Editor

9513 Posts
‘Yan sanda sun cika hannu da korarren Kwamishinan Zaɓen Adamawa, Yunusa-Ari

‘Yan sanda sun cika hannu da korarren Kwamishinan Zaɓen Adamawa, Yunusa-Ari

'Yan sanda sun damƙe korarren Kwamishinan Zaɓe na Jihar Adamawa, Hudu Yunusa-Ari, kan abin da ya aikata yayain zaɓen gwamna a jihar. Kakakin 'yan sanda, Muyiwa Adejobi, ya bayyana a cikin sanarwar da ya fitar ranar Talata cewa, yanzu haka 'yan sanda na tsare da Yunusa-Ari. Sanarwar ta ce 'yan sanda sun cika hannu da Arin ne a Abuja, inda yake ci gaba da amsa tambaya kan dalilin da ya sa ya yi riga malam masallaci wajen bayyana sakamakon zaɓe alhali ana tsaka da tattara sakamakon zaɓen yayin zaɓen cike giɓi na gwamnan jihar da ya gudana kwanan baya. Ari…
Read More
Mun zo aikin ceto ne, cewar Zaɓaɓɓen Gwamnan Zamfara

Mun zo aikin ceto ne, cewar Zaɓaɓɓen Gwamnan Zamfara

Zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, a'ya ƙaddamar da kwamitin karɓar mulki a ranar Talata a Gusau, babban birnin jihar. Yayin ƙaddamar da kwamitin mai membobi 60, Dauda Lawal ya jaddada cewa ya zo aikin ceto ne tare da sake gina Jihar Zamfara. Sanarwar da ofishin zaɓaɓɓen gwamnan ya fitar mai ɗauke da sa hannun Sulaiman Bala Idris ta nunar cewa, an kafa kwamitin karɓar mulkin ne a ƙarƙashin jagorancin tsohon Sufeto Janar na ‘yan sanda, M.D Abubakar. Da yake jawabi a wajen ƙaddamar da kwamitin, mai girma Dauda Lawal, ya ce nauyin da ya rataya a kan kwamitin shi…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: An tsige Kakakin Majalisar Abia

Da Ɗumi-ɗumi: An tsige Kakakin Majalisar Abia

Majalisar Dokokin Jihar Abia, ta stige Kakakinta, Hon Chinedum Orji, a ranar Talata. Manhaja ta kalato cewar, mambobin Majalisar 18 daga cikin 24 da majalisar ke da su suka rattaɓa hannu kan tsige Kakakin. Ya zuwa haɗa wannan labari babu cikakken bayani kan dalilin tsige Kakakin.
Read More
Masari ya yi bankwana da ma’aikata a matsayin Gwamnan Katsina

Masari ya yi bankwana da ma’aikata a matsayin Gwamnan Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya halarci bikin Ranar Ma'aikata karo na ƙarshe a matsayin shi na Gwamnan jihar. Da yake jawabi a filin wasa na Muhammadu Dikko da ke Katsina, Gwamna Masari ya yaba wa ƙwazon ma'aikatan jihar bisa jajircewar da suke nunawa a wuraren aikinsu tun 2015. Masari wanda ya samu wakilcin mai ba shi shawara na musamman kan ayyukan 'yan ƙwadago, Tanimu Lawal, ya ce, gwamantinsa ta samar da kyawawan manufofi gami da inganta yanayin aiki ga ma'aikatan jihar wanda hakan ya samar da jin daɗi ga al'umar jihar. "Mun kuma…
Read More
An damƙe gurgu na sayar da ƙwaya a cikin kekensa na guragu

An damƙe gurgu na sayar da ƙwaya a cikin kekensa na guragu

Wani abin mamaki ya faru yayin da wani gurgu da ke amfani da kekensa na guraru wajen ya ke sayar da miyagun ƙwayoyi a lunguna da saƙo. Kakakin Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) na ƙasa, Femi Babafemi, ya ce an kama gurgun ɗauke da tabar wiwi mai nauyin kilo gram 1.3 da kuma lita 10 na kwayar Monkeyy Tail, a samame da hukumar ta kai matattarar masu shaye-shaye a yankin Ekpoma na Ƙaramar Hukumar Esan ta Arewa ta Jihar Edo. Ya sanar a Abuja ranar Lahadi cewa bayan gurgun, an cafke wata matashiya mai shekaru 19…
Read More
Ya kashe maƙwabcinsa kan wurin ajiye mota

Ya kashe maƙwabcinsa kan wurin ajiye mota

Wani mutum ya soka wa makwacinsa wuƙa har lahira saboda gardama kan wurin ajiye mota. Lamarin ya faru ne a yankin Ajah na Jihar Legas, kamar yadda kakakin ’yan sandan jihar, Benjamin Hundeyin ya tabbatar. Ya ce, rundunarsu ta tsare wani mutum mai shekara 41 da ya caka wa maƙwabcinsa wuƙa a ciki, ya kashe shi nan take, bayan sun samu saɓani kan wurin ajiye mota a kan layin Gbadamosi da ke Rukunin Gidaje na Badore a daren Asabar. Hundeyin ya ce, an kai rahoton abin da ya faru ofishin ’yan sanda na Langbasa kafin wayewar garin Lahadi. “’Yan sanda…
Read More
Mutane sun yi wa jaruma Tonto Dikeh ca kan shawarar da ta ba wa matan aure

Mutane sun yi wa jaruma Tonto Dikeh ca kan shawarar da ta ba wa matan aure

Daga AISHA ASAS A 'yan kwanakin nan ne labarin cin amanar da aka yi wa jaruma a masana'antar Nollywood, Mimi Linda Yina, wadda aka fi sani da Medlin Boss, ya ja hankalin mutane, ba ma kamar samun masaniyar cewa, ba wai kawai mijinta ya ci amanar ta da mace ne kawai ba, ya ci amanar ta da babbar ƙawarta. Da wannan mutane suka dinga zaro maganganu daga zuciya suna ajiye wa a duk inda maganar zata yi tasiri, musamman ma mata. Da yawa suna tofin Allah tsine ga wannan cin amanar da ƙawa da mijin jarumar suka aikata, a wani…
Read More
Ka adana kuɗinka, shawarar Ɗangote ga mawaƙi Davido

Ka adana kuɗinka, shawarar Ɗangote ga mawaƙi Davido

Ɗangote na siyan mota biyu kacal a shekara takwas - Davido Daga AISHA ASAS Shahararren mawaƙi David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, a cikin wata tattaunawar da ya yi da Forbes, ya bayyana kyakyawar alaƙa da ke tsakanin sa da babban ɗan kasuwa, Aliko Ɗangote. A cikin tattaunawar, Davido ya yi muhimman batutuwa da suka haɗa da irin shawarar da Ɗangote ya fi yawan ba shi a duk lokacin da suka haɗu. Shawarar da za mu iya cewa, da yawa mutane sun yi mamakin fitowarta daga babban mai kuɗi irin Ɗangote. Da yawa idan ka tarar da wani…
Read More
Tarihin Hawan Sallah a Ƙasar Hausa (I)

Tarihin Hawan Sallah a Ƙasar Hausa (I)

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hawan Sallah wata al'ada ce da ta daɗe a tarihin Masarautun Ƙasar Hausa. Masarautar Kano: A wannan masarauta, akwai hawan sallah da ake yi duk shekara a lokacin ƙarama da kuma babbar sallah. Bayanai na cewa Muhammadu Rumfa ne ya assasa tsarin hawan sallah a Kano. Daga cikinsu akwai Hawan ranar sallah da Hawan Nasarawa da Hawan Ɗorayi da Hawan Daushe da Hawan Fanisau. Sai dai daga cikin waɗannan haye-haye da ake yi a Masarautar Kano, guda biyu ne suka fi jan hankali. Hawan Nassarawa: Yayin wannan hawan, sarki na zuwa gidansa da ke Nassarawa daga…
Read More
NAFDAC ta haramta shigo da Indomie Nijeriya

NAFDAC ta haramta shigo da Indomie Nijeriya

Hukumar Kula da Inganci Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC), ta ce an haramta shigo da taliyar Indomie zuwa Nijeriya daga ƙetare bayan da aka yi zargin gano sanadari mai haddasa cutar daji ko kansa a cikin wani nau'in taliyar. Majiyarmu ta ce a baya-bayan nan jami'an kiwon lafiya a ƙasashen Malaysia da Taiwan sun gano taliyar Indomie samfurin "Sapecial Chicken" na ɗauke da sanadarin 'ethylene oxide' mai ƙarfin haifar da cutar kansa. Bayanai sun ce 'Ethylene oxide' sanadari ne da akan yi amfani da shi wajen kashe ƙwayoyin cuta a jikin kayan aikin kiwon lafiya. Ma'aikatar Lafiya ta Malaysia…
Read More