04
May
04
May
Jirgin saman Air Peace ya yi nasarar kwaso ɗaliban Nijeriya sama 270 daga Filin Jirgin Saman Aswan da ke Masar zuwa Abuja, inda ya sauka Babban Filin Jirgin Saman Nnamdi Azikiwe da misalin ƙarfe 11:38 na dare a ranar Laraba Haka shi ma jirgin sojojin saman Nijeriya, NAF C-130, ya biyo baya jim kaɗan ɗauke da mutum 80. An cimma wannan nasarar ce bayan mako guda da bai wa 'yan ƙasa tabbacin kwaso waɗanda lamarin ya shafa da Gwamnatin Tarayya ta yi. Bayanai sun ce, sakamakon rufe sararin samaniyar ƙasar Sudan mai fama da rikici, ya sa aka yi jigilar…
03
May
"An bar Arewa a baya ta fuskar samun damar karatu kyauta" Daga ABUBAKAR M. Taheer Dakta Habiba Iliyasu Atta wadda senior lakcara ce a Department ɗin Microbiology na Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya. A cikin wannan tattaunawa da wakilinmu Abubakar M Taheer ya yi da ita, ta kawo matsalolin dake saka ƴan Arewa rasa damar samun guraben karatu a ƙasashen waje. Haka kuma Dakta ta kawo irin nasarorin da ta samu wajen samun 'scholarship' na PTDF da hanyoyin da mutum zai bi wajen samun irin damar da ta samu, wato 'scholarship' ɗin, tare kuma da bayyana mana irin ƙalubalai…
03
May
Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Musa Sani Aliyu wanda aka fi sani da Musa Khan, ma'aikaci ne a gidan rediyon Jalla da ke birnin Kano. Wata rana da daddare misalin ƙarfe tara a kan hanyarsa ta komawa gida bayan ya tashi daga wajen aikinsa a daidai kan titin Club Road kusa da ofishin Kwastom yayin da yake tafiya wasu vata gari a kan babur suka sha gabansa yayin da suka nemi ya bada wayar da ke jikinsa, kafin ya sa hannu ya zaro wayar daga aljihunsa, sai ɗaya daga cikin su ya fitar da wata wuƙa da ke jikinsa da aka…
03
May
An sake samun nasarar kwashe wani rukuni na 'yan Nijeriya da suka maƙale a Sudan zuwa ƙasar Masar a ranar Laraba. Hukumar kula da 'yan Nijeriya mazauna ƙetare (NiDCOM), ta tabbatar da hakan a shafinta na Tiwita, inda ta ce 'yan Nijeriyar sun isa Masar daga Sudan lafiya ƙalau, yanzu kuma suna shirin barin Masar zuwa Nijeriya. “Fasinjoji 350 sun isa Filin Jirgin Saman Aswan da misalin ƙarfe 9.30 am. Jirgin saman NAF C130 ne zai kwashe su" zuwa gida Nijeriya, in ji sanarwar. Ta ƙara da cewa, jirgi mai lamba “C130 zai kwashi fasinja 80, yayin da Airpeace zai…
03
May
*Daga yanzu dole kowane ɗan indostiri ya zama cikakken mamba mai rijista - NFVCB Daga BASHIR ISAH Hukumar Tace Fina-finai ta Ƙasa (NFVCB), ta nuna damuwarta kan yadda masana'antar fina-finai ke samar da fina-finai marasa inganci saboda rashin aiki da ƙwarewa. Hukumar ta nuna damuwar tata ce cikin sanarwar da ta fitar mai ɗauke da sa hannun shugabanta, Thomas Adedayo, wadda aka aike wa ɗaukacin masu ruwa da tsakin masana'antar fina-finai. Domin kawar da wannan matsalar, Adedayo ya ce wajibi ne a dawo a riƙa aiki da ƙwarewa a harkar fim, kama daga masu rubuta labaran fim zuwa masu kwalliya…
03
May
'Yan uwan korarren Kwamishinan Zaɓe na Jihar Adamawa, Barr. Hudu Yunusa-Ari, sun ce Kwamishinan da kansa ya kai kansa Hedikwatar 'yan sanda don amsa gayyatar da aka yi masa amma ba tsarewa ba kamar yadda 'yan sanda suka bayyana. Sun ce, a ranar 5 ga Mayu 'yan sanda suka gayyace shi zuwa hedikwatarsu don amsa tambayoyi, amma bisa ra'in kansa ya tafi ofishin a ranar 2 ga Mayu, 2023 “Wani Sanata ne ma ya tuƙa shi zuwa Babban Ofishin 'Yan Sandan," a cewar wani ɗan uwan Kwamishinan 'Yan uwan sun bayyana wasiƙar gayyatar da 'yan sanda suka aike wa Arin…
03
May
Daga SHAMSUDDEEN MUHAMMAD Wannan rubutu labarin karan kaina ne, na abin da 'yan hukumar rarraba wutar lantarki (KEDCO) suke min a yanzu haka. Kuma yana da kyau mu san gidana mutum 4 ne kacal a ciki, biyu manya biyu yara, don haka wutar da muke amfani da ita ba ta da yawa. Hasali ma firji ne kaɗai yake jan wuta a gidan, shi ma kuma sai mu yi kwana 4 ba wuta mai karfin da za ta iya kunna shi. Sannan kuma ba a saka mana mita ba, don haka, bill ake kawo min duk wata (postpaid billing). Na yi…
03
May
Daga FATUHU MUSTAPHA Na ga babban abinda 'yan Kwankwasiyya suke yaƙar Dakta Nasiru Yusuf Gawuna da shi shi ne, wai zai yanka filaye da a ce ya ci zave, to amma ga wasu tambayoyi: Waye ya yanka maƙabartar Kukar Bulukiya aka yi gidan mai? Ko nan ma Ganduje ne? Wa ya rushe Badala, da sunan zai yi titi, ko shi ma Ganduje ne kawai ya tava yi? Waye ya raba Daula Hotel ga maƙarrabansa? Shi ma Gwamna Ganduje ne? Shin kantinan da aka gina a kan ganuwar da ke Ƙofar Mata ma Gwamna Ganduje ne ya yanka su? Waye ya…
03
May
*Ya jajanta wa waɗanda iftila'in ya shafa Zaɓaɓɓen gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana alhininsa game da gobarar da ta tashi a shahararriyar kasuwar wayar salula da ke Bebeji Plaza a Gusau, babban birnin jihar. Lamarin dai ya faru ne a daren ranar Litinin, inda gobarar ta lalata ƙadarori na miliyoyin Naira. Da yake jawabi ga shugabannin kasuwar da kuma waɗansu daga cikin waɗanda abin ya shafa a yayin ziyarar gani da ido da ya kai kasuwar ranar Talata, Lawal ya jajanta wa masu sayar da wayoyin salular da kuma masu ƙadarorin waɗanda tabbas suka yi asarar da ba…
