Editor

9513 Posts
APC ta yi ra’ayin Akpabio da Barau su jaigoranci Majalisar Ƙasa

APC ta yi ra’ayin Akpabio da Barau su jaigoranci Majalisar Ƙasa

Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa na Jam'iyyar APC (NWC) ya sannar da bin tsarin karɓa-karɓa dangane da shugabancin Majalisar Taraya zubi na 10. A cewar sanarwar da jam'iyyar ta fitar a ranar Litinin ta bakin Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa, Felix Morka, tsarin karɓa-karɓar da jami'yyar ta shirya yin amfani da shi ya ƙunshi: Shugaban Majalisar Dattawa - Kudu maso Kudu - Sanata Godswill Akpabio (Akwa Ibom), Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa – Arewa maso Yamma - Sanata Barau Jubrin (Kano). Sauran su ne; Shugaban Majalisar Wakilai, Arewa maso Yamma – Hon. Abass Tajudeen (Kaduna), Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai Deputy Kudu maso…
Read More
‘Yan bindiga sun ɗauke amaryar da yaran Sarki a Kaduna

‘Yan bindiga sun ɗauke amaryar da yaran Sarki a Kaduna

Wasu da ake zargin 'yan fashin daji ne sun kai hari fadar Sarkin Kagarko, Alhaji Sa'ad Abubakar, da ke yankin Kudancin Kaduna inda suka yi awon gaba da ahalin gidan da dama. Waɗanda 'yan bindigar suka sace sun haɗa da yara guda tara da jikoki da dama haɗi da wasu daga cikin garin. Majiyarmu ta ce maharan sun kai harin ne da misalin ƙarfe 11:15 na dare a ranar Lahadi inda suka tafi kai tsaye faɗar sarkin. A cewar majiyar, “Sun ɗauke amaryar sarki tare da yara tara da kuma jikoki, amma amaryar ta samu ta kuɓuce ta dawo gida."…
Read More
Sauraren Ƙararrakin Zaɓe: Kotu ta ɗage zamanta zuwa ranar Talata

Sauraren Ƙararrakin Zaɓe: Kotu ta ɗage zamanta zuwa ranar Talata

Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa mai zamanta a Abuja, ta ɗage zamanta zuwa ranar Talata. Yayin zamanta na gaba, ana sa ran Kotun ta saurari ƙorafin da Atiku Abubakar da jam'iyyar APM suka shigar ne game da zaɓen na Shugaban Ƙasa. Sannan ta saurari ƙararrakin da Jam'iyyar Labour da APP da kuma Peter Obi suka shigar a ranar Laraba. Duka ƙararrakin da aka shigar suna ƙalubalantar sakamakon zaɓen Shugaban Ƙasa da ya gudana ne a ranar a ranar 25 ga Fabraru. Zaɓen da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta tabbatar da Bola Tinubu ma Jam'iyyar APC a matsayin wanda…
Read More
Gwamnatin Tarayya ta ƙara harajin shigo da shinkafa da alkama

Gwamnatin Tarayya ta ƙara harajin shigo da shinkafa da alkama

Daga AMINA YUSUF ALI Gwamnatin tarayya ta ba da sanarwar sake waiwayar harajin shigo da kayan waje (IAT) a matsayin wani ɓangare na tsara dokar harajin Gamayyar kasuwanci ta Afirka (ECOWAS) (CET) 2022-2026, wannan ya sa ta yi ƙari a kan haraji ga jasashe masu shigo da shinkafa, alkama, barasa, da sauran hajoji guda 189. Wannan sabon ƙarin harajin na shekarar 2023, ya ɗaga harajin kan shinkafa da ta haura kilo 5, ko mai yawa amma a rarrabe zuwa kilo 5, to za a biya harajin kaso 60, wanda kaso 50 ake biya a baya. Hakazalika, shigo da alkama ko…
Read More
Duniya rawar ‘yammata: BUA ya kere arzikin Ɗangote a watan Afrilun bana

Duniya rawar ‘yammata: BUA ya kere arzikin Ɗangote a watan Afrilun bana

Daga AMINA YUSUF ALI AbdulSamad Rabiu, hamshaƙin ɗan kasuwa a Nijeriya, kuma mutum na biyu ma fi dukiya a ƙasar ya buga tarihi a watan Afrilun shekarar bana ta 2023 a cewar sakamakon binciken kwanan nan da Forbes suka gudanar. Ƙarfin arzikin na Abdulsamad Rabi'u ya yi tashin gwauron zabi zuwa Dalar Amurla biliyan $8.6 a ƙarshe watan Afrilun na bana. Wato dai an samu ƙaruwar maƙudan kuɗi har Dalar Amurka biliyan $300 wato kwatankwacin Naira biliyan 138.14 musamman idan aka kwatanta dukiyarsa da dalar Amurka biliyan $8.3 da take a 1 ga watan Afrilu, 2023. Wannan ya nuna cewa,…
Read More
Ƙungiya ta yi gargaɗi masu neman kawo cikas wajen rantsar da Tinubu

Ƙungiya ta yi gargaɗi masu neman kawo cikas wajen rantsar da Tinubu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Wata ƙungiya mai suna 'White Witches and Wizards Association of Nigeria', ta yi gargaɗi game da yunƙurin kawo cikas a bikin rantsar da zaɓaɓɓen shugaban aasa, Bola Tinubu, a ranar 29 ga Mayu, 2023. Da yake zantawa da manema labarai bayan taron da suka yi a Kalaba, babban birnin jihar Kuros Ribas, mai magana da yawun ƙungiyar, Dokta Okhue Oboi, ya yi ikirari gabanin dawowarsa daga hutu a Turai, ƙungiyar ta bai wa zaɓaɓɓen shugaban kariya domin tabbatar da cewa babu wani mummunan abu da ya same shi. Oboi ya ce, bayan an yi nazari sosai…
Read More
NDYC ta gargaɗi matasan Neja-Delta kan tashin hankali

NDYC ta gargaɗi matasan Neja-Delta kan tashin hankali

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ƙungiyar Matasan yankin Neja Delta (NDYC) a ranar Talata ta buƙaci matasan da su guji ayyukan da za su iya lalata zaman lafiya da ake samu a yankin. Shugaban hukumar na ƙasa, Abido Jator ne ya yi wannan kiran a Abuja, yayin da yake roƙon matasan da ke ƙoƙarin kada hankali da su janye zanga-zangar da suke shirin yi na nuna adawa da hukumar raya yankin Neja Delta (NDDC). Matasan sun zargi hukumar ta NDDC da cewa ba su ɗauke su tare da kuma kasa biyan buƙatunsu. Jator ya ce, ƙungiyarsa ta daƙile zanga-zangar da matasan…
Read More
Illar fyaɗe

Illar fyaɗe

Daga AISHA ASAS Masu karatu barkanmu da sake kasancewa a shafin iyali na jaridar Manhaja, fatan Allah Ya albarkanci zuri'armu, Ya ba mu zaman lafiya. Kafin komai zan so mu fara da bayyana ma'anar kalmar fyaɗe kafin mu kai ga tattauna matsalolin da ake fuskata bayan fyaɗen. Fyaɗe wani nau'in cin zarafi ne ta ɓangaren jima'i, amfani da ƙarfi yayin kusantar mace ko namiji, ma'ana yi ba da amincewar abokin tarayya ba. Idan aka ce fyaɗe, hankalin mutane ya fi tafiya ne ga mata, a ganin su mata ne kawai ake yi wa cin zarafi ta ɓangaren fyaɗe. Ko kaɗan…
Read More
Labaran ƙarya na barazana ga ‘yancin faɗin albarkacin baki – Ahmed Maiyaki

Labaran ƙarya na barazana ga ‘yancin faɗin albarkacin baki – Ahmed Maiyaki

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Babban Jami’in Yaɗa Labarai na Cigaban Ƙungiyar Fafutukar Neman ’Yancin ’Yan Jarida, Malam Ahmed Maiyaki, ya bayyana damuwarsa kan ƙalubalen da ake fuskanta na ’yancin aikin jarida a kasar nan. Maiyaki ya bayyana "labarai na ƙarya" da kuma bayanan ƙarya a matsayin wani ɓangare da ke barazana ga 'yancin faɗin albarkacin baki a matsayin kan gaba ga sauran 'yancin ɗan adam. Shugaban na MDINIGERIA a cikin wata sanarwa da aka raba wa manema labarai a Kaduna a ranar Larabar da ta gabata ya bayyana cewa, taken ranar ’yan jarida ta duniya ta 2023: ‘Shaping a Future…
Read More