Editor

9513 Posts
Almudahanar N2.1bn: Kotun Ɗaukaka Ƙara ta tabbatar da hukuncin da aka yanke wa Maina

Almudahanar N2.1bn: Kotun Ɗaukaka Ƙara ta tabbatar da hukuncin da aka yanke wa Maina

*Maina zai shafe shekara takwas a gidan kaso Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja ta tabbatar da hukuncin ɗaurin shekara takwas da aka yanke wa tsohon Shugaban Kwamitin Kula da Fansho, Abdulrasheed Maina kan yin sama-da-faɗi da kuɗaɗen fansho Naira biliyan 2.1. Alƙalan da suka saurari shari'ar, baki ɗaya su ukun sun yi ittifaƙi kan tabbatar da hukuncin da aka yanke wa Maina kamar yadda Mai Shari'a Okon Abang ya karanto. Jagoran alƙalan, Elfreda Williams-Daudu, ya tabbatar da hukuncin da Babbar Kotu ta yanke wa Maina ɗin wanda a kan haka shi Maina ya ɗaukaka ƙara. Alƙalin ya ce an…
Read More
Ingila ta yi sabon Sarki bayan shekaru 70

Ingila ta yi sabon Sarki bayan shekaru 70

*Sarki Charles na III ya gaji mahaifiyarsa Rahotanni daga ƙasar Ingila sun ce, an gudanar da gagarumin bikin naɗin Sarki Charles na III a wannan Asabar, inda Arcbishop na Canterbury ya sanya masa kambin sarautar Ingila domin maye gadon mulki na marigayiya Sarauniya Elizabeth ta biyu. Bikin, shi ne irinsa na farko cikin shekaru 70 da suka gabata. An gani tare da jin yadda mahalartar bikin suka ɓige da sowa a yayin sanya wa Sarkin kambin sarauta na zinari wanda aka samar da shi tun a ƙarni na 17. Tun bayan da aka gudanar da makamancin wannan biki a shekarar…
Read More
Jarumi Uzee ya zama jakadan Bankin Musulunci na TajBank

Jarumi Uzee ya zama jakadan Bankin Musulunci na TajBank

Daga AMINA YUSUF ALI Fitaccen jarumin nan na Kannywood da Nollywood, Usman Uzee, ya zama jakadan bankin nan na Musulunci, wato TajBank. A ranar Alhamis, 4 ga Mayu, 2023, jarumin ya rattaba hannu kan yarjejeniyar da bankin tare da manyan jami’an bankin. Idan dai za a iya tunawa, bankin na TajBank yana daga cikin kalilan din bankuna a Nijeriya da ba su mu’amula da kudin ruwa. Shi kuwa Jarumi Uzee yana daga kalilan din jarumin Nijeriya da suke fitowa a finafinan Arewa da na Kudu. Daya daga cikin fitattun finafinan da ya fito shine, Voiceless, wanda ya samu hawa manhajar…
Read More
Za mu ci gaba da tuna ‘Yar’adua saboda cigaban da ya kawo wa Nijeriya – Jonathan

Za mu ci gaba da tuna ‘Yar’adua saboda cigaban da ya kawo wa Nijeriya – Jonathan

Daga UMAR GARBA a Katsina Tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan ya bayyana tsohon maigidansa, Umaru ‘Yar’adua, a matsayin shugaba maras son zuciya. Ya bayyana haka ne a wani ɓangare na ranar cika shekara 13 da rasuwar tsohon shugaban ƙasar na Nijeriya. Jonathan ya kasance mataimakin Umaru Musa 'Yar’Adua daga 2007 zuwa 2010 A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Tiwita ranar Juma’a, inda ya ce, “A wannan rana shekara 13 da ta wuce, ƙasarmu ta yi rashin gawurtaccen shugaba maras son zuciya, Shugaban Ƙasa Umaru Musa Yar’Adua." Mutum ne mai son zaman lafiya da adalci da kuma kamanta…
Read More
Yadda aka gudanar da addu’o’in tunawa da ‘Yar’adua bayan cika shekara 13 da rasuwa

Yadda aka gudanar da addu’o’in tunawa da ‘Yar’adua bayan cika shekara 13 da rasuwa

Daga UMAR GARBA a Katsina Gamayyar ƙungiyoyi masu goyon bayan jam'iyyar PDP, sun shirya taron addu'a gami da karatun Al'ƙur'ani mai girma don tunawa da tsohon Shugaban Ƙasar Nijeriya, marigayi Malam Umaru Musa 'Yar'adua a masallacin hedikwatar jam'iyyar PDP dake Katsina. Taron addu'o'in na zuwa ne bayan da marigayi 'Yar'adua ya cika shekaru 13 da rasuwa a ranar Juma'a, 5 ga watan Mayu, 2023. Da yake jawabi a wajen taron addu'ar, Shugaban kwamitin riƙon ƙwarya na jam'iyyar wanda ya samu wakilcin Lawal Rufa'i Safana, ya bayyana cewar, shirya taron addu'o'in ya zama wajibi duba da gagarumin cigaba da marigayin ya…
Read More
WAEC ta bayyana ranar da za a yi jarrabawar 2023

WAEC ta bayyana ranar da za a yi jarrabawar 2023

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hukumar Shirya Jarrabawa ta Afirka ta Yamma (WAEC) ta sanar da cewa za a gudanar da jarrabawar kammala Sakandare ta Yammacin Afirka ta 2023 (WASSCE) na tsawon makonni bakwai, tsakanin 8 ga Mayu zuwa 23 ga Yuni, 2023. Shugaban hukumar na ƙasa, Patrick Areghan ne ya bayyana hakan a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai gabanin jarrabawar a Legas a ranar Alhamis, 4 ga Mayu, 2023. Areghan ya ce, jarabawar za ta ƙunshi mutane 1,621,853 daga makarantun gwamnati da masu zaman kansu 20,851.
Read More
Ronaldo ke kan gaba wajen karɓar albashi a duniyar wasan ƙwallon ƙafa

Ronaldo ke kan gaba wajen karɓar albashi a duniyar wasan ƙwallon ƙafa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shahararrun ’yan wasan ƙwallon ƙafa Lionel Messi da Cristiano Ronaldo da kuma Kylian Mbappe na cikin jerin ’yan wasa 10 da suka fi ɗaukar albashi a wannan shekarar. A cikin jadawalin da jaridar Forbes ta fitar na ’yan wasa 10 da aka fi biya a wannan shekarar, ya nuna cewar Ronaldo ne ke mataki na ɗaya sai Messi ke biye masa a mataki na biyu ya yin da Mbappe ke a mataki na uku. Wannan nasarar da Ronaldo ya samu dai ta biyo bayan sauya shekarar da ya yi daga Manchester United a shekarar da ta…
Read More
Ba zan maida wani yanki na Nijeriya saniyar-ware ba – Tinubu

Ba zan maida wani yanki na Nijeriya saniyar-ware ba – Tinubu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi alƙawarin yi wa ƙasa ayyukan ci gaba daidai-wa-daida ba tare da nuna wariya ga wani vangare na ƙasar ba. Tinubu, wanda za a rantsar da shi a matsayin shugaban ƙasa a ranar 29 ga Mayu, ya bayyana hakan ne a jiya Laraba a Fatakwal, babban birnin jihar Ribas. A sanarwar da Abdulaziz Abdulaziz, mataimaki ga zaɓaɓɓen shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai ya aikowa Daily Nigerian Hausa a yau Alhamis, Tinubu ya fadi hakan ne yayin ziyarar aiki ta kwanaki biyu a jihar, domin ƙaddamar da…
Read More
‘Yan sanda sun cafke ‘yan ƙungiyar asiri 55 a Ribas

‘Yan sanda sun cafke ‘yan ƙungiyar asiri 55 a Ribas

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Ribas, sun kama mutanen da ake zargin ‘yan ƙungiyar asiri ne 55 da ke aikata ta’asa a yankin Diobu da ke a garin Fatakwal babban birnin jihar. An cafke su ne a wata mavoyarsu da ke yankin Diobu a ranar Talata. Wata majiya da ta buƙaci a sakaya sunanta, ta bayyana cewa, tawagar ‘yan sanda da ke yaƙi da ‘yan ƙungiyar asiri da ke caji ofis ɗin ‘yan sanda na Mile 1 ne suka kama su. Manhaja ta lura da cewa, kai samamen da kuma kamun an yi ne bayan…
Read More
Kamfani Max Air zai yi jigilar Mahajjatan Kano – NAHCON

Kamfani Max Air zai yi jigilar Mahajjatan Kano – NAHCON

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Alhazai ta Nijeriya, NAHCON, ta naɗa kamfanin Max Air a matsayin kamfanin jigilar maniyyatan Jihar Kano 5,917 zuwa ƙasar Saudiyya a lokacin aikin Hajjin bana. Babban Sakataren Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano, Muhammad Abba Ɗambatta ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya kira a Kano. Ya ƙara da cewa, kamfanin yana da inganci kuma yana da jiragen sama uku masu ƙarfin iya jigilar mahajjata sama da 1000 kowanne. Jaridar ta tuna cewa hukumar jin daɗin alhazai ta jihar Kano da gwamnatin jihar sun yi maraba da matakin…
Read More