Editor

9513 Posts
MAVIN ta buƙaci a daina nuna wariya ga masu nakasa

MAVIN ta buƙaci a daina nuna wariya ga masu nakasa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A yayin da ake gudanar da bikin zagayowar ranar nakasassu, ƙungiyar Musulmi Masu Nakasassu ta Nijeriya (MAVIN) ta buƙaci zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu da zaɓaɓɓun gwamnoni da su samar da ayyukan yi ga nakasassu a faɗin tarayyar ƙasar nan. A cikin wata sanarwa, shugaban ƙungiyar, AbdulWasi Salaudeen, ya ce nakasassun Nijeriya sun cancanci a yi bikin. Ya baygana cewa, duk da rashin daidaito, har yanzu nakasassu su na cika sashinsu na ayyuka daban-daban. Ya ƙara da cewa, “Dukkanmu mun cancanci yabo domin mun yi nasarar tattara kanmu waje guda, lokacin da kuma bayan zaɓe cikin…
Read More
Tun da Hudu ya haɗu da ’yan sanda…

Tun da Hudu ya haɗu da ’yan sanda…

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA A ƙarshe dai, rundunar 'yan sandan Nijeriya ta ba da labarin cewa ta kama kwamishinan zaɓe na jihar Adamawa Barista Hudu Yunusa Ari da tun farko hukumar zaɓen INEC a taƙaice ta dakatar da shi don ayyana sakamakon zaɓe ba tare da hurumin yin hakan ba. Yayin da a ka ɗauka za a ji Ari ya miƙa kansa ga rundunar ko kuma a ce rundunar ta gayyace shi don amsa tambayoyi, sai kwatsam sanarwa daga kakakin rundunar Olumuyiwa Adejobi ta ce 'yan sanda sun kama Hudu Ari don gudanar da bincike a kan sa da ma…
Read More
‘Yan sanda sun kama mutum biyu da suka birne tsoho da ransa a Jihar Binuwai

‘Yan sanda sun kama mutum biyu da suka birne tsoho da ransa a Jihar Binuwai

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Rundunar ‘yan sandan jihar Benuwai sun kama wasu matasa biyu da suka kashe wani tsoho Ihwakaa a ƙauyen Ikyve dake Ƙaramar Hukumar Konshisha. Ihwakaa ya gamu da ajalinsa bayan matasan ƙauyen sun zargesa da tsafi. Wani mazaunin ƙauyen da baya so a faɗin sunansa ya ce rikicin ya somo ne bayan zarginsa da kashe ɗan Ihwakaa mai suna Henry, sirikarsa da jikarsa jaririyar a rana ɗaya. Mazaunin ya ce ba tun yanzu ba mutanen ƙauyen na zargin tsohon da yin amfani da ruwa a ƙauyen domin yin tsafi da mutane. “A dalilin haka ya…
Read More
TinT da IBP sun horas da mutum 34 batun biyan haraji a Kano

TinT da IBP sun horas da mutum 34 batun biyan haraji a Kano

Daga RABI'U SANUSI a Kano Ƙungiyar bibiyar haraji da akafi sani da Follow Taxes ko T in T tare da haɗin gwii IBP ta shirya mlwa mata da maza bita a kan abin da ya shafi haraji a jihar Kano. Wannan taro na zuwa ne adaidai lokacin da mafi yawan jama'a ke kokawa da irin ƙalubalen da ke ci wa al'umma tuwo a ƙwarya kan batun haraji a jihar Kano da ma ƙasa baki ɗaya. Da yake yi wa mahalarta taron ƙarin bayani, ɗaya daga cikin masana dangane da batun haraji a jihar Kano kuma Shugaban kungiyar wanzar da zaman…
Read More
Raɗɗa zai tantace ma’aikatan gwamnati bayan an rantsar da shi

Raɗɗa zai tantace ma’aikatan gwamnati bayan an rantsar da shi

Daga UMAR GARBA a Katsina Zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Katsina, Dakta Dikko Umaru Raɗɗa, ya bayyana shirin gwamnatinsa na gudanar da tantance ma’aikata a ɗaukacin ƙananan hukumomin jihar 34, bayan rantsar da shi a matsayin gwamna a ranar 29 ga watan Mayun 2023. Raɗɗa wanda ya gabatar da tambayoyi a lokacin wani shirin talabijin, ya nuna rashin jin daɗinsa da wasu ma’aikatan duk da cewa suna cikin tsarin biyan albashi na gwamnati har yanzu ba su da wani tasiri wajen bayar da hidima. "Abin da muke so mu yi shi ne, tantance ma’aikata sosai idan muka zo don tabbatar da cewa…
Read More
2023: An tsinci gawar ɗan takarar gwamna cikin daji ta fara ruvewa

2023: An tsinci gawar ɗan takarar gwamna cikin daji ta fara ruvewa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja An tsinci gawar tsohon ɗan takarar gwamna a Jam’iyyar APGA a Jihar Enugu cikin daji. Mamacin mai suna Dons Ude, ya fito takarar zaɓen fidda gwani a zaɓen gwamnan jihar na 2023 da aka kammala cikin Maris. An tsinci gawarsa ce bayan an bayyana sanarwar vacewarsa tun a ranar Asabar. An ce an tsinci gawar Ude daidai Kwanar Mil 9 da ke Ƙaramar Hukumar Udi, cikin Jihar Enugu. An kuma tabbatar da cewa ita ma motarsa wadda ya ke ciki daga lokacin da aka neme shi aka rasa, an ganota. Dama kuma tun da…
Read More
Haaland ya kafa tarihin yawan jefa ƙwallo a gasar Firimiyar Ingila

Haaland ya kafa tarihin yawan jefa ƙwallo a gasar Firimiyar Ingila

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ɗan wasan gaba na Ƙungiyar Manchester City Erling Haaland ya kafa tarihin yawan cin ƙwallaye a gasar Firimiyar Ingila, inda a wannan kaka ya zura ƙwallaye 35. Ɗan wasan wanda ɗan asalin ƙasar Norway ne, ya zarce yawan qwallaye 34 da ’yan wasa Alan Shearer da kuma Andrew Cole suka ci a gasar. Bayan tashi daga karawar da su ka yi da West Ham a gasar Firimiyar Ingila, 'yan wasan City sun jeru don jinjina wa ɗan wasan bisa bajintar da ya yi. Haka nan ƙungiyar ta Manchester City ta samu nasarar jefa ƙwallo ta dubu…
Read More
Majalisar Dokoki: A karon farko jam’iyyun adawa na shirin kafa shugabanci

Majalisar Dokoki: A karon farko jam’iyyun adawa na shirin kafa shugabanci

*Yadda fafatawar neman shugabancin Majalisar Dokokin Nijeriya yake ƙamari Daga MAHDI M. MUHAMMAD Makonni ƙalilan kafin a rantsar da Majalisar Dokokin Nijeriya ta 10, a karon farko jam’iyyun adawa a ƙasar su na ƙara samun ƙwarin gwiwar yin yunƙurin naɗa shugabanci a majalisar, musamman ma Majalisar Wakilai, wacce yawansu ya ɗari na jam’iyya mai mulki, wato APC. To, sai dai kuma ita ma APC ɗin tana cigaba da jan ɗamara kan sai ta ga abinda ya ture wa buzu naɗi. A karon farko dai a tarihin Nijeriya an zaɓi mambobin jam’iyyun adawa har sun fi na jam’iyya mai mulki bayan…
Read More
Batun bautar da ƙananan yara a Nijeriya

Batun bautar da ƙananan yara a Nijeriya

Akwai wani al'amari mai matuƙar tayar da hankali da ban tausayi kan yadda ake amfani da yara masu ƙananan shekaru maza da mata don yin aiki ko bauta a gidaje da sauran wurare da suka haɗa da shaguna, otel-otel, wuraren kwana na manyan makarantu ko ɗakunan kwanan ɗalibai a jami’o’i. Akasarin yaran ’yan ƙasa da shekaru 15 ne kuma ana ɗaukarsu ne da nufin yin aikace-aikacen da suka haɗa da shara, wanke-wanke, wanki, goge-goge, ɗebo ruwa da rainon jarirai da kula da yayayyun yara da makamantansu. Mafi yawan yaran ana kawo su cikin birni daga ƙauyuka lokaci zuwa lokaci, ta…
Read More
N-YED ta tallafa wa marayu da kayan masurufi a Kano

N-YED ta tallafa wa marayu da kayan masurufi a Kano

Daga RABI'U SANUSI a Kano A ranar Lahadin da ta gabata ne ƙungiyar tallafa wa matasa da marayu da aka fi sani da N-YED ƙarƙashin jagorancin Kwamared Abdulsalam Haruna, ta gabatarwa da marayun dake gidan yara na Ƙaramar Hukumar Nasarawa Tallafin kayayyaki masu ɗumbin yawa dan tabbatar masu da irin gatan da suke da shi. Da yake yi wa manema labarai jawabi yayin taron, Shugaban ƙungiyar na N-YED, Kwamared Abdulsalam Haruna, ya ce lokacin da ya fara tunanin kafa wannan ƙungiya bai tunanin za ta zama haka ba, ya ce duk abin da mutum ya sa niyya a rayuwarsa in…
Read More