Editor

9513 Posts
‘Yan sanda sun kashe ‘yan bindiga uku a Zamfara

‘Yan sanda sun kashe ‘yan bindiga uku a Zamfara

’Yan sanda a Jihar Zamfara, sun kashe wasu ’yan bindiga uku a tsakanin ƙananan hukumomin Tsafe da Bakura a jihar. Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Mohammed Bunu, shi ne ya bayyana haka a ranar Laraba yayin taron manema labarai da ya shirya a Gusau, babban birnin jihar. Ya ce sakamakon musayar wutar da aka yi tsakanin jami’ansu da ’yan bindigar a ƙauyen Gidan Giye cikin Qaramar Hukumar Tsafe, an kashe ’yan bindiga biyu tare da ƙwace bindigogi biyu ciki har da ƙirar AK-49. “A ranar 3 ga Mayu, 2023 da misalin ƙarfe 2:30 na rana, tawagar ’yan sanda da ke sintiri…
Read More
Fara fiffiken tururuwa: Game da Sarkin Kano na 14

Fara fiffiken tururuwa: Game da Sarkin Kano na 14

Daga ALIYU AMMANI Ba yau aka fara tuɓe sarakuna ba a wannan yanki namu na arewacin Nijeriya. Turawan Mulkin Mallaka sun tumɓuke sarakuna da dama a farkon zuwansu, suka kai su Lokoja 'exile'. Bayan samun 'yancin kai a shekarar 1960, gwamnatin Arewa ta warware rawanin Sarkin Kano Sanusi ta tura shi 'exile' Azare. Daga baya gwamnatin Kano ta dawo da shi Wudil.  Da wayonmu, mun ga an sauke Sarkin Muri, Sarkin Musulmi Dasuƙi da Sarkin Gwandu Jokolo. Duk cikin sarakunan da aka sauke daga gadon sarauta tun farkon zuwan turawa ba mu taɓa gani ko jin abubuwan da muke gani da…
Read More
Mutum 15 sun mutu a hatsarin jirgin ruwa a Sakkwato

Mutum 15 sun mutu a hatsarin jirgin ruwa a Sakkwato

Aƙalla 'yan mata 15 aka rawaito sun riga mu gidan gaskiya sakamakon hatsarin jirgin ruwa da ya ritsa da su a ƙauyen Dandeji cikin Ƙaramar Hukumar Shagari a Jihar Sakkwato. Majiyarmu ta ce marigayan, ajali ya cim musu ne a hanyarsu ta zuwa yin itace a wani daji da ke kusa inda jirgin ruwa ya kefe da su da safiyar ranar Talata. A cewar ganau, sama da 'yan mata 40 ke cikin jirgin ruwan da hatsarin ya shafa. Wani mazaunin yankin mai suna Muhammad Ibrahim, ya ce, an gano gwawarwaki 15, yayin da masu aikin ceto na ci gaba da…
Read More
Ya ɗirka wa ’yar shekara 13 da su ke haya a gidansa ciki

Ya ɗirka wa ’yar shekara 13 da su ke haya a gidansa ciki

Ana zargin wani magidanci a Kano da ɗirka wa wata ’yar shekara 13, wadda mahaifiyarta ke zaune a gidansa ciki. A wata tattaunawarta da manema labarai, yarinyar ta ce tun da farko mutumin ya yi mata barazanar yanka ta da kuma tashin su daga gidansa ko su biya shi kuɗin haya, matuƙar ta faɗa wa mahaifiyarta cewa yana lalata da ita. Yarinyar ta ce yanzu haka sun je asibiti saboda cikinta ya tsufa, amma likitoci sun ce ba za ta iya haihuwa da kanta ba, sai an yi mata aiki, don haka sai sun kawo jinin da za a qara…
Read More
Ta kashe ɗanta ta dafa kansa

Ta kashe ɗanta ta dafa kansa

Wata mata ta kashe ɗanta mai shekara biyar, ta daddatsa sassan jikinsa sannan ta dafa naman kansa ta ci. ’Yan sanda sun cafke matar mai shekara 29 ne bayan sun gano sassan jikin ɗan nata a cikin bokiti a gidanta da ke birnin Faqus a lardin Ash Sharqiyah na ƙasar Masar. Kafar yaɗa labarai ta Masrawy da ke ƙasar ta ruwaito cewa, maƙure yaron matar ta yi, ta kashe shi sannan ta daddatsa sasan jikinsa. An ruwaito cewa, kawon mamacin ne ya faro gano abin da ya faru a lokacin da ya ziyarci gidanta, sannan ya sanar da jami’an tsaro.…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Kotun Ƙoli ta tabbatar da Adeleke a matsayin Gwamnan Osun

Da Ɗumi-ɗumi: Kotun Ƙoli ta tabbatar da Adeleke a matsayin Gwamnan Osun

Kotun Ƙoli ta yi watsi da ƙarar da Adegboyega Oyetola na Jam'iyyar APC ya ɗaukaka inda yake ƙalubalantar nasarar da Ademola Adeleke na Jam'iyyar PDP ya samu a matsayin Gwamnan Jihar Osun. Da yake karanto hukuncin yayin zaman kotun a ranar Talata, Mai Shari'a Emmanuel Agim ya tabbatar da hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yanke na cewa Adeleke shi ne wanda ya yi nasara a zaɓen na Osun. Kotun Ƙolin ta ce mai ƙara ya gaza gabatar wa kotun gamsassun hujjoji kan zargin da ya yi cewa an zuba ƙuri'a wuce kima a zaɓen gwamnan jihar Osun da ya…
Read More
Soyayyata ga Kwankwaso ta sa ni sauya akalar waƙoƙina zuwa na siyasa – Tijjani Gandu

Soyayyata ga Kwankwaso ta sa ni sauya akalar waƙoƙina zuwa na siyasa – Tijjani Gandu

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Ga duk mai bibiyar harkokin siyasa a Nijeriya, musamman abin da ya shafi ɓangaren waƙoƙi, ba zai rasa jin labarin Tijjani Gandu ko waƙoƙinsa, musamman waɗanda yake yi wa jagoran Kwankwasiyya Injiniya Rabi'u Musa Kwankwaso, ko kuma Bakandamiyarsa ta Abba Gida Gida, da ya yi wa zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf. Ahmad Tijjani Hussaini Gandu kamar yadda cikakken sunansa yake, fitaccen mawaƙin siyasa ne, da ake jin amonsa a duniya ba a Jihar Kano kaɗai ba, saboda salon waƙoƙinsa da yadda yake kwarzanta jagoransa kuma madugun Kwankwasiyya, wanda ya ce yana alfahari da…
Read More
Aure ya wuce maganar ɗaukar nauyi kawai

Aure ya wuce maganar ɗaukar nauyi kawai

Daga AMINA YUSUFU ALI Barkanmu da sake haɗuwa a wani sabon mako a jaridarmu mai farin jini ta Blueprint Manhaja. Maudu'inmu na wannan mako shi ne maganar ɗaukar nauyin iyali da yadda ya shafi zamantakewar aure. A sha karatu lafiya. Ma'anar ɗaukar nauyin iyali Ɗaukar nauyin iyali yana nufin ɗaukar nauyin da maza suke yi na matan da suka aura da yaran da suka haifa ta fuskar sha'anin kuɗi. Ɗaukar nauyi ya haɗa da ciyarwa, shayarwa, tufatarwa, kula da lafiya, ilimi da sauran madangantansu. A al'adar Bahaushe da addinin musulunci, nauyi ne a kan kowanne magidanci ya kula da waɗancan…
Read More
An cafke masu ƙwacen waya da ƙauraye 74 a Katsina

An cafke masu ƙwacen waya da ƙauraye 74 a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Rundunar 'Yan Sanda ta Jihar Katsina, ta kama wasu masu aikata miyagun laifuka a jihar da suka haɗa da masu ƙwacen waya da ƙauraye da masu safarar miyagun ƙwayoyi da mata masu zaman kansu da kuma masu ba wa 'yan ta'adda bayanan sirri da yawan su ya kai 74. Kakakin rundunar, CSP Gambo Isah ne ya bayyana hakan a Hedikwatar rundunar da ke Katsina babban birnin jihar, a lokacin da yake gabatar da su ga manema labarai. Kakakin rundunar ya bayyana cewar, an kama waɗanda ake zargin ne bayan wani samame da rundunar ta kai,…
Read More
Tarihin Hawan Sallah a Ƙasar Hausa (II)

Tarihin Hawan Sallah a Ƙasar Hausa (II)

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A yau za mu cigaba da kawo tarihin hawan sallah na masarauto daban-daban daga inda muka tsaya a makon da ya gabata. Masarautar Gwandu: Hawan Sallah a Masarautar Gwandu ya samo asali da daɗewa tun zamanin sarakuna kuma an fara ne bayan Jihadi kamar yadda Alhaji Ibrahim Baisat, Galadiman Gwandu ya shaida. Yayin hawan idi da ƙaramar sallah, uwayen ƙasa na ƙasar Gwandu 15 duk suna zuwa da dawakai 30 ko 40 wasu ma 50. A cewarsa, ana gudanar da hawan farko bayan sallar idi. "Idan aka (idar) da idi, ana fara kiɗi, lokacin kakaki su…
Read More