Editor

9513 Posts
Da Ɗumi-ɗumi: Kotun Birtaniya ta ɗaure Ekweremadu shekara 10 a kurkuku

Da Ɗumi-ɗumi: Kotun Birtaniya ta ɗaure Ekweremadu shekara 10 a kurkuku

*Matarsa, Beatrice za ta shafe shekara shida a gidan yari Kotun Birtaniya ta ɗaure tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ike Ekweremadu, shekara 10 a gidan yari kan yunƙurin cire sannan mutum. Kazalika, kotun ta yanke wa matarsa, Beatrice, ɗaurin shekara shida a kurkuku. Kotun ta kama Ike Ekweremadu da matarsa Beatrice da Dr Obinna Obeta, da laifin safarar sassan mutum ƙarƙashin Dokar Safarar Bayi na Zamani. Kotun ta same su da laifin haɗin baki wajen ɗaukar wani matashi ɗan shekara 21 daga Legas zuwa wani asibitin London don cire masa ƙodar da za a dasa wa 'yar Ekweremadun, Sonia. Da…
Read More
Buhari ya karvi baƙuncin fitaccen ɗan kasuwa, Ummaru Shagalinku a Abuja

Buhari ya karvi baƙuncin fitaccen ɗan kasuwa, Ummaru Shagalinku a Abuja

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja Shahararren fitaccen ɗan kasuwaa Nijeriya, Alhaji (Dakta) Ummaru Shagalinku, mamallakin gidan abinin nan mai suna Shagalinku a fadin Arewa, ya kai ziyarar ban-girma da gaisuwar sallah ga Shugaban Ƙasa kuma Kwamandan Askarawan Nijeriya, Muhammad Buhari, a fadarsa dake babban birni tarayya Abuja radar 23 ga Afrilu, 2023. Bayan gaisuwar sallah, Shugaba Buhari ya tattauna da ɗan kasuwar muhimman batutuwa, musamman akan fannin kasuwanci, inda bayan kammala ganawar nasu ne Alhaji Ummaru Shagalinku ya bayyana wa manema labarai farin cikinsa ciki har da Wakilin Blueprint Manhaja a ciki. Alhaji Ummaru ya kuma taya al’umma Musulmai…
Read More
Buhari ya mayar da Nijeriya shekara 100 baya – Buba Galadima

Buhari ya mayar da Nijeriya shekara 100 baya – Buba Galadima

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ƙusa a Jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya soki ƙwazon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da ya yi a shekaru takwas na mulkinsa. Galadima, wanda tsohon abokin siyasar Buhari ne, ya kuma yi iƙirarin cewa shugaban na Nijeriya ya mayar da ƙasar shekaru 100 baya. Da ya ke magana yayin wata tattaunawa da ya yi da tashar talabijin ta Arise a ranar Laraba, Galadima ya kuma nuna rashin amincewa da furucin da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Femi Adesina ya yi, wanda ya yi iƙirarin cewa shugaban zai bar Nijeriya mafi kyau kan yadda ya…
Read More
Nasarar da Lawan Dare ya samu a Gwamnan Zamfara ba tirsasa wa al’umma aka yi ba – Mai-Nasiha

Nasarar da Lawan Dare ya samu a Gwamnan Zamfara ba tirsasa wa al’umma aka yi ba – Mai-Nasiha

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano An ƙalubalanci maganar da Gwamnan Jihar Zamfara ya yi na zargin cewa an yi amfani da wasu jami'an tsaro, sojoji da 'yan sanda sun tursasa wa mutane, su zaɓi Jam'iyyar PDP ba jam'iyyarsa ta APC ba, da cewa wannan magana da ya yi ba haka ba ne, kuma babu ƙamshin gaskiya a cikinta.  Jigo a Jam'iyyar PDP a Jihar Kano kuma masoyi, hadimi ga zaɓaɓɓen gwamnan jihar Zamfara Alhaji Dauda Lawan Dare, Malam Salmanu Mai Nasiha ne ya yi wannan ƙalubalen da yake mai da martani ga maganganun Gwamnan Zamfara Matawalle da ya ke zantawa…
Read More
Sabbin masarautun Kano sun kafu daram ba za su rushe ba, Ganduje ga Kwankwaso

Sabbin masarautun Kano sun kafu daram ba za su rushe ba, Ganduje ga Kwankwaso

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce sabbin masarautu huɗu da gwamnatinsa ta ƙirƙiro sun zo kenan ba rushewa. A makon da ya gabata ne Shugaban Jam’iyyar New Nigerian Peoples Party, NNPP na Ƙasa, Rabi’u Kwankwaso, ya yi nuni da cewa gwamnati mai jiran gado za ta yi nazari a kan tsige tsohon Sarki Muhammadu Sanusi II, da kuma rarraba masarautar. Amma yayin da ya ke jawabi a wajen bikin ranar ma’aikata ta 2023 da aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha, Kano a ranar Litinin, Ganduje ya ce Allah ba zai…
Read More
Ranar ma’aikata: Ma’aikatan Nijeriya sun shiga tasku lokacin mulkin Buhari – NLC

Ranar ma’aikata: Ma’aikatan Nijeriya sun shiga tasku lokacin mulkin Buhari – NLC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya ta ce ma'aikatan ƙasar na cikin wani hali, kuma babu wani sauyin a zo a gani da aka samu tun bayan kama mulkin Shugaba Muhammadu Buhari. A wata tattaunawa da BBC, albarkacin ranar ƙwadago ta duniya, sakataren ƙungiyar ƙwadago ta Nijeriya, Kwamared Nasir Kabir ya ce ci gaba kaɗan ne kawai za a iya cewa ma'aikata sun samu a ƙarƙashin gwamnati mai ci. Ya ce "abin farin ciki ne sake zagayowar ranar ma'aikata ta duniya, amma maganar gaskiya al'amuran da ma'aikata (a Nijeriya) suke ciki da abubuwan da suke fama…
Read More
Barcelona na yunƙurin lashe La Liga na bana

Barcelona na yunƙurin lashe La Liga na bana

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ranar Lahadi Espanyol za ta karɓi baƙuncin Barcelona a wasan mako na 34 a La Liga. Ƙungiyoyin biyu sun tashi 1-1 ranar 31 ga watan Disamba a Camp Nou a karawar farko a kakar bana ta La Liga. Kasancewar wasan na dabi ne, wataƙila a ranar Barcelona za ta lashe babban kofin ƙwallo na Sifaniya. Rabon da Barcelona ta lashe La Liga tun kakar 2018/19, mai kofin 26 jimilla, amma Real Madrid ce mai riƙe da na bara. Kawo yanzu idan aka buga wasannin mako na 34 a ƙarshen mako, zai rage saura fafatawa huɗu a…
Read More
Gwamnatin Tarayya ta musanta nuna ƙabilanci wajen kwaso ’yan Nijeriya daga Sudan

Gwamnatin Tarayya ta musanta nuna ƙabilanci wajen kwaso ’yan Nijeriya daga Sudan

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin Tarayya ta yi watsi da zarginta da nuna ɓangaranci ko kuma ƙabilanci wurin kwaso ‘yan Nijeriyar da ke Sudan. A wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta, an ga wani mutum yana magana da harshen Igbo inda ya bayyana cewa an ƙi kwaso wasu daga cikinsu saboda ƙabilanci. Sai dai a wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Wajen Nijeriya ta fitar, ta bayyana cewa babu ƙamshin gaskiya a iƙirarin da mutum ya yi. “Ma’aikatar ta yi bincike kan zarge-zargen da ya yi kuma tana tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa babu gaskiya a zarge-zargen…
Read More
Nijeriya za ta zama kan gaba a tattalin arzikin ƙasa nan da 2050 – Buhari

Nijeriya za ta zama kan gaba a tattalin arzikin ƙasa nan da 2050 – Buhari

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja A ranar Laraba ne Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da wani sabon shiri na ci gaban ƙasa na dogon lokaci mai taken Nijeriya Agenda 2050 (NA 2050). Shirin dai shi ne tabbatar da cewa ƙasar na samun GDP na kowace Dalar Amurka 33,328 a duk shekara, wanda zai sanya ta cikin manyan ƙasashe masu matsakaicin larfin tattalin arziki a duniya nan da shekarar 2050. Shugaban ya ƙaddamar da NA 2050 kafin a fara taron majalisar zartarwa ta tarayya a zauren majalisar da ke Fadar Shugaban Ƙasa a Villa, Abuja. Ya ce, shirin yana…
Read More
Sojoji sun ceto ma’aikatan jinƙai daga hannu ISWAP

Sojoji sun ceto ma’aikatan jinƙai daga hannu ISWAP

Sojoji sun ceto biyu daga cikin ma'aikatan jinƙai ukun da mayaƙan ISWAP suka yi garkuwa da su a Borno. Waɗanda lamarin ya shafa ma'aikatan ƙungiyar nan ce ta Family Health International (FHI360). Majiyarmu ta tattaro cewar a ranar Laraba aka kuɓutar da ma'aikatan. An yi garkuwa da ma'aikatan ne a masaukin baƙin ƙungiyar da ke ƙauyen Fotoko kusa da Gamborou Ngala, Jihar Borno kwanan baya. Majiyar News Point Nigeria ta ce har yazu da wasu mutum uku a hannun mayaƙan. Sai dai tun bayan sace ma'aikatan babu wata sanarwa a hukumance a kan hakan, walau daga ɓangaren sosjoji ko ƙungiyar…
Read More