai kinkimo bashin N368.7bn daga Bankin Duniya

Buhari zai kinkimo bashin N368.7bn daga Bankin Duniya

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya buƙaci Majalisar Dattawa da ta amince masa ya kinkimo bashin Dala miliyan 800 kwatankwacin Naira biliyan 368.7 daga Bankin Duniya. Buƙatar Shugaban na ƙunshe ne a wata wasiƙa wadda Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya karanto a zauren Majalisar yayin zamanta a rabar Laraba. Buhari ya ce so yake ya yi amfani da kuɗaɗen wajen shirin kyautata rayuwar 'yan ƙasa. Ya ce muddin aka amince masa ya ki kimo bashin, zai raba wa 'yan Nijeriya mutum miliyan 60 Naira dubu biyar-biyar (N5,000) kowannensu don rage raɗaɗin talauci. “Majalisar Zartarwa ta Ƙasa ta amince da…
Read More
Sanadin sakin matar aure saboda ashana na buɗe gidauniyar tallafin mata – Rabiatu Sa’idu

Sanadin sakin matar aure saboda ashana na buɗe gidauniyar tallafin mata – Rabiatu Sa’idu

“Sarautun gargajiya kusan 22 na ke riƙe da su” Daga ABUBAKAR M. TAHEER  Hajiya Rabi'atu Umar Sa'idu mace ce mai matuƙar tausayi ga masu rauni. Ita ce mai gidauniyar Sarauniyar Charity Foundation, wanda ta ke ƙoƙari wajen tallafa wa marasa ƙarfi da marayu a kusan ko'ina a faɗin ƙasar nan. Haka kuma ba ta tsaya anan ba, inda ta ke amfani da dukiyarta wajen gina rijiyoyi ruwa a ƙauyukan da ke fama da matsanancin rashin ruwa. Mace ce da ya kamata ta zama allon kwaikwayon duk wani da yake da tausayi kuma yake da ɗan abin hannunshi.  A cikin wannan…
Read More
EFCC ta tsare tsohon Ministan Lantarki, Sale Mamman kan zargin karkatar da N22bn

EFCC ta tsare tsohon Ministan Lantarki, Sale Mamman kan zargin karkatar da N22bn

Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arziki Zagon Ƙasa da Zambar Kuɗaɗe (EFCC), ta tsare tsohon Ministan Lantarki, Sale Mamman, kan zargin nasabarsa da almundahanar Naira biliyan 22. An tsare Mamman ne da safiyar ranar Laraba. Mamman ya riƙe muƙamin Ministan Lantarki a ƙarƙashin gwamnatin Muhammadu Buhari daga 2019 zuwa 2021. Tsare Mamman ya taso ne sakamakon binciken da hukumar ke yi kan batun aiwatar da wasu ayyuka ƙarƙashin Ma'aikatar Lantarki. Ana zargin Mamman da haɗa baki da jami'an Ma'aikatar masu kula da sashen kuɗi na ayyukan lantarki a Zungeru da Mambilla wajen karkatar da kuɗi Naira biliyan 22 wanda…
Read More
Kotu ta haramta wa NBC ƙaƙaba wa gidajen rediyo da talabijin tara

Kotu ta haramta wa NBC ƙaƙaba wa gidajen rediyo da talabijin tara

Babbar Kotu a Abuja ta ce, daga yanzu ta haramta wa Hukumar Kula da Gidajen Rediyo da Talabijin ta Ƙasa (NBC), ta ci tarar gidajen rediyo da talabijin a faɗin ƙasa. Kotun ta yanke wannan hukuncin ne a zaman shari’ar da ta yi a ranar Laraba. Kazalika, da yake yanke huncin, Alƙalin kotun, Mai Shari’a James Omotosho, ya yi watsi da tarar N500,000 da NBC ta yanka wa tashohi 45 ran 1 ga Maris, 2019 a matsayin horo kan aikata ba daidai ba. Bugu da ƙari, Alƙalin ya ce Dokar NBC da ta bai wa hukumar damar yanka tara, ta…
Read More
Tsarabar taron marubutan Hausa a Kano

Tsarabar taron marubutan Hausa a Kano

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Allah cikin ikonSa Ya bani damar halartar Babban Taron Marubutan Hausa da aka gudanar a birnin Kano, wanda ya samu halartar marubuta, manazarta, malaman jami'o'i da 'yan jarida da dama daga sassan Nijeriya daban-daban. An shirya taron ne da nufin samar da muhallin da tsofaffi da fitattun marubuta za su gana da matasan marubuta na yanar gizo, da kuma tattauna hanyoyin da za a bi a tallafawa ƙananan marubuta masu ƙwazo da ke da burin shiga sahun manyan marubuta, don ganin sun samu ƙwarewar da suke buƙata a fagen rubuce rubucen fim, labaran hikaya, da Gasar…
Read More
NAGARI NA KOWA: Tasirin Muhammad Nami a Hukumar Tara Kuɗaɗen Haraji ta Ƙasa (FIRS)

NAGARI NA KOWA: Tasirin Muhammad Nami a Hukumar Tara Kuɗaɗen Haraji ta Ƙasa (FIRS)

Daga NKEM PRECIOUS(Fassarar Abubakar Salisu) Lambobin yabo guda biyu da Shugaban Hukumar Tara Kuɗaɗen Haraji ta Ƙasa (FIRS) ya samu a wurare biyu kwanan nan, sun nuna irin muhimmaci da ƙwazon da ya ke da shi da kuma jajircewa kan aikin da aka ɗora masa na tattara kuɗaɗen haraji. Lambar yabo ta farko ita ce Kyautar Gwarzon Cibiyar Akantoci ta Najeriya (ICAN), wadda aka ba shi a ranar 6 Ga Mayu, 2023. Nagarta da sanin ya kamata ya sa shi kuma Nami ya sadaukar da wannan muhimmiyar lambar yabo da ya samu ga dukkan 'yan ajin su da su ka…
Read More
Rukuni na bakwai na maƙalallun ‘yan Nijeriya a Sudan ya isa Abuja

Rukuni na bakwai na maƙalallun ‘yan Nijeriya a Sudan ya isa Abuja

A halin da ake ciki, kashi na bakwai na jigilar 'yan Nijeriyar da suka maƙale a Sudan ya isa Babban Filin Jirgin Saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja. Manhaja ta kalato cewar, rukunin mai ɗauke da mutum 136, ya isa Abuja ne da misalin ƙarfe 9:30 na safe a ranar Laraba. Hukumar Bada Agajin Gaggawa (NEMA) ta ce wannan shi ne jirgi na 11 da aka yi jigilar maƙalallun 'yan Nijeriya a Sudan zuwa ƙasarsu. Ta ƙara da cewa, tun bayan ɓarkewar rikici a ƙasar Sudan, baki ɗaya an yi nasarar kwaso mutum 2,002 da ya ƙunsje maza da mata,…
Read More
Gogewa a aikin jarida shi ne kada mai sauraro ya gane inda aka karkata

Gogewa a aikin jarida shi ne kada mai sauraro ya gane inda aka karkata

Daga TIJJANI MUHAMMAD MUSA Zan yi ɗan tsokaci a kan wannan maudu'in don na nusar da ma'aikatan jarida na yanzu ko Allah SWT zai sa wasu a cikinsu su ɗauki darasi in sha Allah. Yan jaridunmu na wannan zamani da yawa sukan kasa bambance tsakanin nuna ra'ayinsu a karan kansu da matsayar gidajen jaridun da suke yi wa aiki sannan kuma su san yadda ya kamace su su gudanar da aiki a matsayinsu na 'yan jarida. Alhali kuwa kowanne tafiyarsa daban. Bari in ba da ɗan misali da harkar siyasa tunda yanzu haka a cikin damunarta muke tsamo-tsamo. Za ta…
Read More